Friday 9 December 2022

Shin Ko Kun San Muhimmancin Bayar da Kyautar Fure A Soyayya?

Tura Wannan Zuwa Ga

Barkanmu da Juma'a. Da fatan masoya suna tsinkar fure cikin ƙoshin lafiya. Shin ko ka san cewa 'fure' tambari ne daga cikin tamburan masoya?


Muhimmancin Furen Soyayya
Hoto: About Islam


MarubuciNura Nakowa


A zamanin da, ana bada kyautar fure ga masoyi domin nuna masa matsayin darajar sa a gurin masoyin sa.


A kan samu mazubi ko maɗauri domin alkinta furen da za a kai wa masoyi.


A kan tura ɗan aike ya kai ko kuma mutum ya kai da kansa. Ya danganta da manufar abin da masoyi yake so ya bayyana wa masoyinsa.


A yadda tsarin yake tun a baya, mata su aka fi ba wa furanni don a burgesu.


Abin ya samo asali ne daga nahiyar turai har ya yaɗu zuwa sauran nahiyoyi daban-daban wanda a yanzu kusan kowacce nahiya da dauloli wannan al'adar ta shiga. Kusan dukkanin fitattun ƙabilu na duniya suna kwatanta wannan al'adar ta miƙa furanni ga masoya.


Fure ganye ne da ke tsirowa da launi iri-iri masu ban sha'awa, kamar launin fari da ja da kore da rawaya ko ruwan ƙwai da launin shuɗi, wani sa'ilin ma da launin makuba da shanshanbale. Ba ya ga kyawawan launuka da furanni ke ɗauke da su, hakanan kuma wasu daga cikin su suna da ƙamshi me daɗin gaske wanda ke jan hankalin masoya. Sai dai kuma furannin da masoya suka fi amfani da su su ne ja da ja me haske (pink) da kore da ruwan ƙwai.


Dalilan bada furen soyayya suna da yawa;


1. Ana bayarwa domin neman soyayyar mace, wato, a ja hankalin ta don ta fahimci cewar ana son ta.


2. Ana bayarwa domin jaddada so da ƙauna a tsakanin masoya.


3. Ana bayarwa domin tambaya ko neman izinin aure.


Haka kuma ana bayarwa idan masoyi zai yi wani shagali ko biki domin taya shi murna. 


Kamar cin jarrabawa na kammala karatu da murnar zagayowar ranar haihuwa ko yayin da masoyi ya yi kyau a wani guri ko a gasar wasanni da makamantan su.


A wannan yanki namu na ƙasar Hausa abin baida tasiri sosai sai ɗan kaɗan da waɗansu waɗanda ake wa kallon wayayyu ko 'Yan Boko suke yi.


Kowacce ƙabila da irin abin da suke kallo a matsayin tambarin da masoya ke amfani da shi a matsayin alamar soyayyar su.


To tambayar da zan muku ita ce, tun da wannan lamari ya bunƙasa a duniya har zuwa wannan yanki namu.....,


Menene tambarin masoya a ƙasar Hausa?


Shin ka taɓa saya ko tsinkar fure ka kai wa masoyiyar ka ko matar ka?


Shin mijinki ko masoyin ki ya taɓa ba ki kyautar fure?


Sai na ji daga gare ku.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun Litinin, Laraba, da Juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user