Saturday 10 December 2022

Kurakurai 5 A Cikin Fim Din A Bikin Suna Tare Da Sharhin Fim Din

Tura Wannan Zuwa Ga

Sharhin fim ɗin ‘A BIKIN SUNA’


Kamfani: SRK Movies

Shiryawa: Danjuma Salisu

Bada umarni: Kamal S. Alkali

Ranar fita: 28-10-2022

Jarumai: Ali Nuhu, Saratu Daso, Mommy Gombe, Musa Mai Sana'a, Shamsu Dan Iya, Maryam Yahaya, Rahama MK, etc.

Mai Sharhi: Habibu Maaruf Abdu


Sharhin Shirin A Bikin Suna Tare Da Kurakurai 5 Na Cikin Shirin
Hoto: MC MALAM IBRAHIM SHARUKHAN


Marubuci: Habibu Maaruf Abdu


GABATARWA:


Fim na farko da Kamfanin SRK Movies ya fara saki a sinima shi ne ‘Jaruma (2020)’ kuma ya samu matsakaiciyar nasara yayin haskashi. Wataƙila hakan ne ya bawa Kamfanin ƙwarin gwiwar ci gaba da sakin duk finafinansa a sinima. Sun saki ‘Makota’ a 2021, sai ‘Daga Dinner’ a farkon wannan shekarar (January, 2022). A jiya Juma’a kuma suka saki sabon shirinsu mai taken ‘A Bikin Suna.’


LABARI:


A Bikin Suna’ labari ne na Mustapha (Ali Nuhu) da matarsa Ummulkhairi (Mommy Gombe). Shekarunsu biyar da aure amma Allah bai nufe su da samun haihuwa ba. Wannan ne ya sa 'yan uwan Mustapha, su Musa Mai Sana’a, da mahaifiyarsu Hajiya Mama (Saratu Daso) suka kafawa Ummulkhairi ƙahon zuƙa. Kullum sai su yi ta mata gori cewa ita juya ce ba ta haihuwa. Abin ya ƙara ta’azzara bayan da Mustapha ya ƙi bin umarnin mahaifiyar tasa na ƙarin aure.


A ɓangare guda kuma, akwai Shamsu (Dan Iya) wanda shi ma ƙanin Mustapha ne, amma ba ya goyon bayan gallazawar da 'yan uwansa suke wa matar yayan nasa, hasalima soyayya yake da ƙanwarta, Ameera. Hakan yasa sauran 'yan uwan nasa shi ma suka juya masa baya. Ana cikin haka, cikin ikon Allah sai Ummulkhairi ta samu ciki, al’amarin da ya chanja komai da komai. Hajiya Umma ta fara nuna ƙauna da kulawa ga sirikar tata. Bayan haihuwar aka haɗa gagarumin bikin suna. A nan ne kuma sabon rikici ya ɓarke yayin da aka sace jaririyar ana tsaka da cashewa A Bikin Suna. Me ya faru daga nan? Ku je Film House Cinema da ke Shoprite Kano don ganin yadda ta kaya.


TA’ALIƘI:


‘A Bikin Suna’ fim ne a kan matsalolin auratayya, zamantakewa da zumunta. A fagen auratayya, mun ga yadda matsalar rashin haihuwa ta haifar da tangarɗa a rayuwar auren Mustapha da Ummulkhairi. Mun kuma ga yadda zamantakewa ta kasance tsakanin ma’auratan da 'yan uwansu. A ɓangaren zumunta kuma, mun ga yadda alaƙa ta lalace tsakanin Mustapha da ƙaninsa Habu (Musa Mai Sana'a), da yadda mahaifiyar Mustaphan ta yi fushi da shi har ma ta hana shi zuwa gidanta, sannan ta daina karɓar komai daga hannunsa.


Fim ɗin ya kuma nuna batun soyayya. Mun ga yadda soyayya ta ƙullu tsakanin Shamsu da Ameera, da kuma halin damuwa da Shamsun ya shiga yayin da masoyiyar tasa ta juya masa baya sakamakon cin mutuncin da 'yan uwansa sukai mata. Sannan akwai barkwanci sosai a fim ɗin, musamman wajen rawar da Musa Mai Sana'a ya taka.


Shirin ya ƙunshi darussa kamar su haƙuri, muhimmancin addu’ah da ilimi. Mun ga yadda Mustapha da Ummulkhairi suka yi haƙuri a bisa matsalar rashin haihuwa, suka yi ta addu’ah, Allah maji roƙo kuma ya biya musu buƙatarsu daga ƙarshe. Sannan mun ga yadda Habu ya kunyata a gurare biyu kasancewar ba shi da ilimin boko. Na farko, sanda shamsu yai masa gori, na biyu kuma sanda ya kasa karantawa Hajiya takardar asibiti. Bugu da ƙari, fim ɗin zai iya zama wata hanya da mutane za su koyi sabon salon gabatar da ‘Bikin Suna’, wato dai ya zama ana gudanar da shi a ƙawataccen waje mai kujeru, kamar yadda aka nuna a fim ɗin, saɓanin yadda aka saba yinsa a al’ada.


ABUBUWAN BURGEWA:


1. Labarin fim ɗin ya tafi kai tsaye zuwa manufar da ake son a cimma, kuma an tafiyar da shi bisa tsari ba tare da ya karye ba.


2. An sanya nishaɗi sosai a fim ɗin ta yadda ba zai gunduri mai kallo ba, duk da cewa labarin a karan kansa ba mai riƙe tunani da sanya zaƙuwa ba ne.


3. Ya ƙayatar sosai yadda fim ɗin ya kafa misalai da wasu abubuwa na zahiri da suke faruwa a tsakanin al’umma a daidai wannan lokacin, irin su ƙwacen waya, satar mutane, harkar Tiktok, yajin aikin malaman jami’a (ASUU Strike), da kuma irin fifikon da Jami’ar Bayero (BUK) take da shi a kan sauran jami’oin Arewacin Najeriya (kwanannan Times Higher Education World University Ranking ya tabbatar da haka).


4. Duka jaruman sun yi ƙoƙari wajen taka rawar da aka ba su. A wannan karon Musa Mai Sana’a bai yi over acting sosai ba. Shamsu Dan Iya da Sumayya Galadi sun haska. Haka ma Ali Nuhu, Saratu Daso da Mommy Gombe.


KURAKURAI:


1. Labarin bai tsaru da kyau ta yadda zai riƙe hankalin mai kallo ya sa shi tunanin abin da zai faru a gaba ba.


2. Wasu ƙwararrun jarumai a fim ɗin, kamar Maryam Yahaya da Teema Makamashi, ba’a ba su damar taka rawa sosai ba.


3. Kayan Ankon da maza suka saka a wajen bikin sunan, wanda yai kama da shigar inyamurai, kwata kwata bai dace ba.


4. Waƙar da Maryam Yahaya ta yi da saurayinta, wanda sau ɗaya kawai aka nuno su tare, ita ma ba ta dace ba. Kamata ya yi a ce Shamsu Dan Iya da Ameera ne suka yi waƙar saboda anfi nuna soyayyarsu.


5. A farko an nuna ƙannen ali Nuhu guda shida (6) ne, amma kuma sai aka ci gaba da nuna guda huɗu (4) kacal har zuwa ƙarshe.


ƘARƘAREWA:


Duk da cewa ‘A Bikin Suna’ shi ma an yi shi ne da irin salon sauran finafinan Kamfanin ‘SRK Movies,’ ya fi sauran tsaruwa. Na jinjinawa daraktan sa, Kamal S. Alkali, da ex-producer, Mal. Ibrahim Sharukh Khan.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user