Saturday 1 December 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai a cikin Film din DAN KUKA A BIRNI tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Dan Kuka A Birni
Tsara Labari: Munzali M. Bichi
Kamfani: 2nd Term Empire
Shiryawa: Kabiru A. Zango
Umarni: Adam A. ZangoJarumai: Adam A. Zango, Fati Washa, Ado Gwanja, Zahraddini Sani, Nasiru Horo, Falalu A. Dorayi, Bado Waziri, Mustafa Naburaska, Jamila Zam-Zam. Da sauransu

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Buba (Ado Gwanja) dauke da jakar matafiya a cikin kauyen su yana neman motar hawa, anan ne ya hadu da mai mashin din haya kuma ya bukaci ya hau don a kai sa tasha, amma sai mai mashin din ya nuna doka ta hana yin goyo, Buba yana nan a tsaye har zuwa sanda wata mota ta sauke wani dan kasuwa a gefen hanya wanda a wajen suka soma rigima da Buba, suna cikin fadan ne Buba ya samu motar zuwa binni tazo giftawa nan ya hau suka tafi.

Bayan saukar sa a cikin tasha ne sai wani barawo Dan Bilki (Zahraddini Sani) ya kyalla ido yaga jakar kayan Buba wadda ya ajiye a kasa don biyan kudin mota, nan fa Dan Bilki ya sace jakar ya gudu wanda hakan yasa bayan Buba ya ankara yabi bayan sa suka kasa tsere kuma sai yi nasarar kama Dan Bilki ba har sai bayan ya gama caje jakar yaga babu abin arziki sai tarkacen tsummokarai, hakan yasa yaji haushi ya bawa Buba jakar sa amma sai Buba ya nuna masa cewar yana dauke da wata takarda ta kudin adashi wanda yazo garin da nufin karba.

Jin haka ne yasa Dan Bilki ya nuna masa cewar yazo gidan sa ya ba shi masauki kafin sanda zai karbi kudin, kuma ya tsara haka ne da nufin sace kudin idan Buba ya karbo, Bayan sun je gidan ne ya ajiye Buba a dakin sa amma sai Buba ya nuna bazai kwana a dakin da babu gado da katifa gami da kayan kallo ba. Jin hakan ne yasa Dan Bilki ya tafi wajen wani abokin sa ba sakkwace mai sayar da nama, wato Ali Meat (Mustafa Naburaska) ya karbo kudin da yake bin sa ba shi sannan ya hado da rancen wasu makudan kudin da nufin sayen kayan more rayuwa don a sakawa Buba a daki kafin sanda zai karbi kudin da shi su sace kudin.

Bayan Dan Bilki ya karbo kudin ne sai yazo ya zuba kayan alatu a cikin dakin da Buba yake ta yadda babu abinda Buba zai nema ya rasa kuma ruwa ma bayashan na rijiya sai na roba mai dadi, haka Dan Bilki ya cigaba da yi masa bauta da nufin wata rana kudin sa za su dawo idan Buba ya dauki kudin adashi, Dan Bilki yayi kokarin ya sace jakar Buba da nufin daukar takardar adashi amma sai Buba yaki yarda ya ajiye jakar sa a dakin, duk inda zai je ko bacci zai yi tana jikin sa, hakan ne ya hana Dan Bilki damar sace jakar sa har sai bayan wani lokaci wanda Buba ya mance jakar a cikin daki.

Nan fa Dan Bilki yabi dare ya zazzage jakar tas amma bai samu komai ba sai wata tsohuwar takarda mara amfani, hakan ne yasa ya tubure akan sai Buba ya biyashi kudaden sa ko kuma ya hada shi da hukuma, nan ta ke kuwa Buba ya amince zai biyasa amma da sharadin sai dai ya koya masa sana’ar sa don a samu kudi, haka Dan Bilki ya koya masa sana’ar sa ta sata amma a karon farko da Buba ya dira a wani gida ya goce a kafar sa bai koma ba sai bayan ya warke kuma da ya koma yayi satar kaya a wata mota nan fa kare ya biyo sa, haka Buba yayi ta bulayi har wata rana ya fado hannun wata matar soja (Fati Washa) wadda take kawo maza gidan ta don yin lalata ta rude su da kudi, amma sai akayi katari mijinta ya dawo sanda Buba yazo gidan, haka Buba yabar gidan da kyar bayan sojoji sun sako shi a gaba za su kama shi.

Kwatsam wata rana sai ga shugaban ‘yan dabar kauyen su Buba (Adam A. Zango) ya shigo birni tare da abokin Buba (Nasiru Horo) tare da sauran tawagar sa ta ‘yan daba, sun zo birni da nufin neman Buba don ya kashe as saboda ya mari kanwar sa. Sai akayi katari kuma Dan Bilki ne ya bawa gayyar ‘yan daban masauki a gidan sa inda Buba yake, duk da dai a sannan Buba yayi wata tafiya baya nan, haka ‘yan daban suka yi ta zaga gari suna neman Buba amma basu gan shi ba, dama kuma sun taho da abokin Buba din ne da nufin ya nuna musu Buba saboda su basu san shi ba, amma sai ga shi wata rana Buba yazo gidan ya tarar da gayyar ‘yan daban sun hadu ba tare da sun gane shi ba. Cikin dare kuwa Buba ya dauke abokin sa (Nasiru Horo) suka gudu daga gidan.

Abubuwan Birgewa:

1- Fim din ya nishadantar da mai kallo.

2- Jaruman sun yi kokari, musamman Buba (Ado Gwanja)

3- Camera ta fita radau, kuma an yi kokari wajen nuna salo wajen amfani da ita. Haka ma sauti ba laifi.Kurakurai:

1- A farkon fim din lokacin da Buba ya fito daga cikin kauye neman motar zuwa Birni, bayan me mashin yace masa ba za shi tasha ba, a sa’in ne kuma wata mota ta sauke wani makeri, tunda an nuna Buba ya fito neman motar hawa ne to ya dace ya gwada fara tsayar da motar da ta sauke makerin ko za su kai shi birnin da ya fito da nufin zuwa, domin yanayin yadda ya kalli motar ya basar, yafi kama da cewar ba wannan motar aka tsara zai hau ba.

2- Lokacin da Dan Bilki ya sace jakar Buba, bayan Buba ya bi bayan sa sun kasa tsere suna gudu, me kallo yaga Dan Bilki ya buya a tsakanin wasu motoci ya zazzage kayan yana dubawa, a sannan ne Buba yazo ya wuce ta wajen a guje sai kuma aka ga ya sake dawowa daidai jikin motar yana duba sa. Shin Buba yasan cewar a tsakanin motocin Dan Bilki ya buya da har ya dawo wajen yana laluben neman sa?

3- Lokacin da Buba yazo birni an nuna Dan Bilki a tasha ya sace masa kaya wanda silar hakan har suka kulla alaka tare, tun daga sannan kuma ba’a sake ganin Dan Bilki a tasha ba, amma kwatsam lokacin da ‘yan daban kauye masu neman Buba wato su (Adam A. Zango) suka sauka a birni cikin tasha, mai kallo yaga Dan Bilki a cikin tashar a tsaye a gefe, shin dama Dan Bilki ya san da zuwan ‘yan dabar ne da har ya sake zuwa tasha a wannan lokacin? Ya dace a samar da wani dalilin mafi gamsar wa na haduwar ‘yan daban da Dan Bilki amma ba wannan ba.

4- Me kallo yaga Buba ya shiga cikin gari da nufin yin tafiya neman kudi a daidai lokacin da su (Adam A. Zango) suka zo gidan Dan Bilki da nufin zama, matsayin Buba na wanda ba dan gari ba, ya dace a sanar da inda zai tafi yawon neman kudi wanda har yasa yace zai dau lokaci a can kafin ya dawo, idan kuma sabani ne aka shirya don kada su hadu da ‘yan dabar dake farautar sa, to ya dace a samar da kwakwkwaran dalilin yin sabanin na su koda ta hanyar cewa Buba ya koma kauye ne don ganawa da budurwar sa Asiya.

5- Lokacin da Dan Bilki (Zahraddini Sani) ya kawo Buba cikin gidan sa, a sanda suka fara sa’insa da makahon da yake haya a gidan sa (Bado Waziri) me kallo yaga ‘yar makahon ta fito daga daki tana tambayar ba’asin abinda ke faruwa, wanda dalilin hakan ne yasa Dan Bilki ya wayance ya nuna Buba yake ciwa mutunci ba mahaifin ta ba. Shin wace alaka ce tsakanin Dan Bilki da ‘yar makahon wadda har hakan yasa yake shakkar cin mutuncin mahaifin ta akan idon ta? Domin har fim din ya kare ba’a nuna cewar budurwar sa bace ko kuma wadda yake wata alakar da ita, sannan kuma ba’a nuna cewar yana tsoron mace ba.

6- Lokacin da matar soja (Fati Washa) ta kawo Buba cikin dakin baccin ta, a sa’in da mijinta ya dawo gida ta boye Buba a cikin kwabar kayan sawa, bayan shigowar sojan me kallo yaga ya bude kwabar a sanda matar tashi take hilatar sa don kar ya bude saboda gudun kada asirin ta ya tonu, amma bayan sojan ya bude kwabar sai aka ga mamaki karara akan fuskar sa duk da an nuna cewar Buba ba ya cikin kwabar kuma bai gan sa ba. Shin wane abu sojan ya gani wanda hakan ya bayyana mamaki karara akan fuskar sa? Tunda bai ga abinda matar tashi take boyewa ba ya dace a samar da wani dalilin na sauyawar fuskar sa koda ta hanyar nuna cewar yaji warin wani abun yana tashi daga cikin kwabar ne.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar sosai, sai dai kuma babu hakikanin cikakken sako ko darasi a cikinsa, sannan kuma labarin bai dire har karshensa ba, domin ba a warware zaren labarin da a ka tufka ba. Idan kuma fim din akwai cigabansa ne, to kuwa ya dace ko da a rubuce ne a bayyana wa mai kallo hakan a karshen fim din, don a fahimtar da shi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: LEADERSHIP A YAU

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user