Saturday 2 June 2018

Karanta Kaji: Kuskure 7 da akai acikin Film din KANWAR DUBARUDU tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga


Tare Da:
Saddika Habib Abba
Suna: Kanwar Dubarudu
Tsara labari: Fauziyya D Sulaiman
Furodusa: Abubakar Bashir Maishadda
Bada Umarni: Kamal S Alkali
Kamfani: Maishadda Inbestment LTD

Jarumai: Ali Nuhu, Rahma Sadau, Aisha Aliyu Tsamiya, Aminu Sharif Momo, Nuhu Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Sulaiman Bosho, Rabi’u Daushe, Musa Mai Sana’a, Baballe Hayatu.

Labarin kanwar Dubarudu labarine na mutanan wani kauye (Kukan Mota) mai garinsu shine (Sulaiman Bosho) da sauran mutanan fadar sa wanda suke sakarcinsu tare domin an nuna duk yawancin mutanan garin sakar karu ne har kuwa da mai garin na su.

Sai kuma gidansu Dubarudu marayune iyayansu sun rasu suna tare da kanwarsa Tani ( rahma Sadau) da kuma matar Dubarudu Indo ( Aisha Tsamiya) sai Iya Marka ( Binta Kofar Soro) kawar kakar su Dubarudu makauniya ce idonta ba ya gani duk tare suke a gidan.

An nuna yanda Dubarudu ya ke mutukar son kanwarsa Tani an nuna Tani a matsayin shagwababbiyar yarinya ce bata ji saboda daurin gindin da ta ke samu a wurin Dubarudu a garin har ana yi ma ta lakabi da (Kanwar Dubarudu) saboda tsan-tsar soyyayar da ya ke nuna ma ta, kwata- kwata bayason bacin ran ta Dubarudu yakan iyayin ko me ne ne akan Tani mutukar wani ya bata ma ta rai duk kuwa da rashin da cewar abin in har ran Tani zai yi fari to zai aikata abin, hatta matarsa Indo( Aisha Tsamiya) idan ta ba ta ran Tani itama bata mata ya ke yi domin yafi son Tani fiye da ita, har Iya Marka itama dati- dari ta keyi da zaman ta tare da su Dubarudu saboda kaucewa batawa Tani rai saboda Dubarudu, kuma duk garin tsoran Dubarudu ake yi mai gari ne kawai ba ya tsoran Dubarudu, an nuna cewar kashi daya ne da Dubarudu shiyasa ko an da ke shi ba ya ji kuma duk wani abu na jarumta shi ake sanya wa a garin saboda karfinsa hatta ga sa idan za’ayi ta gudu shi ake san ya wa a a garin kuma shine yake ciyo wa garin.

Duk saurayin da ya zo yace yana son Tani in har Tani bata son shi a lokacin za ta dauki waya ta bugawa Dubarudu zai zo wurin ya yi wa saurayin duka ya kore shi, Kwatsam rannan sai jikan mai gari ya zo daga birni Abubakar ( Nuhu Abdullahi) suka yi arba da Tani yace babu wacce yake so sai ita, ita ma Tani ganin sa dan gayu dan birni nan da nan itama ta amince da shi aka fara soyyaya har abu ya yi karfi ya je kunnan Mai Gari shima ya nu na amincewarsa da goyon ba ya dari bisa dari Dubarudu yaji dadin hakan sosai kasancewar kanwarsa za ta auri farincikinta har aka yi musu baiko Dubarudu ya ta ho birni Birni karbar fansho din mahaifinsu saboda burin da ya ci na siyayar auran Tani, Mado ( Aminu Sharif) ya shige musu gaba ska je Birni suka karbo kudinsu suka da wo ana ta shirye shiryen auran Tani da abubakar.

Amma daga ba ya da iyayen Abubakar (Rabi’u Rikadawa) da (Asma’u Sani) suka zo daga birni suka ji labarin wadda dansu zai aura kuma suka gan ta suka tubure akan su dansu bazai auri Tani ba domin ya yi karatu mai zurfi kuma yana dan birni ba zai auri ‘yar kauye ba, sai daga ba ya da dannasu ya tubure musu akan cewar shi sai ya auri Tani kuma suka ji labarin yanda Dubarudu ya ke kulawa da Tani sai kuma suka amince masa akan ya auretan.

Abubuwan Birgewa

1-Jaruman film din sunyi kokari wurin baiwa mai kallo dariya musamman Dubarudu (Ali Nuhu) da kanwarsa Tani (Rahma Sadau)

2- hotunan film din sun fita radau sun kayatar da masu kallo.

3- sauti ya fita yadda ya kamata a film din.
kauyan da akayi amfani da shi ya da ce da yanayin labarin.

4- Marubuciyar labarin tayi kokari wurin hado zaren labarin wuri guda a karshan film din.

5- Jaruman film kowanne ya da ce da gurbin da aka sanya shi a film din.

Kurakurai

1- wakar da aka sanya a film din kwata- kwata bata da ce da labarin film din ba.

2- An nuna cewar Dubarudu ya karya alfa ( Rabi’u Daushe) a kafarsa sannan ya karya Tanimu ( Baballe Hayatu) a hannunsa sakamakon fado da su da ya yi daga saman katanga har suka kawo kara gurin mai gari kowannansu an sanya masa kara an daure a inda ya karye amma sai gashi hoto na gaba mai kallo bai ga wannan karan ba kuma kowannasu ya warke garau kuma ba’a rubuta bayan wani lokaci ba ballan ta na ace ko’a wannan lokacin ne suka warke ko targade suka yi bai ci ace har a wannan karamin lokacin sun warke ba ballan ta na karaya.

3- Almajirin da’aka san ya ya shigo bara gidansu Dubarudu a lokacin da suke cin abinci tare da abokansa Alfa da Mudi ya yi girma ace kamar wannan ya shiga gida yin barar abinci.

4- An nuna Dubarudu yana bin zakaran Tani zai kamashi har ya dinga fa dawa gida jan mutane yana bin zakaran duk in da ya yi, masu kallo kowa yaga cewar zakara ne amma sai gashi da Dubarudu ya dawo gida kanwarsa Tani tana maganar kazarta kazarta shin Tani batasan zakara ba ne take kiran kaza ce? kuma sai gashi wasu daga cikin mutanan da suka kawo karar Dubarudu ya shigar musu gida har suka yi cin ci rindo kofar gidansa tare da Mai Gari suma mutanan suna maganar kaza ce Dubarudu ya ke bi har ya shigar musu gida kuma a wurin ga zakaran suna kallonsa a hannun Tani shin duk basu san bambamcin kaza da zakara ba ne?

5- akwai lokacin da Dubarudu ya shigo gidansu yana ta do ka sallama Iya Marka ta ke fada mishi ta ji yana ta fara’a lafiya dai ko? ita da ta ta ke makauniya a ina ta ga fara’ar Dubarudu? tinda a fuska ake ganin fara’a ba jin ta ake yi ba.

6- Katsam mai kallo ya ga shigowar Mado (Aminu Sharif) cikin rayuwarsu Dubarudu har aka ga ya shige musu gaba sun karbo fansho da garatuti din mahaifinsu a birni amma ba’a fadi alakarsu ba ba’a bayyana Mado ko shi wanene a wurin su Dubarudu ba kawai an gan su ta re kuma daga bisani sai gashi sun dawo kauyan ta re har yana neman sa ce Kudin da aka karbo na fansho din da garatutin.

7- Shin Indo ba ta da iyaye ne ko kuma dangi? har film din ya kare ba’a nuna su ba kuma ba’a fadi wani abu akansu ba.

Karkarewa

Fim din Kanwar Dubarudu an yi kokari wurin sanya nishadi da abubuwan ban dariya a cikinsa, amma labarin babu cikakken sako a ciki. Allahu a’alamu!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user