Wednesday 23 November 2022

Sharhin Shirin Labarina Mai Dogon Zango

Tura Wannan Zuwa Ga

Fim ne da tashar AREWA 24 ta fara nunawa a Litinin ɗin da ta gabata. Ibrahim Birniwa ne ya rubuta labarin, haka nan kuma ya ƙunshi 'yan wasa ƙwararru kamar, Nafisa Abdullahi, Garzali Miko, Ali Artwork  Hadizan Sima, Hafsat Idris, Aminu Asid, Jazuli Mukaddas da sauransu. 


Shirin Labarina
Hoto: Saira Movies TV


Marubuci: Muhammad Lawan Prp


Labarina yana bada labarin wata yarinya Sumayya (Nafisa Abdullahi) wadda ta kasance marainiya wadda mahaifinta ya mutu. Mahaifiyarta (Hadizan Sima) na fama da rashin lafiya, an kai ta asibiti sai dai ƙoƙarin neman kuɗin sayen magani ya jefa Sumayya a matsala, ban da harin fyaɗe da ɗan gidan matar da suke haya gidanta (Garzali Miko) ya nemi yi mata, akwai wani mai kemis a unguwarsu Nura (Aminu Asid) ya nemi ta ba shi haɗin kai kawai sai ya ba ta magungunan da aka rubuto wa mahaifiyarta, amma shi ba zai ba ta bashi ba.


Wannan ya tada hankalin Sumayya ta shiga neman mafita. 


Mal. Aminu Saira yayin ɗaukar shirin Labarina Mai Dogon Zango
Hoto: Aminu Saira


Fim ɗin mai yanka-yanka (series) yanka na farko ya ƙare ne a inda Sumayya ta ga ba mafita ta koma wurin Nura tare da amincewa buƙatarsa. 


Fim ɗin ya yi kyau ƙwarai, musamman yadda labarin ya tafi tiryan-tiryan ba karyewa, mai yiwuwa saboda ya haɗu da ƙwararren Marubuci ne. 


Jarumi Rabi'u Rikadawa a matsayin Baba Ɗan Audu yayin ci gaba da ɗaukar shirin Labarina Mai Dogon Zango
Hoto: Aminu Saira

'Yan wasa sun taka rawa sosai, ta yadda za ka ga tamkar gaske ne.


Idan ka fara kallon fim ɗin ba za ka so tashi ba har sai ka ga yadda za a ƙarke. 


Sauti da hoto sun fita raɗau! Ba laifi. 


Tambaya Da Shawara 


Babu wani mai kemis a faɗin garin ban da Nura ne, an ga Nafisa tana ta jele wurinsa.


Yana da kyau a nuna ta je wani ɗakin shan maganin, idan ya so sai a ce ai babu wasu magungunan.


Wannan sharhin zango na farko ne, kashi na ɗaya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user