Showing posts with label DANDALIN MU SHA DARIYA. Show all posts
Showing posts with label DANDALIN MU SHA DARIYA. Show all posts

Tuesday, 17 December 2024

Dariya Dole: Gajeren Labarin Ban Dariya Na 'Yan Zamani

Dariya Dole: Gajeren Labarin Ban Dariya Na 'Yan Zamani

Ba zan taɓa mantawa ba lokacin da wata tsohuwan budurwata ta aiko mini da wasiƙar rabuwa, a daidai lokacin da aka kawo wasiƙar ina tare da mamata.


Gajeren labarin ban dariya na 'yan zamani
Hoto: LinkedIn

Marubuci:-  Dan Nigeria DN


Sai mamata ta tambaye ni " Mene ne kake karantawa anan?".


Sai na ce mata littafin koyon girki ne.


Bayan mintuna biyu haka sai mamata ta gan ni ina kuka, sai ta ƙara tambayata "Me ya sa kake kuka?"


Sai na ce mata an zo daidai wajen da ake yankan albasa ne.

Monday, 28 October 2024

Dariya Dole: Bafulatani Da Dabbobi Masu Magana

Dariya Dole: Bafulatani Da Dabbobi Masu Magana

Wani Bafulatanin ƙauye ne ya tafi kiwon shanu, to yana da kare, can da yamma ta yi sai ya kaɗo shanunsa don su dawo gida.


Bafulatani Da Dabbobi Masu Magana
Hoto: Ahmad Zada/Freepik

Suna tafiya yana dukansu, can sai wata saniya daga cikin su ta ce: "Haba Dan Allah, ka saurara mana da duka haka nan mana, kamar ka samu jakuna?


Koda jin haka sai wannan Bafulatanin ya fara gudu, yana ta gudu karen shi na biye da shi, sai da ya yi gudu kamar ran shi zai fita, sai ya samu wata bishiya ya nufi inuwarta da niyyar hutawa, da zaunawarsa sai ya ce "Wash!!! Tunda nake a duniya ban taɓa jin dabba ta yi magana ba sai yau" .


Sai karen shi ma ya ce: "Wallahi ni ma haka.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba, amma mun yi gyare-gyare a rubutun domin ya nishaɗantar da ku tare da gamsar da ku.

Tuesday, 22 October 2024

Kyakyatawa Dole: Saurayi Da Amaryar Mafarki

Kyakyatawa Dole: Saurayi Da Amaryar Mafarki

Bayan na gama shiryawa zan fita ofis, sai amaryata ta fito da shagwaɓa ta riƙe hannun jakar da ke rataye a kafaɗata. Ta ce "Darling yau a gida za ka zauna ka yi min kitso ko?"


Saurayi Da Amaryar Mafarki
Hoto: Thais Varela/Unsplash

Sai na juyo na dube ta tare da dafa kafaɗarta.


Na ce mata "Amaryata ki yi haƙuri sai na dawo,".


Cikin tattausar murya ta ce "To My Dear.".


Na tafi har na je bakin ƙofa sai na ji ta ce : "Honey". Juyowar da zan yi sai ta yi min wani kallo mai karya zuciya.


Ban san lokacin da na saki jakar da ke hannuna ba, nan take na yo kwana, na zauna abakin doguwar kujera na ce "Zo na yi miki kitson".


Na ture ɗan kwalin da ke kanta na kama lallausan gashinta ina ja tare da shafawa.


Ban ankara ba, sai da na ji saukar mari, Raasss! Taasss! na miƙe a firgice.


"Wanne irin iskanci ne wannan za ka dinga ja min gemu ina barci?"


Ashe wai mafarki nake yi.


Gemun yayana (Ustas) da muke maleji a katifa ɗaya na kama ina ta faman ja. 


Ya yi ta faɗa a fusace.


Kwana na yi cikin takaici ni ban gama mafarkin ba kuma na sha mari.


Gwaurantaka ba ta yi ba, ku je ku yi aure.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba, amma mun yi gyare-gyare a rubutun domin ya nishaɗantar da ku tare da gamsar da ku.

Wednesday, 2 October 2024

Dariya Dole: Ma'aurata Da Aljanu

Dariya Dole: Ma'aurata Da Aljanu

Wani Ango ne ya yi sabon aure shi da matarsa suka tare a sabon gida, kullum kafin su kwanta bacci sai ta wanke kwanukan da aka ci abinci, da tukwane gaba-ɗaya, amma idan safiya ta yi gari ya waye sai su ga duk an ɓata kayan da ta wanke, sai su yi ta mamaki ya haka? Me yake faruwa ne?


Ma'aurata Da Aljanu
Hoto: Maple knoll

Sai suka yanke shawarar cewa yau ba za su yi bacci ba sai sun ga mai yin wannan aikin, dare ya yi dare, sai suka ji an fara motsi a cikin gida, sai suka leƙo su ga ko su wane ne, suna leƙowa kuwa sai suka ga wasu irin halittu sun ɗora girki a kan tukunya, cikin minti biyu abinci ya dahu.


Sai aka fara rabo kamar haka;


Ɗauki wannan ka kai wa Ifritu yana ƙasar India.


Kai kuma miƙa wa Turwas yana ƙasar China.


Kai kuma yi sauri ka je ƙasar Masar (Egypt) ka kai wa Sharfayailu.


Karɓi wannan ka miƙa wa ango da amarya na cikin gidan nan, tun da yau sun laɓe suna kallon mu.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.

Wednesday, 18 September 2024

Mu Kyakyata: Malamin Addini Da Karuwa

Mu Kyakyata: Malamin Addini Da Karuwa

Wani malami mai da'awa ne ya samu wata mata mai zaman kanta ya yi ta zuba mata wa'azi.


Malamin Addini Da Karuwa
Hoto: Magic Baltimore

Marubuci:- Rabi'u Garba Tajuddeen


A ƙarshe ya ce soyayya don Allah ce ta sa shi yake faɗa mata gaskiya.


Karuwa ta ce "Da gaske wannan soyayya ce don Allah?".


Malami ya ce "Idan ba so don Allah ba ne mai zai sa na ɓata lokacina, ina jan hankalinki ki bar aikin saɓo?".


Karuwa ta ce "Akwai abin da ya yi saura".


Malami ya ce na'am.


Karuwa ta ce "Eh! wa'azi kawai bai fiya hana mu wannan sana'a tamu ba, don da ita muke rayuwa.".


Malami ya ce "To mene ne ya yi sauran?"


Karuwa ta ce "Ka aure ni wannan shi ne so don Allah".


To a nan dai wa'azi ya tsaya.


Ƙasa ko sama malam ya yi ɓatan dabo.

Wednesday, 21 August 2024

Dariya Dole: Yara Da Liman A Makabarta

Dariya Dole: Yara Da Liman A Makabarta

A wani ƙauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu, sai suka tsaya shawarar inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gan su ba, sai ɗaya ya bayar da shawarar a tafi maƙabarta.


 Yara Da Liman A Maƙabarta
Hoto: Choose to see good

Bayan sun isa maƙabarta ɗauke da mangoron nan, a ƙofar shiga sai mangwaro biyu su faɗo daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a gan su sai suka bar su nan suka wuce cikin maƙabartar da sauran mangwaron.


Su na shiga sai suka zube mangworon a ƙasa suka fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya ɗauki mangoro ɗaya ya aza a gabanshi ya ce, "Ni ɗaya" sai kuma ya ɗauki ɗaya ya aza a gaban ƙaramin ya ce, "Kai ɗaya."


Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye-shayensa, yana zuwa dai dai ƙofar maƙabarta sai ya ji wata 'yar ƙaramar murya kamar ta yara ana cewa, "Kai ɗaya, ni ɗaya," kuma an ci gaba da maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai gidan limamin ƙauyen.


Yana zuwa ya same shi ƙofar gida yana shirin yin alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam, yau wani baƙon al'amari ke faruwa a maƙabartar can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce mu je in gani.


Su na zuwa, sai suka laɓe a bakin ƙofar maƙabartar, sai suka ji ana cewa, "Kai ɗaya, ni ɗaya, kai ɗaya, ni ɗaya..." Can sai suka ji an ce, "To kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa nan." Can kuma sai suka ji an ƙara cewa, "To waɗancan biyun na bakin kofar shigowa fa?" 


Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai suka ari takalmin kare, su na faɗin ai mu ba mu mutu ba, ba mu daga cikin matattu, tsammani suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan mangwaron su biyu da suka faɗi bakin ƙofa suke nufi ba.


Tushe/Asali: Waziri Aku 

Monday, 5 August 2024

Kyakyatawa Dole: Maigadi Da Alhaji

Kyakyatawa Dole: Maigadi Da Alhaji

Wani Magidanci ne yana zaune da matarsa suna hira sai ta ce "Bari na kawo maka abinci ka ci, na ga yanzu ka dawo daga kasuwa".


Maigida Da Alhaji
Hoto: Ceoministryng


Sai ya ce "To Uwargida me aka dafa ne yau?". 


Sai ta ce "Shinkafa da miya".  


Sai ya ce "Ina fatan dai ba a gidan maƙwabcinmu kika sayo tumatur ɗin ba ko?"


Sai ta ce "Kamar ka sani a can na sayo, kenan ya ya zan yi?"


Sai ya ce "Ina tsoron ko ya saka guba ne a cikin tumatur ɗin".


Sai ta ce "Ai sai da na fara bai wa karen gidan nan tukunna kafin na kawo maka Maigidana". 


Sai ya ce "To shikenan". Ya fara cin abincin kenan, sai 'yar aikin gidan ta shigo ta yi sallama ta ce "Alhaji Maigadi ya ce na gaya maka karen gidan nan ya mutu".


Nan take Alhaji ya karaya sai ya cewa matar tasa "Kafin na mutu zan roƙi gafarar ki domin na yi miki laifi. Mun haifi yara biyu da 'yar aikin gidan nan.".


Sai matar ta ce "Ni ma ka yi mini afuwa a cikin yaranka guda shida, huɗu na Maigadi ne biyu ne kawai naka.".


Ana haka sai Maigadi ya shigo, ya ce "Alhaji wani ne ya yi sallama yanzu koda na amsa sai yake gaya min cewa, a ba ka haƙuri shi ne ya buge karen nan da mota har ya mutu".


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.

Tuesday, 2 July 2024

Kyakyatawa Dole: Tsohuwa Da Alkali

Kyakyatawa Dole: Tsohuwa Da Alkali

A wata kotu ne ana sauraron ƙara jama'a cike maƙil, sai aka buƙaci wata tsohuwa ta fito domin bayar da shaida ga wanda ya kawo ƙara.


Tsohuwa Da Alƙali
Hoto: MediaCat Magazine


Da ta fito sai Lauyan wanda ake ƙara 
ya fito domin yi mata tambayoyi.

Lauya: Baaba shin ko kin san ni Wane ne?

Tsohuwa: eh mana na san ka, ai tun kana ƙarami kai maƙaryaci ne, ka iya haɗa waje, ga ka da yaudara da kuma rashin iya magana ga kuma shaye-shaye da neman mata.

Lauya jikin shi ya yi sanyi cikin jin kunya
ya  je kusa da ɗayan Lauyan sai ya ce "Baaba wannan fa? kin san shi?

Tsohuwa: ai gwanda kaima. Wannan kam ai asalin daƙiƙi  ne gashi da son jin gulma ga kuma munafurci. Kai bari ka ji yanzu haka yana cin amanar matarsa da wasu matan banza har uku kuma ɗaya daga cikinsu matarka ce.

Tana rufe baki sai Alƙali ya kira duka Lauyoyin cikin ƙanƙanuwar murya ta sirri ya ce dasu: "Kun san Allah! idan wani shege daga cikin ku ya kuskura ya tambayeta ko ta san ni, tabbass zai ci ubanshi kuma sai na sa an ƙwace lasisin shi".


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.

Wednesday, 19 June 2024

Dariya Dole: Labarin Tsohuwa Da Direba

Dariya Dole: Labarin Tsohuwa Da Direba

Wata tsohuwa ce a garin Kano ta je tashar mota ta hau zuwa jihar Lagos, an fara tafiya kenan sai tsohuwar nan da tuni ta samu kujera ta zauna cikin fasinjoji ta ce "Malam Direba idan an je Kaduna ka sanar da ni". Direba da ke tuƙi ya ce "To Baba.".


Tsohuwa Da Direba
Hoto: Rappler 


MarubuciImran Musa Jahun

An jima kaɗan tsohuwa ta sake cewa

Direba idan an zo Kaduna ka faɗa min fa, Direba ya hasala ya ce "Gyatuma ai na ji

kuma ban manta ba". Aka ci gaba da tafiya, can a wajen Kura tsohuwa ta sake nanata

zancenta, yanzu kam sauran fasinjoji ma

sai da suka ji haushinta, aka ce haba Gyatuma ai ko Direba ya manta za mu tuna

masa amma kin dage sai ka ce wacce za a 

sace ki.


Wasu daga ciki suka ce a yi haƙuri

gigin tsufa ne.


Allah cikin ikon sa tsohuwa ta kwanta barci, Direba kuma Allah ya

mantar da shi, haka ma sauran mutanen

dake motar duk suka manta, tsohuwa

ba ta farka daga barcinta ba sai da tafiya

ta yi nisa, tsakaninsu da Ikko bai fi 50km,

sai tsohuwa ta farka, ta yi miƙa ta yi hamma ta ce "har yanzu ba a zo Kadunan 

ba ne?" Nan take kowa hankalinsa ya tashi,

aka faɗa ma tsohuwa halin da ake ciki,

nan take ta rusa kuka.


Da jama'a suka ga haka sai aka yi shawara a kan cewar dole Direba ya yi haƙuri a koma Kaduna tunda matar nan ta tsufa da yawa, kuma ba ta da laifi tunda ta yi ta nanatawa.


Aka yi karo-karo aka ƙarawa Direba kuɗin mai aka juyo Kaduna, can wajen Magriba aka iso, aka ce Baba gashi an zo Kaduna.


Tsohuwa ta yi miƙa ta juya ta ce mun zo?

Aka ce ƙwarai kuwa, ta ce "to Alhamdulillahi".



Ta sa hannu ta buɗe jakarta ta hannu.


Ta laluba ta ɗauko PANADOL ɗan gwangwani guda biyu, ta jefa a baki ta bi shi da ruwa, ta ce "Da ma Jikata ce ta ba ni guda huɗu ta ce lallai lallai na sha 2 a Kaduna maganin gajiya ne, idan mun isa Ikko na ƙarasa 2, to tun da yanzu na sha na Kaduna sai kuma mun je Ikko sai na sha sauran biyun."

Monday, 17 June 2024

Kyakyatawa Dole: Yaro Da Limamin Gari

Kyakyatawa Dole: Yaro Da Limamin Gari

A wani ƙauye kimanin shekaru dubu aka yi wani yaro Ɗan baiwa, wato duk lokacin da aka je maƙabarta jana'iza sai yaron ya ga wata jar hula ta taso daga kan mamacin ta hau kan wani mutum.


Mu ƙyaƙyata
Hoto: News18


MarubuciImran Musa Jahun


Duk kuwa wanda ta hau kansa to fa shi ne mai mutuwa na gaba a garin, da Yaro ya ga haka sai ya je yasanar da Liman, da farko Liman bai yarda ba amma yaron ya dinga

faɗa masa wanda hular ta hau kansu har mutum uku kuma suna mutuwa, sai Liman ya samu yaron ya ce masa "Don Allah duk sa'adda ka ga hulal ta taho wajena ka yi min

magana".


Wata rana an je maƙabarta an haƙa rami sai ƙasa ta hau kan Liman, yaron kuma ya ga ƙasar don haka sai yake so ya sanar da

Liman don ya goge ƙasar kansa, sai ya ce "Liman kanka...."


Ai bai ko ƙarasa ba, da Liman ya zabura a guje har yanzu ba a 

samu labarinsa ba.

Sunday, 16 June 2024

Kyakyatawa Dole: Ɗan Sanda Da Samari

Kyakyatawa Dole: Ɗan Sanda Da Samari

Wasu samari su biyar suka tsinci kuɗi miliyan biyar suka fara rigama yadda za'a raba kudin. 


Kyakyatawa Dole
Hoto: Pinterest


Kowa ya ce daidai za'a raba amma ɗaya ya ce nashi sai ya fi yawa saboda shi ya fara ganin kuɗin, nan fa suka fara hayaniya sai ɗaya daga cikinsu ya ce "a ganina wannan rigima aje Police station a raba mana rigima.".


Suka ɗunguma zuwa gaban DPO suna zuwa suka kwashe labari kaf suka gaya masa. "kuɗi muka tsinta miliyan biyar muke so a raba mana gaddama/gardama. koda difi'o ya ji haka sai ya ɗauko albashinsa da aka biya su a ranar ya rarrabawa 'Yan Sandan da suke kan kanta ya ce ku je na sallame ku.


Ya ce wa masu rigima ku kuma ku biyo ni check office.


Difi'o ya ce "Ina kuɗin?" Sai suka ce da ma ba mu tsintaba kawai tunani muke idan muka tsinci wannan kuɗin nawa kowa zai samu.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba. 

Tuesday, 11 June 2024

Kyakyatawa Dole: Mata Da Miji A Mota

Kyakyatawa Dole: Mata Da Miji A Mota

Wani saurayi ne ya je zance gurin masoyiyarsa, sai budurwarsa ta buƙaci ya ba ta labari, sai ya ce "To amma labarin kashi na 1, da na 2 da na 3 da na 4 ne".


Mata da Miji a mota
Hoto: People Images


Marubuci: Musa Muh'd


Sai ta ce ya ba ta, saurayin ya fara bayar da labarin kamar haka;


Kashi 1: Wani miji ne da matarsa, suna cikin tafiya a mota, can sai suka zo  mararrabar hanya, sai ya cewa matar hanyar hagu za mu bi? Matar ta ce a'a maigida mu bi hanyar da ta bi dama, aikuwa sai ya kwashe ta da mari ya ce "Ni na ke tuƙa motar ko kuwa ke? Hanyar hagu za mu bi, sai budurwar ta yi dariya ta ce "Amma wannan miji akwai mugu."


Saurayi ya ce "Saura kashi na 2: suka bi hanya suna tafiya suka iso gurin masu sai da kifi, Maigida ya saya musu, matar ta ce Maigida mai za a yi da shi? ya ce dafawa za ki yi, aikuwa matar ta zabge shi da mari, ta ce kai ne kake girkin ko ni ce? To Soyawa zan yi.


Budurwar ta ƙyalƙyale da dariya, ta ce amma ta burge ni ka ga sun yi duro, saurayi ya ce  saura kashi na 4, sai budurwar ta ce a'a kashi na 3 dai, saurayi ya kwashe ta da mari, ya ce ni ne nake bada labarin ko ke ce?


Shin idan ke ce budurwar me za ki yi masa?


Monday, 10 June 2024

Dariya Dole: An Kawo NEPA

Dariya Dole: An Kawo NEPA

Wata rana na je baƙunta ƙauyen Zazzau (Zaria), ina shiga garin, sai kawai na ga mutane sai gudu suke yi. To abin ka da Bakano (Ɗan Kano/Ɗan asalin Kano), ban saba ganin irin haka a birnin Dabo (Kano) ba, ban san me ke faruwa ba, kawai ni ma sai na shiga sahun masu gudu.


An kawo NEPA
Hoto: Dr koop


Ana cikin gudu sai na fahimci kowa da ya zo ƙofar gidansu, sai ya faɗa ba tare da duba baya ba, kuma ba tare da rufe ƙofa ba.


Abin da ya kuma ba ni mamaki, da na duba kowa sai na ga ya fita daga hayyacin sa, kamar ya kuɓuto daga dajin Sambisa, ana cikin gudu da abin ya ishe ni sai na yanke shawarar, na riƙe ɗaya na tambaye shi.


Haka kuwa aka yi, ina juyawa na ga wani ɗan ƙwaƙƙwaran saurayi a gefe na, na ce "Malam wai gudun me ake yi ne haka?"


Sai ya ce "Ai wutar NEPA aka kawo, shi ne kowa yake gudu ya je ya saka cajin waya saboda hawa Facebook da Twitter da TikTok da kuma Instagram".


Hmm Wai da Ma Haka 'yan Zaria su ke?


Lura: ƙirƙirarren labari ne.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba. Mun kuma gyara wasu abubuwan a labarin domin ya ƙayatar da ku.

Wednesday, 5 June 2024

Dariya Dole: Labarin Teburin Mai Shayi

Dariya Dole: Labarin Teburin Mai Shayi

An yi wani gagarumin hatsari a kan teburin mai shayi inda madara, lifton, bonbita da indomie ne suka rasa rayukansu ciki har da wani ɗan guntun biredi da ya tsallake rijiya da baya.


Rumfar Mai Shayin
Hoto: Thestatesman


Biredin ya shaida mana cewa shi ma bai san yadda hatsarin ya auku ba kawai ya tsinci kansa a ruwan zafi ne.


Rundunar 'yan masa/waina ta kama 'yan fashi da masoki zagaye da tukunyar ɗan wake.


Mun samu labari cewa a cikin wannan satin kimanin ɗan wake 17,900,000 ne suka riga mu gidan gaskiya.


Injiniya Dambu ya kai ziyarar bazata zuwa birnin maiduguri inda saukarsa ke da wuya ya maƙale a wuyan falmata.


Babban jami'i mai kula da yanayin kanwa mai suna Lado ya yi mata ƙwaƙƙwarar bugu a gadon baya.


Manema labarai sun tattauna da injiniya Dambu inda ya ce ba zai daina shaƙe wuyan mutane ba matuƙar ba a cin sa da ruwa a kusa.


Lura: Don nishaɗi kawai aka wallafa shi.


Tushe/Asali: Babu hanyar tabbatar da ainihin mamallakin rubutun, saboda rubutun yana yawo ne a kan yanar gizo-gizo ba tare da asalin sunan mamallakin shi ba.

Saturday, 30 March 2024

Dariya Dole: Tambayoyin Rainin Hankali Da Amsoshin Rainin Hankali

Dariya Dole: Tambayoyin Rainin Hankali Da Amsoshin Rainin Hankali

TAMBAYOYIN RAININ HANKALI GUDA GOMA DA AMSOSHIN SU. 


Nishadi Zalla
Hoto: Buzzfeed

MarubuciAbdulyassar Goron Dutse


ZAN AMSA GUDA TARA DAGA CIKI, KU DAURE KU AMSA MUN TA GOMAN .


1. Alwala nake yi, sai wani ya tambaye ni wai Sallah za ka yi ne ? Sai na ce a'a umara zan yi da aikin hajji.


2. Ina jin bacci na fara gyangyaɗi sai ƙanwata ta ce bacci za ka yi ? Sai na ce suma nake yi ina farfaɗowa.


3. Na tsaya a Bustop ina jiran mota, sai wani ya ce mota za ka hau ? A'a jirgin sama nake jira zai sakko ya ɗauke Ni.


4. Kano a ƙasar Nigeria take ? A'a a dajin sambisa take.


5. Ya gan ni a layin ATM, kuɗi za ka cira ne? A'a zunubina zan cire idan kana so sai na ba ka.


6. Na sayo ragon sallah, yankawa za ku yi ? A'a form za mu saya mai ya fara karatu a gidan Liman.


7. Wai shin shugaba Bola Ahmed Tinubu Ɗan Siyasa ne? A'a malamin islamiya ne.


8. Na ba shi katin gayyata na aurena da budurwata, sai ya ce yanzu aure za ka yi ? A'a haifata za'a yi a ƙara shayar da ni a yayeni.


9. Amarya ta sayo katifa, sai ya ce mata kwana/bacci za ku rinƙa yi akai ? Sai ta ce a'a gutsira za mu rinƙa yi muna sha da shayi.


10. Shin yanzu  kuna karanta wannan  abin da na wallafa ne?....(Posting din nawa ..............)?

Sunday, 9 August 2020

DARIYA DOLE: SAURA KUMA KU CE KARYA NAKE YI

DARIYA DOLE: SAURA KUMA KU CE KARYA NAKE YI

A ƙasar China akwai wani Biri wanda ake zuwa dashi Makaranta tun yana ƙarami, yanzu haka shine Lecturer a babbar jami'ar ƙasar China.

SAURA KUCE KARYA NAKE YI...

Saura kuma wani ya ce "Karya nake yi".

Lura: Anyi ne kawai domin ayi raha.

Don haka, kada ka fassara labarin da wata manufa daban.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 7 August 2020

DARIYA DOLE: A CIKIN SU 10 WAYE YAFI WANI TAFKA SHIRME DA RASHIN KAN GADO?

DARIYA DOLE: A CIKIN SU 10 WAYE YAFI WANI TAFKA SHIRME DA RASHIN KAN GADO?

1. BAKANO: Wanda yana likita ya tada wani mara lafiya daga bacci musamman domin yayi masa allurar bacci.

WAYE YAFI WANI TAFKA SHIRME DA RASHIN KAN GADO...

2. BASAKKWACE: Wanda yake yiwa shuka ban ruwa a dai-dai lokacin da ake sharara ruwan sama.

3. ƊAN FULANI: Da ya fesa turare a jikinsa a dai-dai lokacin ɗaukar hoto da niyyar wai idan an wanko hoton zaiji ƙamshin turaren.

4. ƊAN KADUNA: Da ya sanya radiyo a firinji domin ya saurari cool music.

5. ƊAN KEBBI: Wanda yaci abinci a hotal ya wanke kwano.

6. BABARBARE: Wanda ya tsugunna ya gaida sarkin garinsu lokacin da ya ganshi a TV a gurin wani taro.

7. ƊAN BAUCHI: Wanda yasa aka yi masa polish a takalmi saboda zaiyi hoton passport.

8. BAKATSTSINE: Wanda yana tafiya yayi tuntuɓe da wani abu a duhu saiya ɗauka ya shinshina a hancinsa yaji ashe kashi ne sai yace "ALHAMDULILLAH!" da ban taka ba.

9. DAN GASHUA: Wanda yaje banki da sifana zai buɗe account.

10. BAZAMFARE: Wanda yayiwa ATM CARD ɗinsa lamineshin saboda gudun kada ya karye ko kuma ya koɗe.

LURA: Ba muyi wannan abun domin cin fuska ga wata ƙabila ko yanki ba, mun yi ne kawai domin a yi nishaɗi.

A ra'ayin Ka ko kuma a ra'ayin Ki waye yafi  wani shirme a cikin su? Aika mana da ra'ayin Ka/Ki a adireshin e-mail ɗin mu a muryarhausa24@gmail.com

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 19 April 2020

Dariya Dole: Labarin Wani Saurayi Da Wata Budurwa Akan Gadon Amarci

Dariya Dole: Labarin Wani Saurayi Da Wata Budurwa Akan Gadon Amarci

Kasancewar yau ba aiki ina gida ina hutawa, matata tana haɗa min wani ƙayataccen kunun aya da lemo mai daɗi irin na ma'aurata.

Maganin Gwauro...

Ni kuma na bararraje a kan gado ina jiranta ta kawo min.

Bayan kamar minti ɗaya, sai gatanan ɗauke da kofin (jug) cike da kunun aya, tun kafin ta ƙaraso yawu na ya tsinke, na miƙa hannu na da niyyar ta bani.

Kawai sai ta yi mun fari da ido, ta ce masoyina buɗe bakin ka na baka, haka na buɗe baki na kamar wani ƙaramin yaro tana tsiyaya min ina ta sha.

Kawai sai na ji ana yaya ka tashi akuyar gidan malam lado tanama fitsari abakin ka.

Wai ashe mafarki nake yi bansani ba.

Wayyo Allah!!!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Sunday, 12 April 2020

DARIYA DOLE: LABARIN WANI DAN JARIDA

DARIYA DOLE: LABARIN WANI DAN JARIDA

Wata rana ne da safe wani ɗan Jarida ya fito zashi Office.

Rashin Sani Yafi Dare Duhu....

Yana zuwa bakin titi sai ya tarar anyi hatsari.

Kunsan yadda ɗan jarida yake, yana so ya ɗauki labari da ɗumin-ɗumin sa amma jama'a sun rufe hanyar da zai samu yaga abinda ke faruwa, ballantana yaga meke faruwa.

Kawai sai ya ɗaga murya yana cewa:

"Wayyo Babana ne ku matsa in mai kallon ƙarshe na shiga Uku! Ku taimaka na ganshi karya mutu , shi kaɗai ya rage min a duniya."

Kafin kace wani abu nan take kowa ya matsa ya buɗa masa hanya yana matsawa sai yaga ashe........

ƊAN AKUYA NE MOTA TAKAƊE!!!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Wednesday, 4 December 2019

DARIYA DOLE: NEMAN SHAWARA

DARIYA DOLE: NEMAN SHAWARA

Jiya ne ina bacci da daddare sai namanta ban rufe baki na ba.

Neman Shawara

Sai wani ɓera ya shiga ciki, ya wuce har cikin ciki na.

Kuma gskiya yana takuramin kuma yaƙi mutuwa.

Duk wani abinci dana ci sai ya cinye shi.

Dalilin da yasa kenan nake neman shawara akan in haɗiyi magen ne ta cinye ɓeran ko kuma in sha maganin ɓera Rat Poison domin ya kashe min ɓeran?

Aika da Shawarar Ka a Email ɗin Mu a muryarhausa24@gmail.com

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN WANI MATASHI DA MATSAFA

KARANTA LABARIN WASU MATAFIYA DA ALJANI A SAHARA

KARANTA LABARIN WANI LECTURER DA WATA DALIBAR SA

Kada a manta wannan ƙirƙirarren labari ne bai faru a zahiri ba, anyi shine kawai domin nishaɗi.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode