Wednesday 21 August 2024

Dariya Dole: Yara Da Liman A Makabarta

Tura Wannan Zuwa Ga

A wani ƙauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu, sai suka tsaya shawarar inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gan su ba, sai ɗaya ya bayar da shawarar a tafi maƙabarta.


 Yara Da Liman A Maƙabarta
Hoto: Choose to see good

Bayan sun isa maƙabarta ɗauke da mangoron nan, a ƙofar shiga sai mangwaro biyu su faɗo daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a gan su sai suka bar su nan suka wuce cikin maƙabartar da sauran mangwaron.


Su na shiga sai suka zube mangworon a ƙasa suka fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya ɗauki mangoro ɗaya ya aza a gabanshi ya ce, "Ni ɗaya" sai kuma ya ɗauki ɗaya ya aza a gaban ƙaramin ya ce, "Kai ɗaya."


Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye-shayensa, yana zuwa dai dai ƙofar maƙabarta sai ya ji wata 'yar ƙaramar murya kamar ta yara ana cewa, "Kai ɗaya, ni ɗaya," kuma an ci gaba da maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai gidan limamin ƙauyen.


Yana zuwa ya same shi ƙofar gida yana shirin yin alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam, yau wani baƙon al'amari ke faruwa a maƙabartar can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce mu je in gani.


Su na zuwa, sai suka laɓe a bakin ƙofar maƙabartar, sai suka ji ana cewa, "Kai ɗaya, ni ɗaya, kai ɗaya, ni ɗaya..." Can sai suka ji an ce, "To kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa nan." Can kuma sai suka ji an ƙara cewa, "To waɗancan biyun na bakin kofar shigowa fa?" 


Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai suka ari takalmin kare, su na faɗin ai mu ba mu mutu ba, ba mu daga cikin matattu, tsammani suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan mangwaron su biyu da suka faɗi bakin ƙofa suke nufi ba.


Tushe/Asali: Waziri Aku 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user