Monday 28 November 2022

Kyawawan Dabi'un Mutanen Da Suka Fi Samun Nasarori A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Sakamakon neman ilimi da nake yi a manyan ƙasashe biyu na duniya, da kuma zagaye sama da kasashe goma sha bakwai a duniya, na haɗu da jama’a masu yawan gaske, kuma na koyi abubuwa da dama daga wajensu.


Ɗabi'un Mutane Masu Nasara
Hoto: Freepik


MarubuciBello Galadanchi


Na buɗe kamfani na farko a Amurka ina da shekaru 21, sannan na samu aiki a Muryar Amurka ina da shekaru 24. Na kuma buɗe makaranta tawa ta kaina ina da shekaru 28. Na yi nasara a wasu harkokin, wasu kuma na faɗi, lamuran da suka koya mun darussa da yawa na rayuwa. Sakamakon waɗannan hawa da sauka, da kuma haɗuwa da mutane da yawa waɗanda suka yi nasara, a nawa ra’ayin akwai  manya-manyan ɗabi’u guda huɗu;


1. BA SU KWAIKWAYAR SAURAN JAMA’A, SAI DAI A KWAIKWAYE SU: Abubuwan da sauran jama’a suke yi ba su harzuƙa su. Kullum tunaninsu shi ne ta yaya za’a inganta waɗannan abubuwa? Sun fi mayar da hankali akan abubuwan da ke da naƙasu, kuma al'umma ba ta ankara ba, da kuma irin alherin da za’a samu daga warware waɗannan matsaloli. Da sun gama fahimtar haka, sai su hau aiki.


2. SUN SAN ABUBUWAN DA SUKA IYA: Masu nasara a rayuwa sun fi mayar da hankalinsu akan abubuwan da suka riga suka iya, da kuma watsi da inda suke da matsala. Abin da suke yi shi ne ƙara himma da ƙwazo wajen ƙwarancewa da laƙantar abubuwan da suka iya, domin su fi kowa.


3. SUN IYA HAƊA HAZAƘA DA BAIWA: Kowa a duniyar nan yana da irin nashi baiwa. Su mutanen dake nasara a rayuwa na fahimtar baiwar su, sannan su kasance masu aiki tuƙuru domin inganta ta, da kuma ganin ta warware matsalolin al'umma.


4. DOGARO DA ALLAH: Mutanen dake nasara sun fahimci cewa duk ƙwazonsu, dole sai sun haɗa da ibada. Sun san cewa addu’a ba ta aiki idan mutum bai miƙe tsaye ya nemi abin da yake buƙata ba. Saboda haka sun fi kowa addu’a, kuma sun fi kowa ƙwazo.  


Ga misali: Hajiya Aisha ta iya dafa abinci (2. SUN SAN ABUBUWA DA SUKA IYA), saboda haka, ta yanke shawarar buɗe sabon gidan abinci na zamani. Amma abin da ta lura da shi shi ne, gidajen abinci suna da matuƙar yawa, saboda haka ta yaya za ta bambance nata da na sauran mutanen garin baki ɗaya? (1 BA SU KWAIKWAYAR SAURAN JAMA’A, SAI DAI A KWAIKWAYE SU) Hajiya Aisha ta lura cewa jama’a da yawa suna zuwa gidan abinci, amma sai ruwan ido ya hana su zaɓen abin da suke so. An riga an yanke musu shawara, sai dai su zaɓi irin abincin da suke so, masu dafawa su dafa. Ita kuma, sai ta ƙirƙiri wani sabon tsari. Tsarin shi ne duka kayan abincin da ba’a dafa ba suna waje, an jera su a cikin gilashi. Naman kaza ne, salak ne, naman rago, ganda, karas ne, doya, dankali, shinkafa, taliya, wake da sauransu. Wato idan kwastoma ya shigo, sai ya ɗauki fanteka, ya zaɓi duk abin da yake so da hannunsa, iya adadin da yake so, sannan a auna akan sikeli, ya biya. Hakan kuwa ya bai wa jama’a sabon salo na sayen abinci, kuma an warware matsalar masu ruwan ido. Mutum zai iya cin duk wani irin abinci da ke wannan shago, iya adadin da yake so, ba tare da kashe kuɗi ya sayi ire-iren abinci biyu ko uku ba. Zai iya haɗa naman rago, naman kaza, taliya da karas. Wani kuma idan ya tashi, sai ya haɗa kifi, salak, shinkafa da taliya. Ba’ayi watanni uku ba, duk labari ya baza gari na wannan sabon gidan abinci mai bai wa jama’a ‘yanci, lamarin da ya yi sanadiyar cincirindon kwastomomi har daga bayan gari. Don ta bunƙasa sana’arta (3 SUN IYA HAƊA BAIWA DA HAZAKA), kullum ƙarfe biyar take tashi da asuba ta fara shirya kayan abinci, ta tabbatar an wanke shagon kuma ta aikawa kwastomominta gaisuwa a shafinta na WhatsApp, da kuma irin sabon kayan abinci da za ta kawo a wannan rana.


Wannan labarin ƙirƙirar shi na yi. Idan akwai wanda yake sha’awar wannan sana’a, to sai ya tuntuɓe ni domin zurfafa tunani da fasalta shi yadda za’a samu alheri. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user