Thursday 29 November 2018

Karanta Kaji: Kadan Daga Cikin Illolin Shan Taba Sigari Ga Lafiyar Dan Adam

Tura Wannan Zuwa Ga
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN-ƘAI. SALATI DA AMINCI SU TABBATA BISA ANNABIN DA BAI TA'BA SAƁO BA. DA IYALANSA DA SAHABBANSA DA DUKKAN BAYIN ALLAH NAGARI.




Rubutawa: Zauren Fiqhu

MECECE TABA SIGARI?

Ita dai taba sigari, ana samunta ne daga tsiron TOBACCO, wanda tarihi ya nuna cewa turawan Maxico da Spain sun kasance suna nomawa tun kusa Shekaru dubu kafin haihuwar Annabi Eisa (as) - wato 100 BC.
Taba Sigari ta shigo Qasar Amurka ne ta hanyar wani bature mai suna Christopher Colombus.

Kuma ta shigo Kasashen Africa ne ta hanyar turawa 'yan Mulkin Mallaka, da kuma 'Yan kasuwa.

Sun shigo da ita tun suna bayarwa amatsayin abun ciniki, suna karbar abubuwa irin namu na Africa, har zuwa lokacin da suka zama 'Yan Mulkin mallaka suka Kwace gonaki da filayen bakaken fata, suka fara nomata suna sayarwa kuma suna tafiya da ita zuwa Kasashensu.

HANYOYIN AMFANI DA ITA.

Mutanen wancan zamanin sun kasance suna Tauna ganyenta ne suna hadiyar yawun, daga baya kuma suka fara Sanya busashen ganyenta acikin Lofe (pipe) suna Zuka.

Daga baya kuma sai turawa suka Qirkiro wata sabuwar hanyar, suna Murza busashen ganyen tobacco suna sanyawa cikin takardun da aka nannade, wannan ita ake kira Sigari.

Daga baya kuma acikin 'yan shekarun nan sun bullo da wani sabon salo, suna sanya mata wasu sinadaran da suke sanya mata Qamshi irin na 'Ya'yan itace kamar Mangoro ko Strawberry ko Apple da sauransu. Wannan shi ake kira SHISHA.

ILLOLIN DA TAKE HAIFARWA

Illolin taba ga lafiyar 'Dan Adam ba zasu lissafu ba, sai dai mu gutsuro kadan daga cikin abinda bincike ya tabbatar kamar haka:

CIBIYAR BINCIKEN CUTUTTUKA TA KASAR AMURKA (CDC) TACE:

1. Shan taba Sigari yana sanadiyyar mutuwar Matasa sama da mutum 480,000 (dubu dari hudu da tamanin) duk shekara. Akasar Amurka kadai.

2. Sama da mutane MILIYAN SHA-SHIDA (16,000,000) ne suke fama da cututtuka daban daban wadanda suke da alaka da shan taba Sigari.

3. Anyi kiyasin cewa sama da mutane miliyon 88 ne suke cutuwa ta dalilin Sigarin da Waninsu yake sha. Kuma Mutane Miliyon 41 ne suka rasu ta dalilin shaqar hayakin da masu shan taba suke hura musu.

4. Sigari ita ce sanadiyyar kashi 90 (90%) na cututtukan Sankarar hunhu mai saurin Kisa (Lung Cancer).

Kuma ita ce sanadiyyar kashi 'daya cikin uku (33%) na duk wata cutar Daji (Cancer) wacce take damun 'yan Adam.

Misali akwai Mouth Ulcer, Cadio-Vascular diseases, da sauransu.

5. Tobacco ita ce sanadiyyar cuttuka masu kama Qirjin 'Dan Adam, kuma masu saurin kisa. Irinsu:

Chronic Bronchitis.
Emphysema.
Aneurism.
Vascular Disease.
Leukemia.
Cataract.
Pneumonea.

Mata masu ciki idan suna shan Sigari akwai yiwuwar Jaririn da yake cikinsu ya kamu da cutar nan ta Asthma. Ko kuma suyi bari, ko kuma su haifi yaron acikin wani irin yanayi.

6. Sigari tana shiga hanyoyin jini, tana gurbatashi, tana toshe ƙofofin da zuciya take harba jini ajikin 'Dan Adam..

ABUBUWAN CUTARWAN DA TAKE KUNSHE DASU:

Acetone.
Acetic Acid.
Ammonia.
Arsenic: wani abu ne wanda ake hada maganin bera dashi.
Benzane.
Butane.
Cadmium : wani irin acid ne.
Carbon Monoxide.
Formaldehyde.
Hexamine.
Lead.
Napthalene.
Methanol.
NICOTINE: Gubar da ake hada maganin Qwari dashi.
TAR: abinda ake zubawa akan tituna (Kwal-ta)
TOLUENE.

Duk wadannan abubuwan akwaisu acikin taba sigari. Kuma kowannensu ko shi kadai aka bari, zai iya hallakar da 'Dan Adam.

ILLOLINTA TA FUSKAR ADDINI

Illolinta ta fuskar addini suna da yawa. Daga ciki akwai:

1. Almubazzaranci ne. Tunda batta amfanar da komai ga jikin 'Dan Adam. kuma Allah yace "Hakika Almubazzarai sun kasance 'Yan uwan Shaitan ne. Shi kuwa Shaitan ya riga ya kafurce ma Ubangijinsa".

2. Tana cutar da lafiyar masu shanta. Allah yana cewa: "Kar ku jefa Hannayenku cikin hallaka".

3. Tana cutar da wadansu: Manzon Allah (saww) ya lissafa Mai cutar da Makobcinsa acikin mutanen da ba zasu shiga Aljannah ba.


Wannan hoto da ke ƙasa misali ne na huhun wanda ba ya shan taba da wanda yake sha.

Hoto daga Dr Hinal

Wannan tunatarwa ce ga dukkan masu hankali. Ku hana kanku, ku hana 'yan uwanku da abokanku shan Sigari.

ALLAaH YA SAWAƘE!

Amin Summa Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Zauren Fiqhu

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user