Friday 25 November 2022

Hanyar Da So Ya Fi Kama Wasu Mutanen Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

Tabbas shi SO tamkar tuntuɓe yake, a kan cikaro da shi wajan da ba a yi zato ba. Abin nufi anan shi ne, wani lokacin ba ka shirya yin Soyayya da kowa ba amma za ka ga ka ci karo da wadda ta zama tilas sai ka kulata.


Yadda So Yake Kama Wasu Mutane
Hoto: Wallpaper Cave


MarubuciNura Nakowa


Misali, za ka iya tsintar kanka a wani guri wanda ba da manufar ka kula wata ka je gurin ba amma hira ko kwatance ko tambaya ya zama sanadin ƙulla alaƙar soyayya tsakanin ka da wata (su ma matan haka ne).


A wani lokacin ma a dalilin wasa ko tsokana ko ɓacin rai yakan zama sanadin soyayya har ma ta kai ga an yi aure.


Ga wasu misalai kamar haka:-


Akwai wani bawan Allah wanda yana daga cikin abokan wani ango waɗanda suka haɗu a wajan walimar aure. Suna zaune a mazaunin su sai ya fuskanci cewa ɗaya daga cikin 'yammatan da suka zauna a kujerun da suke fuskantar nasu ta yi zaman ƙasaita (wato ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya akan guwairta). To sai shi wannan mutumin yake gani kamar ta yi rashin kunya saboda haka bari ya je ya ankarar da ita. To da ya je sai ya je a fusace, yana zuwa sai yasa hanu ya tunkuɗe ƙafar yarinyar kuma ya rufe ta da faɗa. Ita ma da ta ga haka sai ba ta raga masa ba, ta dinga gaggaya masa magana. 


Haka a ka zo aka shiga tsakani aka raba su da ƙyar. 


Amma na katse muku labarin, kasancewar sa abokin ango, ita ma ƙawar amarya sai da sanadi ya sa suka shirya har kuma ya aure ta.


To wannan kenan, karku tambaye ni ko wanene don na san shi ma zai ga wannan saƙon. Hahaha..


Shi kuma wannan ya zo unguwar su abokin karatun sa ne (Ɗan ajin su). Suna tsaye a ƙofar gida sai wata budurwa ta wuce ta gaban su ta shiga cikin gidan, da ta fito sai shi baƙon yake cewa abokinsa ka ga wata kyakkyawar yarinya. Shi ne abokin nasa ya ce masa ai ƙanwata ce idan kana so sai na ba ka ita. Tana waigowa sai ta ce da shi da ya ke haka bayarwar keda sauƙi ba? Shi ne shi baƙon ya ce mata "Ki yi haƙuri, ni da wasa ma nake ina da wacce zan aura.". Sai ta maida martani cewa idan ma da gaske kake kwaji dashi.


To wannan ma kar na kaiku da nisa ashe 'yar maƙotan su ce kuma alaƙar ce silar auren su.


Wannan abu ya faru a ɗaya daga cikin unguwannin ƙofofin Kano.


A ci-gaba da bibiyar mu a ranakun litininlaraba, da juma'a domin ganin abin da muka wallafa na soyayya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user