Kana fama da zafin talauci? Da rashin ci gaba a rayuwa? Shiga ɗaki. Ka rufe ƙofa. Ka kalli madubi, wane ne ka gani cikin madubin?
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Wannan da kake kallo, shi ne wanda ke da alhakin mafarkin da bai cika ba. Shi ne mai laifin faɗuwar burin ka, ɗan lalaci, ɗan fargaba, wanda yake gaza tsayawa ya fuskanci rayuwa.
Dole ka zage ka gaya masa maganganu kamar haka:
"Na gaji da zama a haka. Idan ba za ka tashi ba, to zan bar ka a baya."
Dole ka bar gida, ka bar danginka kuma ka yi watsi da abokanka.
Ka nemi inda babu wanda ya san ka. Ka hau titin da babu fuskokin da suka saba da kai, saboda gaskiyar magana ita ce:
"Ɗan Adam ba ya samun cikakken kuzari sai idan ya yi nesa da harshen da ya saba yi masa dariya".
Sai a lokacin za ka gane dalilin da ya sa mai kuɗin Afirka Aliko Ɗangote ya bar garinsa Kano kuma ya bar mahaifiyarsa Mariya Sunusi Ɗantata, kuma ya bar danginsa Alasawa masu tarin dukiya ya tafi Lagos don gina kansa.
Kamar yadda Ibn Khaldun ya ce:
“Rayuwa tana canjawa daga wuri zuwa wuri; wanda ya tsaya a wuri ɗaya, zai tsaya da cigaba.”
Ka je ka yi faɗa da rayuwarka a wajen da ba kowa ya san ka ba.
Ka yi aikin da ba ka taɓa tunanin za ka iya yi ba. Ka wanke mota, ka share titi, ka ɗauki kaya, ka zauna kasuwa, duk saboda makomar da kake so.
“Man is condemned to be free.” – Jean-Paul Sartre
Fassara
Mutum an haife shi da alhakin zaɓar makomarsa.
Babu laifi a ƙasa, amma laifi ne ka zauna a ƙasa har ka ji daɗin zama.
Kana jin daɗin zama amma aljihunka yana ƙonewa kamar kara a cikin gobara.
Ka yi ta tattakawa akan wahalhalun da na jikin madubin nan bai so.
Ka kakkarya shakkunsa. Idan ya ce "Ka gaji", ka ce masa "Gajiya ba tamu ba ce".
Idan ya ce "Za su yi min dariya", ka ce masa "To su yi ta yi har su gaji."
Saboda:
“The cave you fear to enter holds the treasure you seek.” – Joseph Campbell
Fassara
Ramin da kake tsoron shiga, shi ne ke ɗauke da dukiyar da kake nema.
Mun fi aiki idan muka fita waje, saboda babu wanda ya san mu.
Babu ido, babu tsoron abin da za a faɗa.
Muna zama kamar Ronaldo a cikin gasar Champions League.
Muna aikin da zai saka mu haskaka.
To me zai hana mu daina fargabar ido?
Ka tambayi zuciyarka: Shin kana rayuwa ne don jin daɗin mutane, ko don gina kanka?
Kafin ka fita daga madubin, ka ɗauki alƙawari:
"Zan dawo nan na sake kallonka, amma da kyau da girma. Kai da nake gani a yau, zan sa ka zama abin da kowa zai so ya gani a gobe."