Friday, 22 November 2024

Zafafan Kalaman Soyayya 3 Masu Kwantar Da Hankalin Saurayi Da Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Sirrance kalaman masoyi sukan ƙarawa soyayya lokaci sosai, daga bisani ma ta zama ta har abada, ya zama dole ki ɗauki kalaman masoyinki ki kai su wata mihimmiyar farfajiya ko fada a cikin zuciyarki.


Zafafan Kalaman Soyayya 3 Masu Kwantar Da Hankalin Saurayi Da Budurwa
Hoto: Freepik

Marubuci:- Rabs


1. Kin zamo tamkar jinin jikina a kowane lokaci, a kowacce daƙika jinina yake motsawa haka zalika ke ma a duk wannan lokutan kike motsawa a cikin jikina, raba ni da ke daidai yake da zuƙe jinin jikina.


2. Murmushinki ya kan jefa ni a cikin wani yanayi da nake rasa gane a duniyar wata nake ko a duniyar rana? Babu wanda zai gane sai ni kaɗai na gane a duniyar san ki nake.


3. Zuciyarki tamkar ɗanyen ƙwai ne wanda fashewarsa zai sa a yi asarar ruwan ƙwan da yake ciki ya zama dole na hankalta na nutsu na ci-gaba da kula da wannan ƙwai idan har ina so na ci-gaba da numfashi a doran ƙasa domin rayuwata babu ke mutuwa ce maganinta.


Daɗaɗan kalamai na ƙarawa zuciya ƙarfin gwiwa wajen gabatar da soyayya cikin nishadi da kwanciyar hankali ba tare da saɓawa ta shigo tsakanin saurayi da budurwa ba.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi a kyauta kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user