Thursday 24 November 2022

Siffofin Mutanen Da Za Su Guje Ku A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Akwai wasu mutane wanda kusan kowa yana da su. Idan ka ga kiransu buƙatarsu ce ta taso, ba za su taɓa nemanka akan wani ci-gaba da ya shafe ka ba.


Mutanen Banza
Hoto: Psych Central


MarubuciYahaya S. Kaya


A kodayaushe suna da yaƙinin cewa kai ne mai warware matsalolin su, suna da tabbacin cewa kai ne za ka taimake su a duk lokacin da suka buƙata.


Suna da gaggawa, kuma suna so idan suka zo da buƙata ka a je duk abin da kake yi ka saurare su, hakan ya nuna suna da son kai.


Idan ba ka da lafiya ba lallai su gaisheka ba koda a ce sun sani, saboda dama ba sa nemanka sai sun shiga matsala.


Da a ce za a samu matsala rana ɗaya ka kasa yi musu taimakon da suka buƙata, za su zage ka a bayan idonka, kuma su ce ba ka taɓa yi musu rana ba.


Idan kana yin kasuwanci za su fara da neman aron kuɗi saboda sun san kana da shi kuma za ka ba su, za su fara amsan kayanka kyauta, ba za su ba ka ba har sai an kai ruwa rana.


Waɗannan mutanen ba mutanen arziki ba ne, mutanen banza ne, saboda ba so suke yi ku taru ku gina kanku ba, so suke yi kai da ka gina kanka, su rusa ka.


Yawancin su suna barin ka da zarar sun tabbatar da cewa ta ƙare maka, ma'ana kai ma ka shiga hali na matsin rayuwa ko jarabta.


Za ku haɗu a hanya za su yi fuska kamar ba su san ka ba, ko su fara yin wayar ƙarya.


Ku canja su, wallahi jabun abokai ne.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user