1. Rayuwa za ta iya sauya maka cikin gaggawa ba tare da ka shirya ba, kamar yadda mutuwar miji ya zama mabuɗin da munanan ƙaddarori suke faruwa da Asma'u.
2. Duk yadda miji yake son matar shi, matuƙar 'yan'uwansa da iyayensa ba sa son ta, za ta zama abar tausayi a lokacin da ba ya kusa, koda a ce ma ba mutuwa ya yi ba.
Ya kamata a ce duk yadda za ka yi ka ƙirƙiri zaman lafiya a tsakanin danginka da matarka, don gudun rusa tarbiyyar 'ya'yanka a lokacin da ba ka raye.
3. Al'ummar mu suna taimakawa da kaso mai tsoka wajen lalacewar mutanen da ke kusa da su, maƙwabta ko kuma wanda yake da halin taimako amma ya ƙi taimakawa Dan Allah sai ya nemi ya keta haddi.
4. Samun iyaye nagari rahama ce. Gaskiya babu ta yadda za a yi yaron da ya taso a gidan su Asma'u ya samu tarbiyya, kullum da ashariya ake karin kumallo a gidan, da faɗa da hayaniya, ƙarami ba ya ma babba biyayya.
5. Duk mace mai kishi irin na Samira, za ta iya aikata komai, kuma a ƙarshe ta ƙare a nadama.
Fim na farko da Kamfanin SRK Movies ya fara saki a sinima shi ne ‘Jaruma (2020)’ kuma ya samu matsakaiciyar nasara yayin haskashi. Wataƙila hakan ne ya bawa Kamfanin ƙwarin gwiwar ci gaba da sakin duk finafinansa a sinima. Sun saki ‘Makota’ a 2021, sai ‘Daga Dinner’ a farkon wannan shekarar (January, 2022). A jiya Juma’a kuma suka saki sabon shirinsu mai taken ‘A Bikin Suna.’
LABARI:
‘A Bikin Suna’ labari ne na Mustapha (Ali Nuhu) da matarsa Ummulkhairi (Mommy Gombe). Shekarunsu biyar da aure amma Allah bai nufe su da samun haihuwa ba. Wannan ne ya sa 'yan uwan Mustapha, su Musa Mai Sana’a, da mahaifiyarsu Hajiya Mama (Saratu Daso) suka kafawa Ummulkhairi ƙahon zuƙa. Kullum sai su yi ta mata gori cewa ita juya ce ba ta haihuwa. Abin ya ƙara ta’azzara bayan da Mustapha ya ƙi bin umarnin mahaifiyar tasa na ƙarin aure.
A ɓangare guda kuma, akwai Shamsu (Dan Iya) wanda shi ma ƙanin Mustapha ne, amma ba ya goyon bayan gallazawar da 'yan uwansa suke wa matar yayan nasa, hasalima soyayya yake da ƙanwarta, Ameera. Hakan yasa sauran 'yan uwan nasa shi ma suka juya masa baya. Ana cikin haka, cikin ikon Allah sai Ummulkhairi ta samu ciki, al’amarin da ya chanja komai da komai. Hajiya Umma ta fara nuna ƙauna da kulawa ga sirikar tata. Bayan haihuwar aka haɗa gagarumin bikin suna. A nan ne kuma sabon rikici ya ɓarke yayin da aka sace jaririyar ana tsaka da cashewa A Bikin Suna. Me ya faru daga nan? Ku je Film House Cinema da ke Shoprite Kano don ganin yadda ta kaya.
TA’ALIƘI:
‘A Bikin Suna’ fim ne a kan matsalolin auratayya, zamantakewa da zumunta. A fagen auratayya, mun ga yadda matsalar rashin haihuwa ta haifar da tangarɗa a rayuwar auren Mustapha da Ummulkhairi. Mun kuma ga yadda zamantakewa ta kasance tsakanin ma’auratan da 'yan uwansu. A ɓangaren zumunta kuma, mun ga yadda alaƙa ta lalace tsakanin Mustapha da ƙaninsa Habu (Musa Mai Sana'a), da yadda mahaifiyar Mustaphan ta yi fushi da shi har ma ta hana shi zuwa gidanta, sannan ta daina karɓar komai daga hannunsa.
Fim ɗin ya kuma nuna batun soyayya. Mun ga yadda soyayya ta ƙullu tsakanin Shamsu da Ameera, da kuma halin damuwa da Shamsun ya shiga yayin da masoyiyar tasa ta juya masa baya sakamakon cin mutuncin da 'yan uwansa sukai mata. Sannan akwai barkwanci sosai a fim ɗin, musamman wajen rawar da Musa Mai Sana'a ya taka.
Shirin ya ƙunshi darussa kamar su haƙuri, muhimmancin addu’ah da ilimi. Mun ga yadda Mustapha da Ummulkhairi suka yi haƙuri a bisa matsalar rashin haihuwa, suka yi ta addu’ah, Allah maji roƙo kuma ya biya musu buƙatarsu daga ƙarshe. Sannan mun ga yadda Habu ya kunyata a gurare biyu kasancewar ba shi da ilimin boko. Na farko, sanda shamsu yai masa gori, na biyu kuma sanda ya kasa karantawa Hajiya takardar asibiti. Bugu da ƙari, fim ɗin zai iya zama wata hanya da mutane za su koyi sabon salon gabatar da ‘Bikin Suna’, wato dai ya zama ana gudanar da shi a ƙawataccen waje mai kujeru, kamar yadda aka nuna a fim ɗin, saɓanin yadda aka saba yinsa a al’ada.
ABUBUWAN BURGEWA:
1. Labarin fim ɗin ya tafi kai tsaye zuwa manufar da ake son a cimma, kuma an tafiyar da shi bisa tsari ba tare da ya karye ba.
2. An sanya nishaɗi sosai a fim ɗin ta yadda ba zai gunduri mai kallo ba, duk da cewa labarin a karan kansa ba mai riƙe tunani da sanya zaƙuwa ba ne.
3. Ya ƙayatar sosai yadda fim ɗin ya kafa misalai da wasu abubuwa na zahiri da suke faruwa a tsakanin al’umma a daidai wannan lokacin, irin su ƙwacen waya, satar mutane, harkar Tiktok, yajin aikin malaman jami’a (ASUU Strike), da kuma irin fifikon da Jami’ar Bayero (BUK) take da shi a kan sauran jami’oin Arewacin Najeriya (kwanannan Times Higher Education World University Ranking ya tabbatar da haka).
4. Duka jaruman sun yi ƙoƙari wajen taka rawar da aka ba su. A wannan karon Musa Mai Sana’a bai yi over acting sosai ba. Shamsu Dan Iya da Sumayya Galadi sun haska. Haka ma Ali Nuhu, Saratu Daso da Mommy Gombe.
KURAKURAI:
1. Labarin bai tsaru da kyau ta yadda zai riƙe hankalin mai kallo ya sa shi tunanin abin da zai faru a gaba ba.
2. Wasu ƙwararrun jarumai a fim ɗin, kamar Maryam Yahaya da Teema Makamashi, ba’a ba su damar taka rawa sosai ba.
3. Kayan Ankon da maza suka saka a wajen bikin sunan, wanda yai kama da shigar inyamurai, kwata kwata bai dace ba.
4. Waƙar da Maryam Yahaya ta yi da saurayinta, wanda sau ɗaya kawai aka nuno su tare, ita ma ba ta dace ba. Kamata ya yi a ce Shamsu Dan Iya da Ameera ne suka yi waƙar saboda anfi nuna soyayyarsu.
5. A farko an nuna ƙannen ali Nuhu guda shida (6) ne, amma kuma sai aka ci gaba da nuna guda huɗu (4) kacal har zuwa ƙarshe.
ƘARƘAREWA:
Duk da cewa ‘A Bikin Suna’ shi ma an yi shi ne da irin salon sauran finafinan Kamfanin ‘SRK Movies,’ ya fi sauran tsaruwa. Na jinjinawa daraktan sa, Kamal S. Alkali, da ex-producer, Mal. Ibrahim Sharukh Khan.
Fim ne da tashar AREWA 24 ta fara nunawa a Litinin ɗin da ta gabata. Ibrahim Birniwa ne ya rubuta labarin, haka nan kuma ya ƙunshi 'yan wasa ƙwararru kamar, Nafisa Abdullahi, Garzali Miko, Ali Artwork Hadizan Sima, Hafsat Idris, Aminu Asid, Jazuli Mukaddas da sauransu.
Labarina yana bada labarin wata yarinya Sumayya (Nafisa Abdullahi) wadda ta kasance marainiya wadda mahaifinta ya mutu. Mahaifiyarta (Hadizan Sima) na fama da rashin lafiya, an kai ta asibiti sai dai ƙoƙarin neman kuɗin sayen magani ya jefa Sumayya a matsala, ban da harin fyaɗe da ɗan gidan matar da suke haya gidanta (Garzali Miko) ya nemi yi mata, akwai wani mai kemis a unguwarsu Nura (Aminu Asid) ya nemi ta ba shi haɗin kai kawai sai ya ba ta magungunan da aka rubuto wa mahaifiyarta, amma shi ba zai ba ta bashi ba.
Wannan ya tada hankalin Sumayya ta shiga neman mafita.
Mal. Aminu Saira yayin ɗaukar shirin Labarina Mai Dogon Zango
Hoto: Aminu Saira
Fim ɗin mai yanka-yanka (series) yanka na farko ya ƙare ne a inda Sumayya ta ga ba mafita ta koma wurin Nura tare da amincewa buƙatarsa.
Fim ɗin ya yi kyau ƙwarai, musamman yadda labarin ya tafi tiryan-tiryan ba karyewa, mai yiwuwa saboda ya haɗu da ƙwararren Marubuci ne.
Jarumi Rabi'u Rikadawa a matsayin Baba Ɗan Audu yayin ci gaba da ɗaukar shirin Labarina Mai Dogon Zango
Hoto: Aminu Saira
'Yan wasa sun taka rawa sosai, ta yadda za ka ga tamkar gaske ne.
Idan ka fara kallon fim ɗin ba za ka so tashi ba har sai ka ga yadda za a ƙarke.
Sauti da hoto sun fita raɗau! Ba laifi.
Tambaya Da Shawara
Babu wani mai kemis a faɗin garin ban da Nura ne, an ga Nafisa tana ta jele wurinsa.
Yana da kyau a nuna ta je wani ɗakin shan maganin, idan ya so sai a ce ai babu wasu magungunan.
Jarumai: Umar M. Sharif, Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Hassana Muhammad, Maryam Yahya, Amal Umar, Bilkisu Shema, Aisha Humaira, Abba El-Mustafa, Asma’u Sani, Jamila Umar Nagudu, Aisha Yola. Da sauran su.
Sharhin Fim din Hafeez
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Salma (Aisha Humaira) suna hira da kanwarta Saudat (Amal Umar) a sannan ne kuma mahaifiyar su (Asma’u Sani) ta shigo dakin ta kira Salma da nufin taje wajen bakon saurayin ta Hafiz wanda yazo gidan, jin hakan ne yasa Saudat ta soma yabawa da Hafiz amma sai Salma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar gargadin ta akan kada ta shiga sabgar sabon saurayin ta.
Sai dai kuma cikin rashin sa’a, bayan Salma ta fita zuwa wajen Hafiz tun a haduwar farko yaji bata birge shi ba saboda sabanin fahimta da suka samu wanda ya janyo sanadin day a mari Salma din kafin ya bar gidan.
Amma kuma duk da wulakancin da yayiwa Salma mahaifiyar ta bata ji haushin abin ba sai ma laifin Salma din da take gani saboda ta bata mata shiri domin ta kasha kudi masu yawa a wajen malamai don a jawo mata hankalin Hafiz zuwa kan ‘yar ta saboda kasancewar shi dan masu kudi, a dalilin haka ne ma yasa bayan kanwar Salma ta samu mahaifiyar tasu da rokon a shawo mata kan Hafiz ko ita zai saurare ta, mahaifiyar ta su bata bata lokaci ba wajen daukar Saudat din suka nufi gidan iyayen Hafiz.
Amma duk da kasancewar mahaifiyar Hafiz wato Azeema (Jamila Nagudu) ta kasance aminiya ga Mahaifiyar su Salma (Asma’u Sani) Hakan bai sa Azeema tayi kokarin tilastawa Hafiz akan yayi soyayya da Saudat ba, domin shi dan gata ne sosai a wajen iyayen nasa wadanda ba sa son ganin abinda zai bata masa rai. Shima kuma Hafiz ko bayan day a shigo gidan ya hadu da Saudat sai ya fice daga gidan saboda ganin yadda take kallon shi, amma duk da haka sai da Saudat tabi bayan shi zuwa waje inda ta nuna masa cewar tana kaunar shi, nan Hafiz ya watsar da ita ba tare daya karbi soyayyar ta ba.
Shi dai Hafiz ya taso mutum me tsananin farin jini a wajen ‘yammata, duk budurwar da ta gan shi sai taji ya birge ta kuma ta fara soyayya dashi, akwai ba don komai ba sai don kyau da iya kwalliyar sa gami da kudin da mahaifin shi ya mallaka wanda yake takama dasu. Babban abin takaicin kuma shine, Hafiz sam bai taba ganin yarinyar da ta birge shi ba akaf cikin ‘yammatan da suke zub da ajin su wajen nuna masa cewar suna son shi, gaba daya wulakanci yake yi musu bay a basu fuskar da zasu rayu tare, yayin da a kullum iyayen shi ba su da burin da ya wuce su ga yayi aure ya zauna da iyalin sa.
Hakan ne kuma yasa iyayen shi suka bashi goyon baya wajen zuwa ya ga ‘yar abokin mahaifin sa ko zasu daidaita har ya aure ta, amma cikin rashin sa’a Hafiz sai yaga itama yarinyar bat a birge shi ba, hakan yasa yayi mata kyautar kaya yayi tafiyar sa, wanda ganin haka sai ya yiwa mahaifin yarinyar ciwo (Abba Al-Mustafa) saboda yana matukar son Hafiz ya auri ‘yar shi ko don hakan ya zamo sanadin wani cikar burin sa, dalilin hakan ne yasa yaje ya sanar da mahaifin Hafiz wato (Yakubu Muhammad) cewar Hafiz ya amince da auren ‘yar sa, amma ko da mahaifin Hafiz ya tuntube sa sai ya nuna sam ba haka bane.
Ana tsaka da haka ne Hafiz ya hadu da Safna (Hassana Muhammad) wadda ta kasance ‘yar talakawa, tun daga sanda ta taimakawa da Hafiz ruwa ya zuba a motar shi sai yaji ta birge shi har ya kamu da son ta, sai dai kuma tun daga lokaci na farko day a fara zuwa hira wajen ta yaci karo da mahaifin ta Malam Sada (Ali Nuhu) sai hankalin Hafiz ya tashi, domin ya taba cin zarafin Malam Sada ya ture shi da mota har yaji masa rauni kuma ya soma kokarin dukan Malam Sada din.
Ko da Hafiz ya fahimci cewar Malam Sada ne mahaifin Safna sai hankalin shi ya tashi amma son da yake mata ne yasa ya kasa hakuri da ita yayi yunkurin turo iyayen sa, sai dai kuma Malam Sada yaki yarda da auren Hafiz da Safna saboda wulakancin da Hafiz din yayi masa. Ganin yadda Hafiz ya rikice akan son Safna ne hakan yasa iyayen sa suke takaici saboda ba ‘yar masu kudi ya nema ba, amma son da suke yiwa Hafiz ne yasa suka yi ta kokarin ganin cewar an daidaita da mahaifin Safna, ana cikin haka kuma sai aka tashi mahaifin Safna wato Malam Sada daga gidan da yake haya, hakan ne yasa ya hada kan iyalan sa gaba daya ya koma kauye, duk da kafin tafiyar shi, mahaifin Hafiz yayi masa tayin muhalli amma Malam Sada yaki amincewa domin shi mutum ne me zafin zuciya da gudun abin hannun wasu.
Ko da Hafiz ya samu labarin cewa Safna sun koma kauye sai ya gujewa iyayen sa ya tafi kauyen su Safna don neman soyayyar ta. Bayan zuwan Hafiz kauyen ne da yadda yake yin wahala sai abin ya soma bawa Malam Sada tausayi wato mahaifin Safna har daga karshe ya amince da nadamar Hafiz sannan ya bawa Hafiz din dammar turo magabatan sa don ya aura mishi Safna.
Abubuwan Birgewa:
1. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa sannan an nuna tsantsar soyayya muhimmancin da jajircewa kan abinda mutum yake so.
2. Daraktan fim din yayi kokari wajen tafiyar da labarin bisa tsari ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari sosai.
3. Sauti ya fita radau, hoto ma ba laifi
4. An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.
5. Wakokin fim din sun yi dadi kuma sun nishadantar.
Kurakurai:
1. Lokacin da Malam Sada (Ali Nuhu) yaje neman rancen kudi a wajen wani me kanti, da kuma lokacin daya dawo gida sa’in da akayi masa rauni a kafar sa, muryoyin jaruman basu hau da bakin su ba a wuraren.
2. An nuna cewar iyayen Hafiz masu kudi ne kuma suna nuna masa gata da tsantsar kulawa, amma kuma lokacin da Hafiz ya gujewa iyayen na sa ya tafi kauye wajen masoyiyar sa, me kallo bai ga sun yi yunkurin neman shi ba. Ya dace a nuna cewar sun watsa cigiyar sa ko da ta kafafen sadarwa ne.
3. Me kallo yaga Hafiz ya taso cikin gata da sangarta daga wajen iyayen sa, wanda hakan ya ba shi damar da ya ke cin mutuncin duk wanda ya so, musamman na sama da shi, amma sai ga shi kuma lokacin da Hafiz ya gane kuskuren da yayi wajen cin zarafin Malam Sada mahaifin budurwar sa, wanda har Hafiz din ya bar gaban iyayen sa don neman soyayya da kuma yafiyar mahaifin budurwar tasa, duk da ganin faruwar hakan amma ba a nuna cewar iyayen Hafiz sun yi nadama ba a bias tafarkin da suka dora dan nasu na rashin tarbiyya, ya dace a nuna cewar sun yi nadama ko don ganin illar da rashin tarbiyya ta ja wa Hafiz wanda abin ya zamo sanadin da Hafiz ya nisance su.
4. Shin wace irin sana’a mahaifin Hafiz yake yi ne? An nuna cewar Hafiz ya taso cikin gata da tunkaho da dukiyar mahaifinsa, sai dai kuma har fim din ya kare ba a nuna irin sana’ar da mahaifin nashi ya ke yi ba wadda ta sa ya mallaki dukiya me tarin yawan da a ke fada.
Fim din ya fadakar kuma labarin ya yi nasara wajen rike mai kallo, sannan kuma an nuna tsantsar soyayya gami da muhimmin darasi a kan wasu matasan masu ji da giyar kudi, wanda hakan ke sa wa su wulakanta makaskanta, yayin da daga karshe su ke yin nadama a kan hakan. Wallahu a’alamu!
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Suna: Namijin Kishi. Tsara labari: Yakubu M. Kumo. Kamfani: Kumo Production. Daukar Nauyi: Yakubu M. Kumo. Shiryawa: Sale Yaro. Bada Umarni: Ali Gumzak Sak.
Fim din “Namijin Kishi” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani bawan Allah mai Suna Habibu (Sadik Sani Sadik). Habibu wani mutum ne mai fama da tsananin kishi a kan matarsa wato Fa’iza (Hafsat Idris). Kishinsa ya sa ko unguwa ba ya bari ta fita, ko da gidansu za ta je ba ya bari ta je ita kadai, sai dai ya je ya kai ta ya zauna ya jira ta. Haka Fa’iza ta ringa rayuwa cikin matsi sakamakon tsananin kishin mijinta. Hatta ‘yan uwanta na jini maza ma idan su ka je gidanta sai ya nuna bacin ransa a kan hakan. A sakamakon hakan ne, ‘yan uwan nata ma duka su ka kauracewa zuwa gidan nata.
Zaman Habib da Fa’iza bai wuce wata hudu ba, amma saboda tsabar tsananin kishinsa har ya yi mata saki har guda biyu a kan dalilan da ba su taka kara sun karya ba. Hakan ya sa saura igiyar aurensa daya ce ta rage a kan Fa’iza. Mahaifiyar Habib da kawunsa su na masa fada a kan ya kiyaye a kan maganar Fa’iza, saboda sun tabbata idan har bai daina wannan mahaukacin kishin nasa ba to tabbas zai karasa wannan saki dayan da ya rage a tsakaninsu.
Wata rana mahaifin Fa’iza wato Alhaji (Shehu Hassan Kano) ya kawo mata ziyara, suna cikin hira sai ga Habibu ya dawo daga aiki kawai da ya shigo ya jiyo muryar namiji a cikin falon gidanshi, kawai sai ya dakko katako ya nufo falon da gudu. Ya na shigowa a fusace kawai sai ya ga ashe Alhaji ne, nan dai ya yi ta bawa Alhaji hakuri yana cewa a yi masa afuwa kuskure ne wallahi ai bai san shi bane.
Ana nan dai watarana Babar Fa’iza ba ta da lafiya, sai Fa’iza ta nemi izinin Habib a kan tana so ta je, sai ya ce mata ta bari ya dawo sai ya kaita. Karshe dai da a ka kara kiran ta a ka sanar da ita cewa jikin ya yi muni, shi ne kawai ta kirawo Habib ta ke fada masa cewa za ta fita ta hau babur din haya ta tafi saboda jikin Hajiyar ya yi tsanani. Sai ya ce mata kada ta hau babur ta jira shi, sai ta fita ta hau babur kawai ta kyale shi ta yi tafiyarta . A haka kuwa a ka samu tsautsayi sai ta yi hatsari a hanya. To a lokacin shi ma Habib ya yanke shawarar cewa kawai zai dawo ya dauke ta ya kai ta gidan da kansa.
A hanyar tahowar tasa ce, kawai sai ya ga taron mutane a wani guri, yana lekowa kawai sai ya ga Fa’iza a zaune cikin jini a tsakiyar maza. Shi ne a ke bashi labarin ai hatsari su ka yi a hakan ma sai da wani ya dakko ta ya dawo da ita gefen hanya da tuni mota ta take ta. Ai kuwa yan jin cewa namiji ne ya dakko ta ya kawo ta gefen hanya, kawai sai Habib ya fadi a sume, daga nan a ka kwashe su sai a asibiti.
Habibu yana farkawa ne sai ya nufo inda Fa’iza take, isowarsa ke da wuya kawai, sai ya tashe ta ya rufe ta da fada yana zagin ta yana cewa ta ci amanarsa. Kawai Habib yana bude baki sai yace ya saki Fa’iza. Yana sakinta sai ga Alhaji ya shigo dakin, sai Fa’iza take fada masa ai Habib ya sake ta. A nan ne fa Habib ya fara cewa shi fa da wasa yake ba sakin ta ya yi ba. Shi ne Alhaji ya fara fada masa magana yana cewa to ko kai mahaukaci ne Fa’iza ta kwace maka kenan har abada.
A haka dai Habib ya yi ta rayuwa cikin kunci a sakamakon sakin Fa’iza. Ya koma tamkar mahaukaci, kullum cewa ya ke shi fa sai Fa’iza ta dawo gidansa wai shi ai ba sakin ta ya yi ba. Haka ya yi ta yawon bin malamai wai yana so a ba shi wata fatawar da za ta iya saka matarsa ta dawo izuwa gareshi. Amma ko’ina ya je ana fada masa cewa matarsa fa ba za ta dawo gareshi ba har sai wani ya aure ta sun rabu, to sannan ne za ta iya dawowa izuwa gareshi.
A karshe dai haka dole Habib ya hakura da Fa’iza. Ta yi aure ta auri Ahmad (Ali Nuhu), bayan ‘yan sanda sun kama Habib sakamakon naushin da ya yi wa Ahmad. A karshe shi ma Habib dole ya yi hakuri da Fa’iza, ya je ya sake aure shi ma. Bayan ya dawo cikin hankalinsa ne, sai a ka maida shi gurun aikinsa bayan dakatarwar da a ka yi masa a baya. Kuma sannan ya ci-gaba da rayuwarsa kamar yadda ya kamata.
Namijin Kishi
ABUBUWAN YABAWA
1. Sunan Fim din ya dace da labarin duba da irin namijin kishin da Habib ya ke nunawa a cikin fim din.
2. Fim din ya samu aiki mai kyau, saboda ba a samu matsaloli masu yawa a cikinsa ba.
3. Labarin ya samu nasarar rike mai kallo tun daga farko har karshe.
4. Labarin mikakken labari ne, bai karye ba tun daga farko har karshe.
5. Jaruman cikin fim din sun taka rawa mai kyau a ciki, musamman Habib da Fa’iza sun taka rawa sosai a irin fitowar da su ka fito a ciki.
6. An nuna tasirin soyayya ta gaskiya, domin duk da abinda Habib ya ke yi wa Faiza tana son shi duk da haka, saboda ta san soyayya ce ta saka yake yin wannan tsananin kishin a kanta.
7. Nadamar da Habib ya yi a karshe, zai zama izina ga masu irin tsananin kishi irin na shi.
Namijin Kishi
KURAKURAI
1. Kalaman da Mu’azzam kanin Fa’iza ya zo yana fadawa Mamansu a gida bayan ya dawo daga gidan Fa’iza a lokacin da Habib ya kama yi masa fada saboda ya kwanta a kan kayanta, sam ba su dace da maganganu da ya kamat da ya yi a gaban mahaifiyarsa ba.
2. A lokacin da Habib ya kai Fa’iza asbiti har ya ke cewa ba za a yi mata (scanning)ba, idan har babu likita mace a asibitin, kalaman da ya ringa fadawa likitan a lokacin da su ke asibitin sam basu da ce a ringa fadar su a wannan gurun ba.
3. Ya kamata a nuna Ahmad da Fa’iza a gidansu bayan sun yi aure koda sau daya ne.
4. Ya kamata ace an nuna lokacin da Habib ya yi wa Fa’iza saki biyun farko bayan aurensu, domin masu kallo su kara fahimtar labarin sosai.
KARKAREWA
Fim din “Namijin Kishi” fim ne da ya bayyana irin tsananin kishi wanda Habib ya ke yi wa matarsa Fa’iza, sai dai kishin nashi ya wuce ka’ida, wanda hakan ne ma ya jawo masa nadama a karshe. Tabbas abu ne mai kyau ga dukkan wanda ya san mai yake da ya ringa nuna kishi ga matarsa. Sai dai kodayashe ana so kada kishin ya wuce ka’ida. A karshe dai an ga yadda wannan zazzafan kishin na Habib ya kai shi ga yi wa Fa’iza saki har guda uku, wanda hakan ya tilasta masa rabuwa da ita duk da irin kaunar da yake mata. Sannan yana da kyau masu bada umarni a fim su ringa kula da irin kalaman da ya kamata su ringa amfani da su a cikin fina-finansu, saboda ya zama ya zo dai-dai da tsari da kuma ka’ida.
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Suna: Salma Bankwana. Daukar Nauyi: Nura M. Inuwa. Kamfani: ABNUR Entertainment. Shiryawa: Abdul Amart. Bada Umarni: .Sadik N. Mafia.
Salma Bankwana
SHARHI: Musa Ishak Muhammad
Jarumai: Adam A. Zango, Fati Washa, A’isha Aliyu Tsamiya, Hadiza Muhammad, Baballe Hayatu, Balarabe Jaji, Asamau Sani, Alasan Kwalli, Malam Inuwa, Bankaura, da sauransu.
Fim din “Salma Bankwana” fim ne da aka gina shi a matsayin ci-gaban fim din “Salma.” Fim ne da yake dauke da labarin wani matashi mai suna Naseer (Adam A. Zango) mai tsananin soyayya ga kanwarsa kuma budurwarsa wato Salma (A’isha Aliyu Tsamiya). Sun kasance suna tsananin kaunar junansu, domin kuwa sun shaku sosai, sai dai kash! Salma ta rasa rayuwarta sakamakon hadarin mota da ya ritsa da ita a lokacin da ta tafi Sakkwato domin rabon katin bikinsu da Naseer.
Rasuwar Salma ta zowa Naseer da wani irin yanayi mawiyaci, wanda hakan ne silar susucewar komai nashi. Saboda a kullum ba shi da abun yi idan ba tunaninta da anbatonta ba. Ta kai har sunbatu ya ke a kanta. A bangare guda kuma akwai Minal wadda take tsananin kaunarsa wadda hakan ya tilasta mata yin komai irin na Salma domin ta samu shiga a gurun Naseer.
Wannan shi ne a takaice abunda ya faru a cikin fim din Salma wanda kuma shi ne tushe na wannan fim mai suna “Salma Bankwana.” A haka Naseer ya ci gaba da rayuwa cikin tsananin kewar Salma da kuma bayyana irin tsananin kaunar da yake mata duk da ce wa bata raye, domin har fada yake cewa shi fa a gurunsa Salma bata mutu ba domin tana rayuwa ne a cikin zuciyarsa.
Ita kuma Minal tana ta ci gaba da shirye-shiryen yadda zamanta sai kasance da Naseer domin kuwa an kusa aurensu. Tana ta shirin ya za ta yi ta saka shi ya manta da Salma sannan ya maye gurbinta a zuciyarsa da ita. Sai dai tun kafin auren nasu, Naseer ya sha fadawa Minal cewa dole sai ta yi hakurin zama da shi saboda shi bazai taba yi wa wata mace irin son da ya yi wa Salma ba.
A daya bangaren kuma, a can gidansu Naseer wato gidan da suka rayu da Salma a lokacin da take raye, akwai kanwar Salma mai suna Sakina wadda ita ma take cikin tsananin son Naseer sai dai ta kasa samun amincewarsa, saboda ya ce dabi’unta sam ba su yi kama da na Salma ba, saboda haka ba zai taba aurenta ba. Duba da irin mawiyacin hali da Sakina take ciki ne yasa mahaifinta wato Alhaji wanda shi ne ya rike Naseer a gidansa tun yana karami, ya kirawo Naseer a kan ya daure ya auri Sakina duba da cewa ita kadai ce ta rage musu a rayuwarsu tunda Allah ya karbi rayuwar Salma kuma basa so ita ma su rasa ta saboda ciwon sonsa. Sai dai a nan ma Naseer ya kara bayyanawa Alhaji cewa fa sai dai a yi hakuri saboda gaskiya shi bazai iya auren Sakina ba.
Bayan an yi auren Naseer da Minal, Minal ta fara karo da matsaloli tun a daren da aka kai ta gidan Naseer, domin ya ringa kiranta ne da sunan Salma wanda hakan ya yi matukar bakantawa Minal rai, sai dai ya bata hakuri da neman cewa ta yi masa uzuri. A Haka dai tayi ta rayuwa cikin kunci a gidan Naseer domin kuwa kullum haukarsa a kan Salma kara bayyana take.
Kullum kokarinta shi ne ya za a yi Naseer ya dan bata dama domin ta bayyana irin cikakkiyar soyayyar da take masa, amma sai dai hakan yaki samuwa. Haka Naseer ya bi ko’ina a cikin gidan nan ya cike shi da hotunan Salma, amma Minal duk tayi hakuri saboda burinta na ganin farin cikin mijnta.
Hakurin Minal ya je karshe, domin kuwa wata rana ta dauki hoton Salma ta yi jifa da shi a kasa wanda hakan ya saka ya farfashe, ai kuwa nan take Naseer ya hau dukanta. Yana cikin dukan nata ne sai ga mahaifiyarta Hajiya Balaraba (Asamau Sani) da kaninta Bashir (Abba Kabugawa) suka shigo, suna shigowa ne fa suka samu Minal tana ta kuka shi kuma Naseer ya biyo ta da gudu yana fadawa mahaifiyarta cewa wai Salma ta kirawo da gawa. A nan ne dai Hajiya Balaraba ta dauke Minal ta tafi da ita gida kuma ta ce mahifin Minal sai ya nemar mata hakkinta. Wanda sakamakon hakan ne aka saka ‘yan sanda suka shigo har gida suka kama Naseer aka je aka kulle shi.
A karshe bayan an fito da Naseer daga hannun ‘yan sanda, Shi ne Alhaji wato mahaifinsa na ruko ya dauke Naseer da abokinsa Kabeer (Baballe Hayatu) zuwa gurun Malam (Malam Inuwa) inda a nan ne aka yi wa Naseer wa’azi mai nawi da ayoyi da hadisai, wanda hakan ya zama silar yin nadamarsa a kan irin abubuwanda ya aikata. Sannan ya kirawo Minal ya bata hakuri, kuma ya yi mata alkawarin daina dabi’un da yake, wanda bayan ta amince ta dawo gidanta ne a ka nuno shi ya dakko duka hotunan Salma da suke gidan yana kona su. Sannan kuma ya koma gida ya yi wa Sakina alkawarin zai aureta yanzu.
Abubuwan Yabawa
1. Sunan Fim din ya dace da labarin.
2. Labarin mikakken labari ne wanda bai yanke ba tun daga farkon shi har karshensa.
3. Fim din ya samu aiki mai kyau kwarai da gaske.
4. Jaruman duka sun dace da labarin duba da irin rawar da kowanne ya taka a gurbinsa.
5. An samu kalamai na kwarewa a cikin fim din.
6. An nuna tasirin yin soyayyar gaskiya, domin tana yin tasiri sosai idan an gina ta a kan gaskiya.
7. An nuna tasirin samun mace ta gari domin dabi’un Salma kyawawa da kuma addinin da take da shi, su ne suka saka Naseer yake mata irin wannan so din.
Salma Bankwana
Kurakurai
1. Duk irin abinda Malam ya fadawa Naseer wanda har suka zama silar chanjawar sa,an fada masa irin su a baya amma mai yasa bai canja tun a lokutan ba har sai da aka zo gurun Malam sannan?
2. Lokacin da aka nuna Naseer yana tuna lokacin da yake fadawa Salma cewa yana so ya mallaka mata rabin dukiyarsa, ba a nuna wa mai kallo cewa za a shiga tunani ba kuma ba a nuna masa an dawo ba,
wanda hakan zai sa mai kallo ya yi zaton cewa ita ma wannan fitowar da aka nuna ana tunanin, ba wai tunanin bane.
3. Ya kamata a dan nuna rayuwar Minal da Naseer a gidansu bayan ya canja domin a nuna ta samu farin ciki ko yaya ne a gidanta.
4. Irin kalaman da Naseer yake amfani a kan kowa wajen bayyana irin son da ya ke yi wa Salma suna yin tsauri da yawa, duba da irin yadda yake magana da iyayensa da kuma sirikarsa akan Salma.
Karkarewa
Fim din “Salma Bankwana” fim ne da ya nuna irin yadda ake samun wasu sukan samu kansu a cikin matsananciyar soyayya da kuma irin halin da suke samun kansu a ciki.
An nuna tsantsar soyayya ta gaskiya a cikin fim din da kuma irin tasirin da take yi a cikin zuciyoyin maabotanta.
Sannan an nuna kwarewa sosai a cikin aikin fim din, domin kun an samu nasarori da yawa kuma ya kayatar da mai kallo.
Kuma ba a samu kurakurai da yawa a cikin fim din ba.
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Suna: Matar Mijina Tsara Labari: Nazir Alkanawi Kamfani: S.H Ea: Abdul Amart Umarni: Sadik N. Mafia
Matar Mijina
Jarumai: Adam A. Zango. Aisha Aliyu Tsamiya, Fati Washa, Umar Gombe, Maryam Ceeter. Da sauran su.
A farkon fim din an nuna Mutallab (Adam A. Zango) Yana bacci a cikin daki yayin da ‘ya’yan sa Yusra da Salim suka shiga suka tashe sa don yayi Karin kumallo. Bayan Mutallab ya tashi ya kimtsa ne ya fita wajen aikin sa, a sannan ne Suwaiba (Maryam Ceeter) tazo wajen Matar sa wadda ta kasance kawa ce a wajen Suwaiba. Suwaiba ta kasance tana nuna wa Jalila (Aisha Aliyu Tsamiya) aibun auren da tayi gami da ajiye karatun tan a jami’a ta zabi aure, yayin da Jalila take nuna mata hakan ba laifi bane saboda tana jin dadin irin soyayyar da mijin ta Mutallab yake nuna mata. Suwaiba tana kokarin zuga Jalila don kada ta cigaba das akin jiki da mijin ta Mutallab saboda gudun kada ya karo mata kishiya, amma Jalila tana nuna ko da hakan ta kasance ba laifi bane zata iya zama da kowacce mace wadda mijin ta zai aura. Wata rana Mutallab ya hadu da wata budurwa Samira (Fati Washa) wadda yaji ta birge shi kuma yana son auren ta, hakan ne yasa ya fara nuna wa Samira kudurin san a son auren sa kuma cikin dan lokaci kadan Samira ta amince da bukatar sa suka fara soyayya. Mutallab ya sanar da matar sa Jalila cewar yana soyayya da Samira sai hakan bai dameta bat a nuna masa goyon bayan ta akan auren da zai kara, har ya zamana cewa Mutallab yakan hada Jalila da Samira a waya su gaisa har ma suyi hira, sannan kuma yakan dauki ‘ya’yan sa Yusra da Salim ya kais u wajen Samira su gaisa. Tun Samira tana ja baya da Jalila hart a saki jiki da ita kuma ta fahimci cewa Jalila mace ce mai son zaman lafiya wadda kuma bata damu da soyayyar da ake yi da mijin taba. Wata rana Suwaiba kawar Jalila ta fito tare da kawayen ta daga cikin makaranta sai taga Mutallab ya budewa Samira motar sa yaja sun tafi, hakan ne ya kidima tat a garzayo ta sanar da kawarta Jalila abinda idanun ta suka gani, amma sai Jalila ta nuna rashin damuwar ta akan abin duk da Suwaiba ta nuna mata cewar yarinyar da ta gani tare da Mutallab bata da nutsuwa, amma yardar da Jalila tayi da mijin ta itace tasa ta gamsu da cewar ba zai ci amanar taba. Cikin dan lokaci kadan aka bikin Mutallab da Samira ya gabato, wanda hakan yasa Jalila ta soma gayyatar jama’a da sauran dangin ta har ma ta fidda kalar ankon da za su saka ranar biki. Hakan ne yasa wasu daga cikin ‘yan uwan ta suke kokarin zuga ta don kart a amince da hakan, yayin da wasu dangin nata kuma suka yi fushi da ita suke ganin kamar bata da hankali saboda tana murna don za’a yi mata kishiya. Ana ya gobe daurin aure sai Mutallab yayiwa Jalila sallama ya koma dakin hotel tare da abokan sa don su samu sakewa saboda baya son hayaniyar jama’a ‘yan biki. Kwatsam ana tsaka da shagalin biki sai ga Suwaiba kawar Jalila ta zo ta tabbatar mata da cewar Samira amaryar da za’a kawo mata tana dauke da cutar kanjamau, saboda abokin tan a makaranta wanda ake zargin tana mu’amula dashi an gane cewar yana dauke da wannan cutar. Jin hakan ne ya tashi hankalin Jalila ta kira mijin tat a nuna kada a daura wannan auren, amma sai Mutallab yayi zaton cewa kishi take da abin sai yaki saurarar ta. Sai dai kuma tun bayan auren Samira da Mutallab sai Jalila taja jikin ta gefe ta daina mu’amula da mijin ta, sannan kuma taki amincewa akan ya kusance ta saboda tana ganain cewa shima ya kamu da wannan cuta ta kanjamau. Hakan ne yasa ko ya kwana a kan gadon ta sai ta cire shimfidar gadon ta kona saboda kyankyamin sad a take yi. Ganin abinda ke faruwa ne yasa Mutallab ya soma nadamar karin auren da yayi saboda baya son abinda ke faruwa tsakanin sad a Jalila. Hakan ne yasa ya kira iyayen Jalila don su tuhume ta akan abubuwan da take yi masa, a sannan ne Jalila ta basu labarin abinda Suwaiba kawarta ta gaya mata, jin hakan ne kuma yasa Samira ta karyata cewar tana dauke da cutar kanjamau, wannan daalilin ne kuma yasa aka je asibiti akayi gwaji wanda ya tabbatar da cewa Samira da Mutallab bas u da wannan cuta ta kanjamau. Faruwar hakan c eta sa Jalila tayi nadama kuma ta roki gafarar mijin tad a ta Samira, wanda hakan yasa lokacin da Suwaiba ta sake zuwa gidan suka hadu gaba daya sukayi mata duka don kokarin kawo karshen munafurcin ta.
Abubuwan Birgewa:
Labarin ya tafi kai tsaye har ya adire bai karye ba.
Sunan fim din ya dace da labarin.
Daraktan yayi kokari wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace, haka kuma yayi kokari wajen ganin cewa jaruman sun isar da sakon da ya dace, domin sun yi kokari wajen isar da sakon da ya dace. Hoto ya fita sosai, haka ma sauti ba laifi.
Kurakurai:
Bayan auren Mutallab (Adam A. Zango) da amaryar sa Samira (Fati Washa) me kallo ya gan su a wani falo na daban wanda bai yi kama da gidan sa da aka fara bayyanawa a fim din ba, sannan kuma yanayin da aka nuna kamar dama a gidan suke, shin canja gida suka yi? Idan kuma gidan bangare biyu ne to ya kamata tun a farko a bayyanawa me kallo, duk da dai yanayin yadda aka bayyana tsarin gidan a baya bai yi kama da cewar bangare biyu bane.
Lokacin da Jalila (Aisha Tsamiya) ta sami labarin cewa amaryar da mijin ta zai aura tana dauke da cutar kanjamau, me kallo yaga tana guje masa domin ko zama a inda yake bat a yi, wanda bayan ya kwanta akan shimfidar ta ma sai ta kona zanin gadon duk da shima zanin gadon bata taba shi da hannu ba har sai da ta sa leda ta rufe hannuwan nata, sannan ta dauka ta kona, shin Jalila ba ta san cewa ba a daaukar cutar kanjamau ta hanyar zaman takewa da masu cutar ba? Tun da an nuna cewar tana da ilimin addini da na zamani gami da fahimta, bai dace kuma a nuna cewar ta kona shimfidar da mijin ta ya kwanta ba don gudun kamuwa da cutar da take zargin sad a ita.
Lokacin da Jalila ta fara fadawa kawarta Suwaiba labarin cewa mijin ta zai kara aure, bayan tafiyar Suwaiba me kallo yaji muryar ta a waya sa’in da ta kira Jalila tana sanar da ita cewar yarinyar da mijin ta zai aura tana saka hotunan sa Instagram, haka zata zuba idanu bazata dau mataki ba, shin ya akayi Suwaiba ta gane cewar amaryar da za’a auro tana saka hotunan Mutallab a Instagram alhalin a sannan bat a san sunan tab a kuma bata ga ma hoton tab a balantana ayi zaton ko a sannan ta san ta? Ya dace a samar da dalili kafin faruwar hakan.
Karkarewa:
Fim din ya fadakar domin an nuna illar daukar zugar kawaye tare da kuma illa ga budurwa mai sakin jiki da maza a waje wanda hakan yakan ja mata mugun zargi.
Haka kuma an nuna darasi ga wasu matan ta hanyar nuna musu ba laifi bane don mijin su zai kara aure. Wallahu a’alamu!
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Suna: Rudani Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo da Jamilu Ahmad Yakasai Kamfani: Almubarak International Films Production Limited Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda Umarni: Ahmad A. Bifa Jarumai: Ali Nuhu, Jamilu Ahmad Yakasai, Ibrahim Mandawari, Aisha Aliyu Tsamiya, Rukayya Umar, Hajara Usman, Hadiza Muhammad da dai sauransu
Sharhi: Hamza Gambo A farkon fim din an nuna Baba (Ibrahim Mandawari) ya shigo gidan sa iyalan sa sun tarbe shi suna yi masa murnar karin shekarar haihuwar sa. An nuna cewar yana zaune da matar sa (Hajara Usman) tare da ‘ya’yan sa Yaya Bashir (Ali Nuhu) da kanin sa Sadik (Jamilu Yakasai) wadanda suma suke tare da matayen su a cikin gidan. Duk da kasancewar shi Sadik suna samun rashin jituwa da matar sa Habiba (Aisha Aliyu Tsamiya) wadda tsananin kishin sa da take yi yasa har ta fara zargin sa akan yana bin matan banza, hakan yasa lokacin da zai tafi London taki amincewa da tafiyar sa saboda tana zargin cewa ba aiki zai tafi ba zai je ne kawai don ganawa da budurwar sa baturiya. Sun samu rashin jituwa a sanda mijin nata Sadik zai bar kasar duk da kasancewar yayi mata bayanin aikin da zai kaishi London din amma ta kasa fahimta. Bayan tafiyar Sadik London sai Habiba ta soma rashin lafiya, amma bayan zuwan ta asibiti sai aka tabbatar mata da cewar tana dauke da larurar cuta mai karya garkuwar jiki wato kanjamau. Jin hakan ne ya tashi hankalin Habiba ta kara tabbatar da zargin da take yiwa mijinta na cewar yana neman matan banza. Bayan ta dawo gida ta sanar da iyayen sa sai aka kira sa aka bukaci yaje asibiti acan London din don a auna jininsa don a gane ko yana dauke da cutar shima, amma sai Sadik yaki amincewa da hakan har a karshe mahaifin sa ya bukaci yabar aikin da yake ya dawo gida domin a sannan rigima ce ta afku iyayen Habiba suna neman mika maganar zuwa kotu don a bi wa ‘yar su hakkin ta. Hakan ne yasa Sadik ya dawo gida najeriya aka je wajen likita ya duba jinin sa, sai dai bisa mamaki da aka duba sai aka gane cewar babu cutar kanjamau din a jikin sa. Hakan ne ya sake haifar da hargitsi domin iyayen Habiba sun ki yarda da binciken da akayi saboda suna zargin cewa a jikin sa ne Habiba ta dauki cutar kanjamau. A karshe dai dangin Habiba suka kai Sadik asibitin da suke ganin za’a fada musu gaskiya, sai dai kuma acan din ma sakamakon iri daya ne bayanai sun tabbatar da cewar Sadik bashi da cutar kanjamau, hakan ne yasa zargin kowa ya koma kan Habiba, domin ta jima da guduwa gidan iyayen ta, acan din ne mahaifiyar ta (Hadiza Muhammad) ta rutsa ta da tambayar inda ta kwaso cutar kanjamau, sai dai kuma Habiba ta gaza bata amsa. Ana tsaka da haka ne Sadik yaje gidan su Habiba ya fada mata gaskiyar cewa baya mu’amula da matan banza kuma budurwar sa ta kasar waje sun jima da rabuwa domin saurayin ta yayi masa gargadin kada ya sake ganin su tare. Bayan Sadik ya gama bawa Habiba labari ne sai ya bukaci da tayi dai tunani don a gane inda ta samu larurar kanjamau, ya bata misalin cewar ba sai ta hanyar jima’i ake daukar cutar ba, akan iya samun ta ta hanyar yankan farce ko kitso ko wani dalili daban na haduwar jini. Jin hakan ne yasa Habiba ta bashi labarin cewa wata rana kawarta tazo gidan ta tun tana amarya ta bata shawara akan yin tsarin iyali don kada ta haihu da wuri, sai dai kuma bayan zuwan su asibitin sai likita ya tabbatar musu da cewar sirinji daya ne ya rage wanda za’a yi musu allura, sai dai ya fita ya siyo wani, amma sai duk su Habiba suka nuna sauri suke yayin da kawar ta ta bukaci cewar tunda su kawaye ne a yi musu da guda dayar kuma a fara yi mata sannan a yiwa Habiba, hakan kuwa akayi nan aka fara yi mata allurar sannan aka yiwa Habiba. Bayan Habiba ta gama ba shi labari sai Sadik yaje neman kawar Habiba a gidan ta amma sai ya samu labarin cewa ita da mijin ta sun rasu kuma ana zargin cutar kanjamau ce ta kashe su. Wannan dalilin ne yasa aka gane inda Habiba ta samu larurar cutar kanjamau, kuma Sadik yayi alkawarin zai kai ta London don nema mata magani kuma idan ta warke yayi alkawarin zai mayar da ita dakin sa. Abubuwan Birgewa: 1- Labarin ya fadakar kuma ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba, sannan kuma an yi kokarin saka abubuwan da suka rike mai kallo har zuwa karshen labarin. 2- An yi kokari sosai wajen samar da muhallin da su ka dace da labarin wato (locations) 3- Daraktan ya yi kokari sosai wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace, haka yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari musamman Habiba wato Aisha Tsamiya. 4- Sauti ya fita radau, haka ma hoton fim din ya fita radau domin an yi kokari wajen nuna salon daukar hoton fim din. Kurakurai: 1- An nuna cewar tun Habiba ta na amarya kawarta ta raka ta wajen yin allurar tsarin iyali (wato family planning) wanda dalilin hakan ne ya sa a ka samu matsalar da Habiba ta kamu da larurar cutar kanjamau, sai dai kuma duk da a na daukar cutar ta hanyar jima’ai kuma an nuna cewar Sadik ya na tare da matar tasa har na tsahon lokaci, amma shi bai kamu da wannan larurar ba, ya dace a nuna wa mai kallo dalilin da ya sa Sadik bai kamu da cutar ta kanjamau ba. 2- Lokacin da Sadik ya bawa Habiba labarin budurwarsa wadda su ka yi soyayya a kasar waje, me kallo ya ga Sadik ya dauki budurwar tasa a can kasar London ya kai ta gidan wata dattijuwa wadda ya kira da Mom. Shin wace ce wannan dattijuwar wadda Sadik ya kai budurwarsa gidan ta a London? Tun da an nuna mahaifiyarsa a Najeriya (wato Hajara Usman). To, ya dace a yiwa me kallo bayanin matsayin dattijuwar nan a wajen sa ko da ta hanyar nuna cewar ‘yar uwar mahaifin sa ko mahaifiyar sa ce 3- Shin ina mahaifin Habiba? Har fim din ya kare mai kallo bai gan shi ba kuma ko a baki ba a ambace shi ba, duk da kasancewar akwai matsaloli da yawa na fannin auren Habiba da suka taso wanda ya kamata ace an ga mahaifin ta a cikin maganar, amma ba a gan shi ba sai wani Barrister da aka nuna a matsayin kawun su. Idan ma mutuwa mahaifin ta yayi to ya dace ko a baki ne a fada. Karkarewa: Fim din ya fadakar kuma labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa. An nuna illar bin shawarar kawaye, sannan kuma an yi kokari wajen isar da wani muhimmin sako wanda al’umma zasu amfana da shi, domin fim din ya koyar da wani darasi wanda jama’a zasu kiyaye rayuwar su da lafiyarsu. Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradin Mu Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya Mun kudiri aniyar tsage gaskiya na bada labarai da suka hada da harkokin yau da kullum Da zummar samar da zaman lafiya da kuma daukaka kima da martabar al’adun Hausa. DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode
Allah Ya kara kawo masana'antar Kannywood zuwa karshen wannan shekara.
Ba ma wannan kadai ba, masana'antar ta samu ci gaba da har ta yi fina-finai iri-iri, wadanda yawanci na barkwanci da soyayya ne, da kuma almara, wadanda kalilan ne.
Daga ciki akwai fim din ban-dariya na Adam A. Zango, wato Dan Kuka a Birni da fim din Ali Nuhu da ya yi shi shekara 18 baya kuma ya sake yinsa yanzu, Mujadala, da dai sauransu.
Kabiru Jammaje, wanda shi ne musabbabin farfadowar sashen Ingilishi a Kannywood, ya sake daukar nauyin wani kasaitaccen fim din sarauta mai suna In Search of the King.
Da alamun fim din Nafisa Abdullahi, Yaki a Soyayya, ma za a ji dadinsa, saboda haka shekarar ta 2018 ta kayatar.
Wadannan fina-finan da aka jero a kasa su ne suka fi shahara da fice a wannan shekarar, wacce ta zo dab da babban zaben Najeriya wanda za a yi farkon shekara mai zuwa.
Ga shi siyasa ta kunno kai cikin masana'antar ta Kannywood, har ma ake ganin ta janyo rarrabuwar kawuna gami da barazanar kara raba kan mambobin masana'antar da ba a jima da sasanta su ba - kodayake, wannan ba shi ne maudu'inmu yanzu ba.
Fina-finan ba bisa daraja aka jera su ba:
1. Ruwan Dare
Hakkin mallakar hotoYASIN AUWALImage captionRuwan Dare ne ya yi fice a cikin fina-finan Kannywood na 2018
Fim din, wanda daraktansa shi ne Yaseen Auwal kuma ake ganin yana daya daga cikin fina-finan Kannywood da suka fi dacewa da yanayin da ake yanzu, yana shagube ne cikin salon tsoratarwa ga matasan da suka gama jami'a kuma suke raina duk wani aikin da ba na ofishi ba.
Aminu Sharif, wato Momoh, da Sadiq Sani Sadiq wasu mutane ne da suke son yin kudi ko ta wane hali kuma masu tsananin buri ne, wadanda sun gama digirinsu na farko a fannin Akanta da Tattalin Arziki.
Abokinsu kuwa, wanda shi ma ya gama jami'ar, Baballe Hayatu, ba irin salonsu ya dauko ba.
Saboda haka, daga karshe sai ya samu nasara.
Su kuma wadancan biyu daga karshe sun koyi darasi sannan suka yi nadama.
Fim din ya yi matukar haduwa saboda yadda jigonsa yake da alaka da wannan zamanin.
Kuma 'yan wasan, wadanda aka ambaci sunayensu a sama da ma wadanda ba a ambata ba, sun yi kokari sosai.
Za a iya kau da kai daga 'yan kura-kuran cikin fim din - irin su ambatar Yugoslavia a matsayin kasa, kura-kuran nahawun Turancin Ingilishi, da sauransu.
2. Rabi'atu
Hakkin mallakar hotoGOOGLEImage captionMaryam Yahaya a fim din Rabia'atu
Rabi'atu, wanda Aminu S. Bono ya yi darakta, an shirya shi ne kwata-kwata a gidaje guda uku; kuma yana nuna irin hadarin da 'yar aikin gida ke shiga a gidan da take aiki.
Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin ita ce Rabi'atu, takan yi duk aikace-aikacen babban gidan Alhaji Rabiu Rikadawa, yayin da matarsa, Hadiza Muhammad, kuwa ke zuwa wajen aiki; 'ya'yansa hudu kuma makaranta suke zuwa.
Rabi'atu dai yarinya ce mai yarinta kuma kamammiya, wacce gidansu ba masu karfi ba ne.
Saboda haka kowa a cikin gidan da take aiki sonta yake yi, har ma manyan 'ya'yan gidan guda biyu suke takara da juna wajen samun karbuwar soyayya a wajenta.
Sai dai ba ta amince da su ba, tana mai jaddada musu cewa sun wuce ajinta.
Sai dai duk da haka ba wanda ya hakura a cikinsu.
Ana haka, kwatsam sai wata rana Alhaji ya zo gidan ya same ta ita kadai har ya yi lalata da ita.
Daga bisani, sai matar Alhaji ta gano Rabi'atu fa ta samu juna-biyu sakamakon lalata da Alhaji ya yi da ita.
Aka yi ta gumurzu dai har zuwa karshe.
Fim din bai ci kudi ba, amma ya yi matukar dacewa da yanayin da ake ciki yanzu.
Sannan, labarin ya yi kama da zahiri kuma daraktan da mataimakansa da kuma 'yan wasan, wadanda ba shahararru ba ne, sun yi aiki da basira sosai.
Babu rawa da waka a ciki.
Ba ma wannan ba, karshen fim din ya kayatar.
3. Fuska Biyu
Hakkin mallakar hotoADAM ZANGOImage captionFim din Fuska Biyu
Fuska Biyu yana nusarwa ne game da yadda wasu iyaye ke saurin aurar da 'ya'yayensu mata ba tare da bincike kan mazajen da za su aurar wa ba.
Fim din yana ba da labari ne na wani madugun masu garkuwa da mutane, Adam A. Zango, wanda da rana yake bayyana a matsayin mai sayar da kifi.
Amal, wata kamilalliyar yarinya, wacce 'yan uwanta ba masu karfi ba ne, takan sayar da abinci a gefen teburin da Zango ke ikirarin yana sayar da kifi.
A haka sai suka fara soyayya.
Irin abin duniya da yake ba ta ya sa mahaifiyarta take jin akwai lauje cikin nadi.
Amma mahaifinta kuma ya dage cewa 'yarsa fa ta samu mijin aure.
Sai kuma da lokaci ya kure sannan mahaifin ya fahimci kuskurensa.
Fim din akwai jan hankali cikinsa.
Yana da amfani sosai a kalle shi.
4.Risala
Hakkin mallakar hotoABUBAKAR S SHEHUImage captionFim din Risala
Sunan wannan fim, Risala, wata kalma ce ta Larabci, wacce ke nufin "sako".
Risala, wanda Abubakar S. Shehu ya yi darakta, siffofin zamanin baya yake da su.
Gogaggen tauraron nan, Sadiq S. Sadiq (Zakariyya), ya yi wata tafiya da nufin neman mutumin da ya yi wa ba-daidai ba don neman afuwa.
Tafiya ce mai cike da karaskiya, masifu da abubuwan al'ajabi.
Abin bai tsaya a haka ba - sai da ya sake haduwa da wata jarrabawa a wani gari da ake kira Baihan, garin da mutumin yake.
Wannan mutumin ya yarda zai masa afuwa amma sai in ya amince zai auri 'yarsa, wacce, a cewarsa, ta fi kowa muni a garin kuma musaka ce.
Sai Zakariyya ya amince amma ba cikin son ransa ba.
Ashe dai yarinyar nan ba haka take ba; hasali ma, yarinyar matukar kyau ne da ita.
Bayan 'yan kura-kurai da fim din ke da su kamar rashin takaita darussa da yake koyarwa, da kuma ci-da-karfi wajen aiwatar da wasu abubuwa, fim din ya dauko tarihin haihuwar shahararren malamin addinin Islaman nan ne, Abu Hanifa.
Kodayake yawancin fina-finan Kannywood kwaikwayo su ake yi daga wani waje.
Baya ga haka, sautin shirin ya dauku.
5. Hakki
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAMISU IYANTAMAImage captionFim din Hakki
Kamar yadda ake fada, tsohuwar zuma da ita ake magani.
Sanannen kamfanin shirya fina-finai, Iyantama, shi ya yi fim din Hakki yayin da Hafizu Bello, kwararre a harkar, ya yi darakta.
Labari ne kan wani mai suna Jabir, wanda jajirtaccen ma'aikaci ne kuma dan gwagwarmaya a wani kamfanin fata.
Ba a san shi da karba ko ba da cin hanci ba.
Ba tare da nuna fargaba ba, yake yaki da rashin adalci da kuma rashin kyautawar da hukumar kamfanin ke yi wa ma'aikata.
A bangare guda kuma, akwai labarin wani gungun 'yan mata da suke janyo mazaje cikin wani loko domin abokansu na aikata miyagun laifuka su samu damar fasowa don yi musu fashi.
Har yanzu fim din a sinima kawai ake samunsa.
Ya kuma samu damar shiga sahun fina-finai don samun lambar yabo.
Ya samu karbuwa ne saboda irin sakon da yake isarwa, wanda gaba daya ya sha bamban da irin fina-finan Kannywood na soyayya.
Kuma ya dace da zamanin da ake ciki musamman yayin da kungiyar kwadago ke ta fama da gwamnati wajen ganin an samu karin albashi.
6. Mariya
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI NUHUImage captionFim din Mariya
Fim din Mariya, wanda Ali Nuhu ne daraktansa, yana nuni ne kan yadda lamarin auren 'ya mace yake a kasar Hausa.
Labari ne na Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin Mariya kuma ake tuhumarta da kashe mijinta, Baba Karkuzu, da abokinsa, Musa Maisana'a, ta hanyar saka musu guba.
Kafin a yi mata auren dole, tare da Abdullahi (Umar M. Sharif) take soyayya.
Ga shi tana da buri na karantar aikin likita.
Daga bisani sai aka gano ashe ba ita ta yi kisan ba.
Babban kuskure a cikin fim din shi ne rashin fito da takamammun al'amura fili.
Duk da haka, fim din ya dace da zamanin da ake ciki yanzu.
'Yan wasa ma sun yi kokari.
Maryam Yahaya, kamar yadda ta saba, ta yi abin a-zo-a-gani.
Wadanda suka fito hatsabibai ma kamar su Garzali Miko, Baba Kurzuku, da Alhassan Kwalle sun taka rawar gani.
Tacewa da haskakawa da kuma kwalliya a fim din suna da jan hankali.
7. Larai Ko Jummai
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/SADIQ MAFIAImage captionMaryam Yahaya da Amal Umar a fim din Larai ko Jummai
Rikici tsakanin kishiyoyi ba bakon maudu'i ba ne a Kannywood yayin da nuna fada kan 'ya'yayen kishiyoyin kuwa abu ne bako.
Jummai (Amal Umar) da Larai (Maryam Yahaya) 'yan uba ne.
Yayin da mahaifiyar Jummai (Ladidi Fagge) masifaffiya ce, ta Larai kuwa ba haka take ba: shiru-shiru ce.
Mijinsu (wato Bashir Nayaya) yana ta hakuri da su dai.
Kamar yadda ya saba faruwa a kauyuka, kawai sai 'ya'yan baffanunsu (Abdul M. Sharif da Garzali Miko) suka tsunduma cikin soyayya da wadannan 'ya'yan Bashir Nayayan.
Da yake Garzali attajiri ne saboda a birni yake aiki, Ladidi sai da ta yi kutun-kutun ya auri 'yarta.
Kwatsam sai abubuwa suka sauya: Abdul ya zo ya fi Garzali kudi bayan ya bi shi sun tafi birni tare.
Sadiq N. Mafia ne daraktan fim din kuma shi wannan fim ya kece sauran fina-finai saboda dalilai da dama, duk da bai watsu kamar sauran fina-finai ba saboda ba a kashe masa kudi sosai ba.
Fim ne da ke matukar nuna zahiri, wanda za mu iya cewa shi ne zakara wajen nuna ainihin rayuwar Hausawa a kauye da kuma rashin jituwa kan "abin da bai taka kara ya karya ba" da ke tsakanin kishiyoyi a gidan mijinsu.
8. Taqaddama
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI GUMZAKImage captionFim din Takaddama
Fim ne da Ali Gumzak ne daraktansa kuma labari ne na "abin da ya taba faruwa da gaske" na wani sangartaccen dan wani shahararren mai kudi, Hassanu (Aminu Sharif).
Duk lokacin da ya yi laifi aka kulle shi, attajirin mahaifinsa, Alhaji Bilya (Ali Nuhu), wanda yake kut-da-kut da 'yan siyasa, kan ba da kudi domin a sake shi.
Ga shi mahaifin ba ya karbar shawara ko uzurin kowa.
Sai dai Hassanu da mahaifin nasa karshensu bai yi kyau ba bayan ya kashe abokinsa, Salisu, a lokacin da suka yi rigima a wani gidan rawa.
Hassanu ya ja kunne wa dayan abokinsu, Nura (Abba Almustapha), wanda aka yi kisan a gabansa, cewa kar ya fada wa kowa shi ma zai kashe shi.
Sai dai Nura bai iya barin wannan barazana a zuciyarsa ba, wanda hakan shi ya tona asirin wanda ya yi kisar, wato Hassanu.
Fim din ya yi kokari wajen nuno yanayin rayuwar manyan Najeriya.
'Yan wasan sun yi kokari.
Shirin Ya koyar da darasi sosai, duk da cewa "kayatarwa" da "koyar da darasi" a lokaci guda abu ne da Kannywood ke fama da shi.
9. Kawayen Amarya
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/YAKUBU MOHAMMEDImage captionFim din Kawayen Amarya
Fim ne da 2 Effect Empire wanda kuma Yakubu Muhammad ya ba da umarni.
Kuma fim ne da 2 Effect din suka saba yin irinsa, wato mai kyale-kyale da kuma tattaro manyan taurari.
Labari ne na wani mai kudi, Alhaji Abdulsalam, da ke da mata uku.
Bai taba haihuwa ba.
Saboda fargabar haka sai ya dauko wani yaro ya mayar da shi a matsayin dansa.
Daga baya ma sai matan nasa suka samu juna biyu suka haihu.
Uwar gidansa (Saratu Gidado, wato Daso) kullum alfaharinta shi ne "ai mahaifinta ne sanadin kudin Alhaji", saboda haka, ya kamata komai nata da na danta ya zama daban.
'Ya'yan Alhaji (wato Ali Nuhu da Sani Danja da kuma Yakubu Muhammad) a rana guda suka yi aure.
Kamar yadda sunan fim din yake, haka fim din ma yake tattare da cakwakiya da kaceniya a yayi da bayan bikin auren, wanda yawancin kwayayen amaren ke janyowa.
Duk da fim din na ban-dariya ne, amma yana dauke da darrusa.
Babban matsalarsa ita ce "sautin ADR", wanda shi ne sake nadar murya don a saka wa fim kafin watsa shi.
Maganganun ba sa tafiya daidai da motsin lebe a fim din.
Haka dai babu abin da aka yi wa Daso bayan ta kashe mutane har biyu.
Fim ne da zai kayatar sosai.
10. Li'ani
Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI GUMZAKImage captionFim din Li'ani
Ali Gumzak ne daraktan wannan fim din.
Labari ne na wani mai suna Alhaji Sunusi (Rabiu Rikadawa), wanda sam ya ki yarda juna-biyun da matarsa ke da shi nasa ne.
Hakan ya kai ga sun je gaban alkali sun yi rantsuwa (Li'an).
Dan da ta haifa, wanda shi ne Ali Nuhu, a wajenta da mijin da ta aura ya girma.
Sai dai daga baya alhaki ya bi Alhaji Sunusi, wanda yake ganin kamar sakayya ce daga Ubangiji sakamakon abin da ya yi wa wannan matar tasa.
Mata takwas ya aura, yayin da daya daga cikinsu ta taba yunkurin kashe shi, amma hakan bai yiwu ba.
Sai da lokaci ya kure kafin ya gane kuskurensa.
Fim din ya hadu saboda irin maudu'in da ke ciki, wanda ba a saba yin fim a kansa ba.
Masu shirya fim din da 'yan wasan duk sun yi kokari sosai wajen saurin fito da al'amura fili.
Babu waka ko rawa a ciki.
Akwai wasu 'yan al'amura na daban wadanda su ma sun taimaka wajen isar da ainihin sakon fim din.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradin Mu Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya Mun kudiri aniyar tsage gaskiya na bada labarai da suka hada da harkokin yau da kullum Da zummar samar da zaman lafiya da kuma daukaka kima da martabar al’adun Hausa. DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode Source: BBC HAUSA