Friday 7 June 2019

Karanta Kaji: Kuskure 4 da akai a cikin Film din SALMA BANKWANA tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Salma Bankwana.
Daukar Nauyi: Nura M. Inuwa.
Kamfani: ABNUR Entertainment.
Shiryawa: Abdul Amart.
Bada Umarni: .Sadik N. Mafia.


Salma Bankwana
SHARHI: Musa Ishak MuhammadJarumai: Adam A. Zango, Fati Washa, A’isha Aliyu Tsamiya, Hadiza Muhammad, Baballe Hayatu, Balarabe Jaji, Asamau Sani, Alasan Kwalli, Malam Inuwa, Bankaura, da sauransu.


Fim din “Salma Bankwana” fim ne da aka gina shi a matsayin ci-gaban fim din “Salma.” Fim ne da yake dauke da labarin wani matashi mai suna Naseer (Adam A. Zango) mai tsananin soyayya ga kanwarsa kuma budurwarsa wato Salma (A’isha Aliyu Tsamiya). Sun kasance suna tsananin kaunar junansu, domin kuwa sun shaku sosai, sai dai kash! Salma ta rasa rayuwarta sakamakon hadarin mota da ya ritsa da ita a lokacin da ta tafi Sakkwato domin rabon katin bikinsu da Naseer.


Rasuwar Salma ta zowa Naseer da wani irin yanayi mawiyaci, wanda hakan ne silar susucewar komai nashi. Saboda a kullum ba shi da abun yi idan ba tunaninta da anbatonta ba. Ta kai har sunbatu ya ke a kanta. A bangare guda kuma akwai Minal wadda take tsananin kaunarsa wadda hakan ya tilasta mata yin komai irin na Salma domin ta samu shiga a gurun Naseer.


Wannan shi ne a takaice abunda ya faru a cikin fim din Salma wanda kuma shi ne tushe na wannan fim mai suna “Salma Bankwana.” A haka Naseer ya ci gaba da rayuwa cikin tsananin kewar Salma da kuma bayyana irin tsananin kaunar da yake mata duk da ce wa bata raye, domin har fada yake cewa shi fa a gurunsa Salma bata mutu ba domin tana rayuwa ne a cikin zuciyarsa.


Ita kuma Minal tana ta ci gaba da shirye-shiryen yadda zamanta sai kasance da Naseer domin kuwa an kusa aurensu. Tana ta shirin ya za ta yi ta saka shi ya manta da Salma sannan ya maye gurbinta a zuciyarsa da ita. Sai dai tun kafin auren nasu, Naseer ya sha fadawa Minal cewa dole sai ta yi hakurin zama da shi saboda shi bazai taba yi wa wata mace irin son da ya yi wa Salma ba.


A daya bangaren kuma, a can gidansu Naseer wato gidan da suka rayu da Salma a lokacin da take raye, akwai kanwar Salma mai suna Sakina wadda ita ma take cikin tsananin son Naseer sai dai ta kasa samun amincewarsa, saboda ya ce dabi’unta sam ba su yi kama da na Salma ba, saboda haka ba zai taba aurenta ba. Duba da irin mawiyacin hali da Sakina take ciki ne yasa mahaifinta wato Alhaji wanda shi ne ya rike Naseer a gidansa tun yana karami, ya kirawo Naseer a kan ya daure ya auri Sakina duba da cewa ita kadai ce ta rage musu a rayuwarsu tunda Allah ya karbi rayuwar Salma kuma basa so ita ma su rasa ta saboda ciwon sonsa. Sai dai a nan ma Naseer ya kara bayyanawa Alhaji cewa fa sai dai a yi hakuri saboda gaskiya shi bazai iya auren Sakina ba.


Bayan an yi auren Naseer da Minal, Minal ta fara karo da matsaloli tun a daren da aka kai ta gidan Naseer, domin ya ringa kiranta ne da sunan Salma wanda hakan ya yi matukar bakantawa Minal rai, sai dai ya bata hakuri da neman cewa ta yi masa uzuri. A Haka dai tayi ta rayuwa cikin kunci a gidan Naseer domin kuwa kullum haukarsa a kan Salma kara bayyana take.

Kullum kokarinta shi ne ya za a yi Naseer ya dan bata dama domin ta bayyana irin cikakkiyar soyayyar da take masa, amma sai dai hakan yaki samuwa. Haka Naseer ya bi ko’ina a cikin gidan nan ya cike shi da hotunan Salma, amma Minal duk tayi hakuri saboda burinta na ganin farin cikin mijnta.


Hakurin Minal ya je karshe, domin kuwa wata rana ta dauki hoton Salma ta yi jifa da shi a kasa wanda hakan ya saka ya farfashe, ai kuwa nan take Naseer ya hau dukanta. Yana cikin dukan nata ne sai ga mahaifiyarta Hajiya Balaraba (Asamau Sani) da kaninta Bashir (Abba Kabugawa) suka shigo, suna shigowa ne fa suka samu Minal tana ta kuka shi kuma Naseer ya biyo ta da gudu yana fadawa mahaifiyarta cewa wai Salma ta kirawo da gawa. A nan ne dai Hajiya Balaraba ta dauke Minal ta tafi da ita gida kuma ta ce mahifin Minal sai ya nemar mata hakkinta. Wanda sakamakon hakan ne aka saka ‘yan sanda suka shigo har gida suka kama Naseer aka je aka kulle shi.


A karshe bayan an fito da Naseer daga hannun ‘yan sanda, Shi ne Alhaji wato mahaifinsa na ruko ya dauke Naseer da abokinsa Kabeer (Baballe Hayatu) zuwa gurun Malam (Malam Inuwa) inda a nan ne aka yi wa Naseer wa’azi mai nawi da ayoyi da hadisai, wanda hakan ya zama silar yin nadamarsa a kan irin abubuwanda ya aikata. Sannan ya kirawo Minal ya bata hakuri, kuma ya yi mata alkawarin daina dabi’un da yake, wanda bayan ta amince ta dawo gidanta ne a ka nuno shi ya dakko duka hotunan Salma da suke gidan yana kona su. Sannan kuma ya koma gida ya yi wa Sakina alkawarin zai aureta yanzu.


Abubuwan Yabawa


1. Sunan Fim din ya dace da labarin.


2. Labarin mikakken labari ne wanda bai yanke ba tun daga farkon shi har karshensa.


3. Fim din ya samu aiki mai kyau kwarai da gaske.


4. Jaruman duka sun dace da labarin duba da irin rawar da kowanne ya taka a gurbinsa.

5. An samu kalamai na kwarewa a cikin fim din.


6. An nuna tasirin yin soyayyar gaskiya, domin tana yin tasiri sosai idan an gina ta a kan gaskiya.


7. An nuna tasirin samun mace ta gari domin dabi’un Salma kyawawa da kuma addinin da take da shi, su ne suka saka Naseer yake mata irin wannan so din.


Salma Bankwana
Kurakurai1. Duk irin abinda Malam ya fadawa Naseer wanda har suka zama silar chanjawar sa,an fada masa irin su a baya amma mai yasa bai canja tun a lokutan ba har sai da aka zo gurun Malam sannan?


2. Lokacin da aka nuna Naseer yana tuna lokacin da yake fadawa Salma cewa yana so ya mallaka mata rabin dukiyarsa, ba a nuna wa mai kallo cewa za a shiga tunani ba kuma ba a nuna masa an dawo ba,


wanda hakan zai sa mai kallo ya yi zaton cewa ita ma wannan fitowar da aka nuna ana tunanin, ba wai tunanin bane.3. Ya kamata a dan nuna rayuwar Minal da Naseer a gidansu bayan ya canja domin a nuna ta samu farin ciki ko yaya ne a gidanta.


4. Irin kalaman da Naseer yake amfani a kan kowa wajen bayyana irin son da ya ke yi wa Salma suna yin tsauri da yawa, duba da irin yadda yake magana da iyayensa da kuma sirikarsa akan Salma.


KarkarewaFim din “Salma Bankwana” fim ne da ya nuna irin yadda ake samun wasu sukan samu kansu a cikin matsananciyar soyayya da kuma irin halin da suke samun kansu a ciki.

An nuna tsantsar soyayya ta gaskiya a cikin fim din da kuma irin tasirin da take yi a cikin zuciyoyin maabotanta.

Sannan an nuna kwarewa sosai a cikin aikin fim din, domin kun an samu nasarori da yawa kuma ya kayatar da mai kallo.


Kuma ba a samu kurakurai da yawa a cikin fim din ba.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: Leadership Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user