Monday 12 December 2022

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (48) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

5. Abokai: Lura da kyau, akwai abokan asali waɗanda aka taso tare tun yaranta, waɗannan su ne abokan rayuwa, duk wani abu da ya ratso maka wanda ya shafi rayuwar yau da kullum ko ya shafi iyali ko zumunta ko taimaka wa wasu su za ka sama a matakin farko, za su ba ka wasu 'yan shawarwari na yadda za ka tafiyar da rayuwarka cikin matattararka ba tare da ka yi baƙin jini ba, kar ka yarda ka yi nesa da su, ko sun ƙaurace maka a dalilin matsayin da ka samu janyo su kusa, ci abinci tare da su a gidajensu komai rashin daɗinsa, kawo naka, kuma idan Allah ya hore maka ka rinƙa ganinsu, duk wata gulma da za a kawo maka ta cewa wani a cikinsu ya zage ka ko ya yi maka sharri matuƙar ba a gabanka ya faɗa ba kar ka damu, yi masa abin da kake yi wa kowa za ka ribaci zuciyarsa.


Mahassada
Hoto: Business Alligators


MarubuciBaban Manar Alkasim


Amma abokan sana'a da kasuwanci daban ne, yi ƙoƙari kowa ya san lokacinsa da inda ya kamata ya ba da gudummuwarsa ga rayuwarka. Abokan asali ba su san gumurzun da ake yi a wurin sana'arka ba, ya kamata su tsaya ne a ɓangaren zamantakewarka, kai kuma sai ka keɓe lokacin zama da su kan wannan, su ma abokan sana'arka komai kuɗinsu kar ka yarda su raina abokanka na asali, kuma kar su shiga rayuwarka ta yau da kullum don ba huruminsu ba ne, idan kowa ya tsaya a mahallinsa abubuwa za su ƙara haske, da wahala ka ji 'yan uwa ko abokai na zaginka.


Na ji wani ana ta zaginsa wai tunda ya sami wata madafar mulki ta siyasa ya haye bai sake kula kowa ba a cikin abokan tafiyarsa, bai kiransu, kuma bai da lokacin shiga cikinsu, a kullum yana sauraron su biyo shi ne shi kuma ya ɗan gutsura musu wani abin, su kuwa cewa suke bari ya gama lokacinsa mu gani, ba mu muka tura shi ba? Wasu kuma roƙon Allah suke ya fito neman wani matakin don su rusa shi, sai na ga ba zarginsa suke yi kan rashin aiki ba, kuskuren da ya yi shi ne bai ajiye abubuwa a mahallansu ba, ya yi watsi da abokan asali ya karɓi wasu jama'ar da rayuwa ta kawo masa daga baya, sai ya manta cewa waɗancan dai zai dawo musu a ƙarshe, bisa ga dukkan alamu yana dab da sakin hanyar nasara.


Shi wannan matsayi na farko da mutum zai samu hanya ce da idan ya bi ta za ta haɗa shi da wata hanyar, a haka har ya isa ga nasara, idan ya yi zaton wannan hanyar da ya hau shikenan ɗoɗar har nasara to fa ya yaudari kansa, yanzu dai ba a makara ba, ina abokanka na asali? Kama su, janyo su jiki, ko ba za ka ba su komai ba nuna musu cewa su ma fa wani abu ne a rayuwarka, bare ma sun cancanci komai tunda tare aka taso, ɗan lura da wasu matsalolinsu waɗanda ba za su gagare ka ba ka warware musu, su ma suna da rawar da suke takawa a rayuwarka, ka ba su damar da za su ji cewa tare kuke, idan ka ɗan sami lokaci ka ziyarce su a inda suke, idan kana da wani abu ka yi musu, duk lokacin da suka buƙace ka su same ka, ka sani ko mutuwa ka yi su ne na farkon tara maka jama'a da yi maka addu'a, sukuninnan da kake ji har da iya riƙe abokan farko.


6. Wanene naka?: Ana yi wa mata dariya ne amma suna da wayonsu, ka lura, wanda yake da ƙoƙari a makaranta ba ya rasa budurwa, wani sa'in ma har hidindumu take yi masa a maimakon shi ne zai riƙa ba ta don shi ne namiji, sirrin anan shi ne: Ta san ita kaɗai ba za ta yi karatun da zai sa ta ci jarabawa ba, sai ta sami wani mai ɗan hankali ta naniƙe masa su riƙa yin karatu tare, idan ma aiki aka ba ta shi zai nemo mata kayan aikin, ko ma ya yi aikin ya kawo mata, mai girman kai ba ƙoƙari sai ka taras da ƙyar take sha, kare mutunci a wurin mace dole ne, anan sai ta san wanda za ta yi mu'amala da shi kar ta ɗauko wanda zai kai ta ya baro, to kai da kake son ka zama mai sukuni da wa kake mu'amala? Wanda ya fi ka idan ka raɓuke shi za ka daɗa samun wayewa ta fuskoki daban-daban da za ka bunƙasa kasuwancinka ko wanda ba amfanin da zai iya ƙara maka a rayuwarka ta ƙoƙarin zama mai sukuni?


7. Duk yadda ka kai da wayewa kana buƙatar addu'a da neman kariya a wurin Allah, a duniyar nan akwai manya-manyan abubuwa guda uku waɗanda ba ƙarya ba ne suna nan: -


A. Mahassada: Waɗannan ko ba ka yi musu komai ba ba su ƙaunar ganin ci-gabanka, yadda ka fara tasowar nan ba su da wani buri illa ganin durƙushewarka gaba ɗaya, za su yi aiki da bakinsu da hannunsu, wasu har da dukiyarsu fatarsu kawai ka durƙushe kamarsu, ko kar ka ɗaukaka irinsu, to sai ka tsaya da dugaduganka, ba wai ka je wurin Boka ba, don shi ma idan ka je ɗin abokin ciniki ya samu, zai yi ta tatsarka ne ta fuskar da ba ka sani ba, koma ga Allah.


B. Masu kambun baka: Waɗannan daban ne, duk abin da suka yi masa baki sai ya lalace, kuma ana haɗuwa da su ba a sani ba, shi ya sa zama da kowa lafiya yake da daɗi, kar ka yarda ka riƙa tada jijiyar wuya da mutane a kan sana'a, wasu ce maka za su yi "Je ka ka gani" sam ba su da aniyar alkairi a zuciyarsu, su ma irin waɗannan idan dai ana yin azkar kamar yadda shari'a ta tanadar abubuwa kan zo da sauƙi, kuskuren da mutum zai yi shi ne ya ce "Ba wanda ya isa ya yi min wani abu" su koma su kwanta. Kai ka tsarkake zuciyarka ka yi kyakkyawar mu'amala da mutane ka nemi tsarin Allah. Idan kana neman zama mai sukuni barci ba naka ba ne, ba ruwanka da kowa wani kuma kai ne matsalarsa.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (49) Cikin Sauki


C. Masu neman abu a wurinka: A cikin mutane akwai waɗanda ba za su zo wurinka neman abu ba sai sun kwana suna wuridi, yadda duk abin da suka ce suna so ka ɗauka ka miƙa, idan mai sana'a ya faɗa hannun waɗannan za su iya kwashe abin da ya tara na shekara 10 a dare ɗaya, ka ga sun karya ka kenan, koma ga Allah yadda ba za su iya samun nasara a kanka ba, na taɓa sanin wani mai ɗunkin hula, idan ya ce kaza yake so a ba shi kai da za ka saya dole ka biya, ba wai don ta yi maka ba, tsabar sihiri da tsafi, kafin su kawo maka kaya sai sun tsaface shi yadda suna gaya maka cikin rawar jiki za ka biya, ka ga a kan hanyarka ta zama mai sukuni idan ba ka koma ga Allah ba tsab za su tunkuɗe ka.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user