Ka tuna rayuwa kamar wasan kwaikwayo ce dukkanmu muna kan matakinmu, muna kuma wasa ne, amma kowanne lokaci da muka samu don dariya, mu yi murmushi da walwala, yana nufin mun ci nasara a gajeren lokaci. Kada mu yarda matsalolinmu su hana mu dariya, kuma kada mu manta da yin alheri ga juna.
Marubuci:- Abu Ibrahim
A rayuwar Ɗan Adam, akwai tarin tambayoyi da mutum ke yi wa kansa. Me ya sa muke rayuwa? Mene ne dalilin kasancewarmu? Shin akwai wani abin da ke bayan komai? Amsoshin waɗannan tambayoyin ba su da sauki; suna buƙatar zurfafa tunani da fahimta ta musamman.
Rayuwa na da matuƙar wahala, kuma hakan ba ya ƙasƙantar da ita. Kowane Ɗan Adam na fuskantar ƙalubale daban-daban, sai dai kuma yadda muke karɓa da fuskantar waɗannan ƙalubale shi ne abin da ke bambanta mutum da wani.
Ilimi shi ne hasken da ke wargaza duhun jahilci da rashin sanin ya kamata .Yana koyar damu yadda za mu tafiyar da rayuwar mu cikin hikima da kafa kyakkyawar rayuwa da zamantakewa.
Haɗin kai yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma nasarar rayuwa gami da zaman lumana.
Kowanne mutum yana da gudummawar da zai bayar a cikin al'umma. Duk sa'adda al'umma suka haɗa kawuna su gamu da fahimtar juna suna haɓaka ƙarfi gami da ƙarfin zuciyar juna ,wanda hakan ke haifar da ci-gaba mai inganci a cikin rayuwar mu.
Ka taɓa shiga damuwa ka rasa yadda za ka yi?
Ga yadda za ka yi amfani da ita don samun wata dama da ita.
Idan ka taɓa fuskantar wata babbar damuwa da ka rasa mafita, ka tuna cewa ƙarfin da ke tattare da kai ya zarce tunaninka. Basirar da Allah ya ba ka, tare da ƙarfin zuciya sun fi kowacce matsala girma. Ka samu ƙwarin gwiwa don ka iya shawo kan kowanne ƙalubale.
A maimakon ka ji tsoro ko fargaba ka kalli kowanne ƙalubale a matsayin damar gwada ƙarfin zuciyarka da ƙarfin tunaninka. Abun al'ajabi ne yadda ƙalubale kan zama hanya mai sauƙi idan kana da cikakken imani da kanka, Allah yasa mu rabauta.
Lokuta da dama abubuwan da ke sauya yanayin mu ba shi ne ainihin abin da ke faruwa da rayuwar mu ba.
Rayuwar duniyar nan cike take da sauyi gami da ƙalubale ta hanyar natsuwa,haƙuri,godiya gami da fahimta za mu samu salama gami da sanyin ruhi.
A cikin wannan duniyar akwai abubuwa da yawa da ke iya tayar mana da hankali wanda idan hakan ya kasance ce dole tunanin mu ya dagule. Natsuwa ba wai kawai rashin motsin rai ba ne, tana da alaƙa da ikon mu wajen sarrafa zuciya da tunanin mu har su zauna lami lafiya cikin salama da annushuwa.
A yadda na yi nazarin rayuwar nan tamkar tafiya ce a cikin daji, sau da yawa muna hasarar hanya mu ci karo da duhu amma a ƙarshe duk wanda ya nace zai ga fitila.
Ilimin zaman duniya na koyar da yadda za mu rayu da juna cikin fahimta, haƙuri, da juriya. Manufar sa ita ce samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma ta hanyar girmama bambance-bambancen mutane.
Wannan ilimi yana taimakawa wajen kawar da tsana da rikici, tare da ilimantar da mu yadda za mu gina al’umma mai zaman lafiya da jituwa.
Wasu lokuta mukan ci karo da abubuwa marasa daɗi a rayuwa, amma juriya da haƙuri na taimakawa wajen guje wa damuwa.
Haƙuri yana haifar da kwanciyar hankali a zuciya.
Ɗabi'a tana nazari ne kan yadda ya kamata mutane su rayu da kuma kyawawan ɗabi'u da ya kamata su runguma. Aristotle ya gabatar da "Virtue ethics" inda ya ce "Ya kamata mu ƙoƙarta don zama mutane masu kyawawan ɗabi'u kamar adalci, jarumta, hikima da nagarta.". A nasa ganin Ɗan Adam zai iya samun farin ciki ta hanyar cimma nagarta, wanda ya kira ta da "Eudaimonia"(wato wanzuwar farin ciki).
Ku zaɓi burin da yake da ma'ana a gare ku sannan ku yi aiki tuƙuru don cimma sa amma kada ku manta da jin daɗin tafiyar rayuwa ba wai kawai kai wa ga manufa ba ce, ishe gamsheshshen cikar muradi shi ne abin dubawa.
Gaskiya na iya kasancewa tana da rassa musamman idan muka lura da yadda 'Yan Adam ke fassara gaskiya ta hanyoyi mabambanta, bisa ga fahimtarsu, al’adunsu, ko kuma ƙwarewarsu. Wato, wani abu da ya zama gaskiya ga mutum ɗaya, watakila ya bambanta ga wani.
Amma, idan ana maganar gaskiya ta asali, wasu na ganin cewa ita ƙwaya ɗaya ce wato tana nan a matsayin abu ɗaya mai zaman kansa ba tare da wani ɓangare ba. Wannan ra'ayi yana ganin cewa gaskiya ba ta sauyawa, duk yadda aka fassara ta.
Mu’amalar da ke tsakanin hankali da zuciya (Mind vs. Heart).
Masu goyon bayan hankali suna ganin ya kamata a yi duk wani abu ne bisa tsarin hankali da fahimta. Yayin da masu goyon bayan zuciya ko suke ganin cewa motsin rai da zuciya su ne ke bayar da shawarar ingantacciyar hanya. Wannan tunani ya samo asali ne daga falsafar da ta ke tambayar hanyoyin yanke shawara na Ɗan Adam, kuma yana jawo hankali sosai a yau musamman idan aka yi la’akari da yadda mutane ke fuskantar ƙalubale masu rikitarwa. Don haka zuciyar mutum (emotional heart) ita ce ke tsara masa shawarar duk abin da zai yi.
Ko kun san cewa biyan buƙatu yana farawa daga cikin zuciya ? Koyi da kyawawan halaye da inganta ƙwarewarku, kuma ku kasance da tabbaci a cikin duk abin da kuke yi.
Kowane mataki na gina kai yana kawo ku kusa da burinku. Ku yi haƙuri, ku yi aiki tuƙuru, kuma ku yi amfani da dukkan damarmakin da suka zo muku.
Tattalin arziki yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar mu, domin yana shafar kowanne ɓangare na zamantakewarmu. Yana bayar da hanyoyi da dama ga ci gaban al'umma, kamar inganta ilimi, kiwon lafiya, da samar da ayyukan yi.
A yau, muna fuskantar ƙalubale da dama, kamar talauci da rashin aikin yi, wanda ke nuna buƙatar ingantaccen tsari na tattalin arziki. Saboda haka, yana da muhimmanci mu fahimci yadda za mu inganta hanyoyinmu na gudanar da harkokin kasuwanci da ciniki, ta yadda za mu bunƙasa tattalin arzikimu da na al'umma baki ɗaya.
Mu lura, cewa duk da cewa kowanne mutum na da rawar da zai iya takawa, haɗin kai da kyakkyawan shugabanci su ne ginshiƙan da za su kai mu ga nasara. Ta haka, za mu iya inganta rayuwar mu da ta zukatanmu tare da gina makoma mai inganci ga al'ummarmu.
Kar ku manta cewa kowanne daga cikinmu yana da hikima da ƙarfi a ciki. Kar ku bar shakkunku da tsoro su hana ku cimma burinku. Ku tashi, ku yi aiki, ku zama waɗanda kuke son zama.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.