Wednesday 9 January 2019

Karanta Kaji: Kuskure 3 da akai a cikin Film din RUDANI tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Rudani
Tsara Labari: Nasir S. Gwangwazo da Jamilu Ahmad Yakasai
Kamfani: Almubarak International Films Production Limited 
Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda Umarni: Ahmad A. Bifa 
Jarumai: Ali Nuhu, Jamilu Ahmad Yakasai, Ibrahim Mandawari, Aisha Aliyu Tsamiya, Rukayya Umar, Hajara Usman, Hadiza Muhammad da dai sauransu 



Sharhi: Hamza Gambo 

A farkon fim din an nuna Baba (Ibrahim Mandawari) ya shigo gidan sa iyalan sa sun tarbe shi suna yi masa murnar karin shekarar haihuwar sa. An nuna cewar yana zaune da matar sa (Hajara Usman) tare da ‘ya’yan sa Yaya Bashir (Ali Nuhu) da kanin sa Sadik (Jamilu Yakasai) wadanda suma suke tare da matayen su a cikin gidan. Duk da kasancewar shi Sadik suna samun rashin jituwa da matar sa Habiba (Aisha Aliyu Tsamiya) wadda tsananin kishin sa da take yi yasa har ta fara zargin sa akan yana bin matan banza, hakan yasa lokacin da zai tafi London taki amincewa da tafiyar sa saboda tana zargin cewa ba aiki zai tafi ba zai je ne kawai don ganawa da budurwar sa baturiya. Sun samu rashin jituwa a sanda mijin nata Sadik zai bar kasar duk da kasancewar yayi mata bayanin aikin da zai kaishi London din amma ta kasa fahimta. 

Bayan tafiyar Sadik London sai Habiba ta soma rashin lafiya, amma bayan zuwan ta asibiti sai aka tabbatar mata da cewar tana dauke da larurar cuta mai karya garkuwar jiki wato kanjamau. Jin hakan ne ya tashi hankalin Habiba ta kara tabbatar da zargin da take yiwa mijinta na cewar yana neman matan banza. Bayan ta dawo gida ta sanar da iyayen sa sai aka kira sa aka bukaci yaje asibiti acan London din don a auna jininsa don a gane ko yana dauke da cutar shima, amma sai Sadik yaki amincewa da hakan har a karshe mahaifin sa ya bukaci yabar aikin da yake ya dawo gida domin a sannan rigima ce ta afku iyayen Habiba suna neman mika maganar zuwa kotu don a bi wa ‘yar su hakkin ta. Hakan ne yasa Sadik ya dawo gida najeriya aka je wajen likita ya duba jinin sa, sai dai bisa mamaki da aka duba sai aka gane cewar babu cutar kanjamau din a jikin sa. Hakan ne ya sake haifar da hargitsi domin iyayen Habiba sun ki yarda da binciken da akayi saboda suna zargin cewa a jikin sa ne Habiba ta dauki cutar kanjamau. A karshe dai dangin Habiba suka kai Sadik asibitin da suke ganin za’a fada musu gaskiya, sai dai kuma acan din ma sakamakon iri daya ne bayanai sun tabbatar da cewar Sadik bashi da cutar kanjamau, hakan ne yasa zargin kowa ya koma kan Habiba, domin ta jima da guduwa gidan iyayen ta, acan din ne mahaifiyar ta (Hadiza Muhammad) ta rutsa ta da tambayar inda ta kwaso cutar kanjamau, sai dai kuma Habiba ta gaza bata amsa. Ana tsaka da haka ne Sadik yaje gidan su Habiba ya fada mata gaskiyar cewa baya mu’amula da matan banza kuma budurwar sa ta kasar waje sun jima da rabuwa domin saurayin ta yayi masa gargadin kada ya sake ganin su tare. Bayan Sadik ya gama bawa Habiba labari ne sai ya bukaci da tayi dai tunani don a gane inda ta samu larurar kanjamau, ya bata misalin cewar ba sai ta hanyar jima’i ake daukar cutar ba, akan iya samun ta ta hanyar yankan farce ko kitso ko wani dalili daban na haduwar jini. Jin hakan ne yasa Habiba ta bashi labarin cewa wata rana kawarta tazo gidan ta tun tana amarya ta bata shawara akan yin tsarin iyali don kada ta haihu da wuri, sai dai kuma bayan zuwan su asibitin sai likita ya tabbatar musu da cewar sirinji daya ne ya rage wanda za’a yi musu allura, sai dai ya fita ya siyo wani, amma sai duk su Habiba suka nuna sauri suke yayin da kawar ta ta bukaci cewar tunda su kawaye ne a yi musu da guda dayar kuma a fara yi mata sannan a yiwa Habiba, hakan kuwa akayi nan aka fara yi mata allurar sannan aka yiwa Habiba. Bayan Habiba ta gama ba shi labari sai Sadik yaje neman kawar Habiba a gidan ta amma sai ya samu labarin cewa ita da mijin ta sun rasu kuma ana zargin cutar kanjamau ce ta kashe su. 

Wannan dalilin ne yasa aka gane inda Habiba ta samu larurar cutar kanjamau, kuma Sadik yayi alkawarin zai kai ta London don nema mata magani kuma idan ta warke yayi alkawarin zai mayar da ita dakin sa.

 Abubuwan Birgewa

1- Labarin ya fadakar kuma ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba, sannan kuma an yi kokarin saka abubuwan da suka rike mai kallo har zuwa karshen labarin. 

2- An yi kokari sosai wajen samar da muhallin da su ka dace da labarin wato (locations)

 3- Daraktan ya yi kokari sosai wajen tafiyar da labarin ta hanyar da ta dace, haka yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman sun yi kokari musamman Habiba wato Aisha Tsamiya.

 4- Sauti ya fita radau, haka ma hoton fim din ya fita radau domin an yi kokari wajen nuna salon daukar hoton fim din.

 Kurakurai

1- An nuna cewar tun Habiba ta na amarya kawarta ta raka ta wajen yin allurar tsarin iyali (wato family planning) wanda dalilin hakan ne ya sa a ka samu matsalar da Habiba ta kamu da larurar cutar kanjamau, sai dai kuma duk da a na daukar cutar ta hanyar jima’ai kuma an nuna cewar Sadik ya na tare da matar tasa har na tsahon lokaci, amma shi bai kamu da wannan larurar ba, ya dace a nuna wa mai kallo dalilin da ya sa Sadik bai kamu da cutar ta kanjamau ba.

 2- Lokacin da Sadik ya bawa Habiba labarin budurwarsa wadda su ka yi soyayya a kasar waje, me kallo ya ga Sadik ya dauki budurwar tasa a can kasar London ya kai ta gidan wata dattijuwa wadda ya kira da Mom. Shin wace ce wannan dattijuwar wadda Sadik ya kai budurwarsa gidan ta a London? Tun da an nuna mahaifiyarsa a Najeriya (wato Hajara Usman). To, ya dace a yiwa me kallo bayanin matsayin dattijuwar nan a wajen sa ko da ta hanyar nuna cewar ‘yar uwar mahaifin sa ko mahaifiyar sa ce

 3- Shin ina mahaifin Habiba? Har fim din ya kare mai kallo bai gan shi ba kuma ko a baki ba a ambace shi ba, duk da kasancewar akwai matsaloli da yawa na fannin auren Habiba da suka taso wanda ya kamata ace an ga mahaifin ta a cikin maganar, amma ba a gan shi ba sai wani Barrister da aka nuna a matsayin kawun su. Idan ma mutuwa mahaifin ta yayi to ya dace ko a baki ne a fada. 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa. An nuna illar bin shawarar kawaye, sannan kuma an yi kokari wajen isar da wani muhimmin sako wanda al’umma zasu amfana da shi, domin fim din ya koyar da wani darasi wanda jama’a zasu kiyaye rayuwar su da lafiyarsu. 

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: LEADERSHIP A YAU



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user