Thursday 25 July 2019

Karanta Kurakurai 4 da akai a cikin Film din NAMIJIN KISHI tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Namijin Kishi.
Tsara labari: Yakubu M. Kumo.
Kamfani: Kumo Production.
Daukar Nauyi: Yakubu M. Kumo.
Shiryawa: Sale Yaro.
Bada Umarni: Ali Gumzak Sak.

Namijin Kishi


Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Ali Nuhu, Sadik Sani Sadik, Hafsat Idris, Garzali Miko, Shehu Hassan Kano, Alhassan Kwalli, Fati Umar, Hajiya Sadiya, Alhaji Dauda, da sauransu.

Fim din “Namijin Kishi” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani bawan Allah mai Suna Habibu (Sadik Sani Sadik). Habibu wani mutum ne mai fama da tsananin kishi a kan matarsa wato Fa’iza (Hafsat Idris). Kishinsa ya sa ko unguwa ba ya bari ta fita, ko da gidansu za ta je ba ya bari ta je ita kadai, sai dai ya je ya kai ta ya zauna ya jira ta. Haka Fa’iza ta ringa rayuwa cikin matsi sakamakon tsananin kishin mijinta. Hatta ‘yan uwanta na jini maza ma idan su ka je gidanta sai ya nuna bacin ransa a kan hakan. A sakamakon hakan ne, ‘yan uwan nata ma duka su ka kauracewa zuwa gidan nata.

Zaman Habib da Fa’iza bai wuce wata hudu ba, amma saboda tsabar tsananin kishinsa har ya yi mata saki har guda biyu a kan dalilan da ba su taka kara sun karya ba. Hakan ya sa saura igiyar aurensa daya ce ta rage a kan Fa’iza. Mahaifiyar Habib da kawunsa su na masa fada a kan ya kiyaye a kan maganar Fa’iza, saboda sun tabbata idan har bai daina wannan mahaukacin kishin nasa ba to tabbas zai karasa wannan saki dayan da ya rage a tsakaninsu.

Wata rana mahaifin Fa’iza wato Alhaji (Shehu Hassan Kano) ya kawo mata ziyara, suna cikin hira sai ga Habibu ya dawo daga aiki kawai da ya shigo ya jiyo muryar namiji a cikin falon gidanshi, kawai sai ya dakko katako ya nufo falon da gudu. Ya na shigowa a fusace kawai sai ya ga ashe Alhaji ne, nan dai ya yi ta bawa Alhaji hakuri yana cewa a yi masa afuwa kuskure ne wallahi ai bai san shi bane.

Ana nan dai watarana Babar Fa’iza ba ta da lafiya, sai Fa’iza ta nemi izinin Habib a kan tana so ta je, sai ya ce mata ta bari ya dawo sai ya kaita. Karshe dai da a ka kara kiran ta a ka sanar da ita cewa jikin ya yi muni, shi ne kawai ta kirawo Habib ta ke fada masa cewa za ta fita ta hau babur din haya ta tafi saboda jikin Hajiyar ya yi tsanani. Sai ya ce mata kada ta hau babur ta jira shi, sai ta fita ta hau babur kawai ta kyale shi ta yi tafiyarta . A haka kuwa a ka samu tsautsayi sai ta yi hatsari a hanya. To a lokacin shi ma Habib ya yanke shawarar cewa kawai zai dawo ya dauke ta ya kai ta gidan da kansa.

A hanyar tahowar tasa ce, kawai sai ya ga taron mutane a wani guri, yana lekowa kawai sai ya ga Fa’iza a zaune cikin jini a tsakiyar maza. Shi ne a ke bashi labarin ai hatsari su ka yi a hakan ma sai da wani ya dakko ta ya dawo da ita gefen hanya da tuni mota ta take ta. Ai kuwa yan jin cewa namiji ne ya dakko ta ya kawo ta gefen hanya, kawai sai Habib ya fadi a sume, daga nan a ka kwashe su sai a asibiti.

Habibu yana farkawa ne sai ya nufo inda Fa’iza take, isowarsa ke da wuya kawai, sai ya tashe ta ya rufe ta da fada yana zagin ta yana cewa ta ci amanarsa. Kawai Habib yana bude baki sai yace ya saki Fa’iza. Yana sakinta sai ga Alhaji ya shigo dakin, sai Fa’iza take fada masa ai Habib ya sake ta. A nan ne fa Habib ya fara cewa shi fa da wasa yake ba sakin ta ya yi ba. Shi ne Alhaji ya fara fada masa magana yana cewa to ko kai mahaukaci ne Fa’iza ta kwace maka kenan har abada.

A haka dai Habib ya yi ta rayuwa cikin kunci a sakamakon sakin Fa’iza. Ya koma tamkar mahaukaci, kullum cewa ya ke shi fa sai Fa’iza ta dawo gidansa wai shi ai ba sakin ta ya yi ba. Haka ya yi ta yawon bin malamai wai yana so a ba shi wata fatawar da za ta iya saka matarsa ta dawo izuwa gareshi. Amma ko’ina ya je ana fada masa cewa matarsa fa ba za ta dawo gareshi ba har sai wani ya aure ta sun rabu, to sannan ne za ta iya dawowa izuwa gareshi.

A karshe dai haka dole Habib ya hakura da Fa’iza. Ta yi aure ta auri Ahmad (Ali Nuhu), bayan ‘yan sanda sun kama Habib sakamakon naushin da ya yi wa Ahmad. A karshe shi ma Habib dole ya yi hakuri da Fa’iza, ya je ya sake aure shi ma. Bayan ya dawo cikin hankalinsa ne, sai a ka maida shi gurun aikinsa bayan dakatarwar da a ka yi masa a baya. Kuma sannan ya ci-gaba da rayuwarsa kamar yadda ya kamata.

Namijin Kishi


ABUBUWAN YABAWA

1. Sunan Fim din ya dace da labarin duba da irin namijin kishin da Habib ya ke nunawa a cikin fim din.

2. Fim din ya samu aiki mai kyau, saboda ba a samu matsaloli masu yawa a cikinsa ba.

3. Labarin ya samu nasarar rike mai kallo tun daga farko har karshe.

4. Labarin mikakken labari ne, bai karye ba tun daga farko har karshe.

5. Jaruman cikin fim din sun taka rawa mai kyau a ciki, musamman Habib da Fa’iza sun taka rawa sosai a irin fitowar da su ka fito a ciki.

6. An nuna tasirin soyayya ta gaskiya, domin duk da abinda Habib ya ke yi wa Faiza tana son shi duk da haka, saboda ta san soyayya ce ta saka yake yin wannan tsananin kishin a kanta.

7. Nadamar da Habib ya yi a karshe, zai zama izina ga masu irin tsananin kishi irin na shi.

Namijin Kishi


KURAKURAI

1. Kalaman da Mu’azzam kanin Fa’iza ya zo yana fadawa Mamansu a gida bayan ya dawo daga gidan Fa’iza a lokacin da Habib ya kama yi masa fada saboda ya kwanta a kan kayanta, sam ba su dace da maganganu da ya kamat da ya yi a gaban mahaifiyarsa ba.

2. A lokacin da Habib ya kai Fa’iza asbiti har ya ke cewa ba za a yi mata (scanning)ba, idan har babu likita mace a asibitin, kalaman da ya ringa fadawa likitan a lokacin da su ke asibitin sam basu da ce a ringa fadar su a wannan gurun ba.

3. Ya kamata a nuna Ahmad da Fa’iza a gidansu bayan sun yi aure koda sau daya ne.

4. Ya kamata ace an nuna lokacin da Habib ya yi wa Fa’iza saki biyun farko bayan aurensu, domin masu kallo su kara fahimtar labarin sosai.

KARKAREWA

Fim din “Namijin Kishi” fim ne da ya bayyana irin tsananin kishi wanda Habib ya ke yi wa matarsa Fa’iza, sai dai kishin nashi ya wuce ka’ida, wanda hakan ne ma ya jawo masa nadama a karshe. Tabbas abu ne mai kyau ga dukkan wanda ya san mai yake da ya ringa nuna kishi ga matarsa. Sai dai kodayashe ana so kada kishin ya wuce ka’ida. A karshe dai an ga yadda wannan zazzafan kishin na Habib ya kai shi ga yi wa Fa’iza saki har guda uku, wanda hakan ya tilasta masa rabuwa da ita duk da irin kaunar da yake mata. Sannan yana da kyau masu bada umarni a fim su ringa kula da irin kalaman da ya kamata su ringa amfani da su a cikin fina-finansu, saboda ya zama ya zo dai-dai da tsari da kuma ka’ida.

MUKALOLI MASU ALAKA:

Kuskure 6 da akai a cikin Film din TAKADDAMA tare da Sharhin Fim din

Kuskure 4 da akai a cikin Film din SALMA BANKWANA tare da Sharhin Fim din

Fitattun Fina-Finan Hausa Guda 10 Mafi Shahara a 2018

Kuskure 6 da akai a cikin Film din DAN KUKA A BIRNI tare da Sharhin Fim din

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: Leadership Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user