Thursday 18 February 2021

Karanta Sababbin Sakonnin Soyayya Na Barka Da Juma'a

Tura Wannan Zuwa

GIMBIYATA


Fatana da burina a kullum, bai wuce na samun matsuguni a cikin zuciyarki ba. Manufata ki so ni, ki ba ni kulawa, ki zamo silar koruwar dikanin damuwata. Ina Son Ki.


Saƙon Barka Da Juma'a


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


KALMA


Ko da a ce ba ki furta min kowace irin kalma ba, a dukkan lokacin da na kalli fuskarki mai cike da annuri, na kan iya bayyana abun da ke a cikin zuciyarki. Wannan misali ne na yadda na damu da ke, fiye da yadda na damu da kaina. Ina Son Ki.


NAZARI


Na jima ina nazarin hanyoyin da zan bi wajen bayyana miki adadin yadda soyayyarki take a raina, amma yanzu na samo wata hanya guda, kin kuwa san wacce ce? Ta hanyar ƙara jaddada miki cewa INA SON KI! Ki Kula Min Da Kanki.


DAƊI


Soyayya na da matukar daɗi, ban tashi gane hakan ba sai da na same ki. Ko da a ce babu kowa a duniya, da iya ke kaɗai zan iya ƙare rayuwata. Fatana a ko da yaushe, ki kasance cikin jin yadda nake ji a kan ki. Ki Huta Lafiya.


KULAWA


Ba zan taɓa bari ki kuɓuce min ba, zan kasance cikin son ki tare da baki kulawa a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki.


TAMBAYA


Ina da wasu tambayoyi a gare ki. Shin me ya sa a dukkan lokacin da idanuwana suka yi tozali da ke, sai na ji zuciyata na kerma, ƙafafuwana na girgiza? Me ya sa nake jin kamar na mallaki komai na duniya, kuma na zama mutum mai sa'a? Tabbas,  ina ganin matsanancin son ki da na kamu da shi, shi ne amsar. Ina Son Ki.


NASARA


Dukkan wata nasara, ko wani ƙoƙarina na cimma wa ƙaddarata, da dukkan wani tinanina, ina yin su ne domin ke, domin yalwata farin ciki da jin daɗi a rayuwarki. Kina Raina, Domin Ina Son Ki.


HASASHE


A dukkan lokacin da nake tinani a kan soyayya, ina hasaso ki a cikin zuciyata. A dukkan lokacin da na ga wani abu mai tsananin kyau, kina bayyana a cikin tinanina. A dukkan lokacin da na shiga damuwa, na kan yi kewar rashin ki a kusa da ni. Amma a dukkan lokacin da nake cikin farin ciki, na kan rintse idanuwana, wanda a haka nake iya hango mu tare, mun zamo ango da amarya. Hm! Ina Son Ki.


RAYUWA


So abu ne da ke shammatar zuciya, ya sa idaniya kuka ko a wani lokaci ya sa mutum ya yi dariya. Ni dai na zamo mutum mai nasara, saboda samun ki a rayuwata ya nesanta ni da damuwa.


YANAYI


Ba wai kawai ina buƙatar martani ko kulawarki ba ne a soyayya, ina son ne, ki kasance cikin jin yadda nake ji a kan ki. Ki kasance cikin jin, zaki iya rayuwa da ni a kowane irin yanayi, kamar yadda nake ji a cikin zuciyata. Ina Son Ki.


TAFKI


Furta kalmar SO a gare ni ba shi ne iya abun da nake tsammanin samu daga gare ki ba, saboda shi SO bai yi kama da gadon furanni ba, haka kuma bai yi kama da kofin ruwan sanyi ba, wani fage ne mai tarin ƙayoyi, kuma shi tamkar wani tafki ne mai cike da muggan halittun ruwa. Fatana karda ki bar ni na sha wuya a cikin sa.


SO


Babu wani da zai iya bayyanar da halin da zuciya ke shiga a dukkan lokacin da ta kamu da so, har da ni ma nan, duk da na kamu da shi. Hakan ce ta sa na mallaka miki zuciyata, domin ki leƙa cikinta, ki ga irin yadda na kamu da son ki. Ba ni da kamar ya ke a wannan duniya. Ina Son Ki.


DALILI


Har yanzu jama'a sun gaza samo dalili, balle su samu amsar bayarwa ga tambayar, me ya sa nake son ki? Amma ke yanzu zan sanar da ke dalilin, ina son ki ne domin Allah, kuma ina fatan ki zamo uwar 'ya'yana. Ina nan cike da kewar rashin ganin Ki.


LAMBU


Tun bayan da na ɗanɗani yadda zaƙin soyayya yake, sai fuskata ta cika da murmushi, idanuwana suka daina ganin munin komai, ya zamana komai na burge ni. Dalilin samun wannan sauyin nawa, na ga yadda na samu sa'ar tsintar kyakkyawan fure a cikin lambun furanni. Ina fatan mu kasance tare, ni da ke har abada. Ina Son Ki.


IDANUWA


Ina fatan bayyana miki yanayin da nake shiga a kullum, a tsakiyar dare ko safiya, a lokutan cin abinci da na bacci, ina kasancewa cikin kewar rashin ganin ki a gefena, tare da jin, da ma na rufe idanuwana na buɗe na gan ki zaune a kusa da ni, da a wannan lokacin zan ƙara tabbatar miki da cewa INA SON KI!



KALMOMI


Jin wasu 'yan kalmomi daga bakinki, ka iya canja rayuwata, zan iya yin komai da kike so, matuƙar ina da dama, domin jin waɗannan kalmomi daga bakinki. Don Allah, ki daure ki furta min cewa, KINA SO NA.


MASOYINA


A dukkan lokacin da na kalli sararin samaniya, mai cike da tarin taurari, babu wani abu da nake fara tinawa face kai, saboda ka zamo tauraro mai haske fuska da zuciyata. Ina Son Ka.


CIWO


Tayaya zan iya bayyana maka yadda nake ji?  Wani zugi ne na ciwo mai tsananin zafi, wani abu ne mai kawar da ido daga ganin komai, ya kore yunwa daga jikina, ya koren jin sautin komai sai nasa, bana ganin komai sai shi. Wai shin mene ne wannan? To ba komai bane face KAI MASOYINA. Hmm! Ina Son Ka.


MAFARKI


Babu sama da SO daga cikin abubuwan da ke saka ni farin ciki da walwala a rayuwata. Soyayyarka ita ce abun da nake matsanancin so. Rayuwa tare da kai, shi ne mafarkina. Ka amince mu rayu tare, hakan shi ne cikar burina. Ina Son Ka.


LOKACI


Zan kasance cikin kewarka, ina mai tinanin irin tsawon lokacin da muka kasance tare, cikin so da ƙaunar juna. Fatana a duk inda kake, zaka kasance cikin tina cewa INA SON KA.


GIDA


Kai ne wanda nake tinani a tsakiyar dare, kuma kai nake fara tinawa da sanyin safiya. Kai ne abun so na a tsawon rayuwa, kuma kai ne wanda nake fatan na rayu tare da shi a gidan Aljanna. Ina matuƙar So da ƙaunarka.


HANZARTA DUBA WANNAN: Sauke Zafafan Sakonnin Soyayya Na Musamman Audio A Kyauta Anan


ZUCIYA TA


Son da nake yi maka, ba zai taɓa gushewa ko canjawa a cikin zuciyata ba, ko da a ce ka juyan baya, ni kuma zan zagayo na fuskance ka. Ina Son Ka.


SAKO MAI MUHIMMANCI


Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user