Friday 4 January 2019

Karanta Kaji: Fitattun Fina-Finan Hausa Guda 10 Mafi Shahara a 2018

Tura Wannan Zuwa Ga
Allah Ya kara kawo masana'antar Kannywood zuwa karshen wannan shekara.Ba ma wannan kadai ba, masana'antar ta samu ci gaba da har ta yi fina-finai iri-iri, wadanda yawanci na barkwanci da soyayya ne, da kuma almara, wadanda kalilan ne.
Daga ciki akwai fim din ban-dariya na Adam A. Zango, wato Dan Kuka a Birni da fim din Ali Nuhu da ya yi shi shekara 18 baya kuma ya sake yinsa yanzu, Mujadala, da dai sauransu.
Kabiru Jammaje, wanda shi ne musabbabin farfadowar sashen Ingilishi a Kannywood, ya sake daukar nauyin wani kasaitaccen fim din sarauta mai suna In Search of the King.
Da alamun fim din Nafisa Abdullahi, Yaki a Soyayya, ma za a ji dadinsa, saboda haka shekarar ta 2018 ta kayatar.
Wadannan fina-finan da aka jero a kasa su ne suka fi shahara da fice a wannan shekarar, wacce ta zo dab da babban zaben Najeriya wanda za a yi farkon shekara mai zuwa.
Ga shi siyasa ta kunno kai cikin masana'antar ta Kannywood, har ma ake ganin ta janyo rarrabuwar kawuna gami da barazanar kara raba kan mambobin masana'antar da ba a jima da sasanta su ba - kodayake, wannan ba shi ne maudu'inmu yanzu ba.
Fina-finan ba bisa daraja aka jera su ba:

1. Ruwan Dare

Ruwan DareHakkin mallakar hotoYASIN AUWAL
Image captionRuwan Dare ne ya yi fice a cikin fina-finan Kannywood na 2018

Fim din, wanda daraktansa shi ne Yaseen Auwal kuma ake ganin yana daya daga cikin fina-finan Kannywood da suka fi dacewa da yanayin da ake yanzu, yana shagube ne cikin salon tsoratarwa ga matasan da suka gama jami'a kuma suke raina duk wani aikin da ba na ofishi ba.
Aminu Sharif, wato Momoh, da Sadiq Sani Sadiq wasu mutane ne da suke son yin kudi ko ta wane hali kuma masu tsananin buri ne, wadanda sun gama digirinsu na farko a fannin Akanta da Tattalin Arziki.
Abokinsu kuwa, wanda shi ma ya gama jami'ar, Baballe Hayatu, ba irin salonsu ya dauko ba.
Saboda haka, daga karshe sai ya samu nasara.
Su kuma wadancan biyu daga karshe sun koyi darasi sannan suka yi nadama.
Fim din ya yi matukar haduwa saboda yadda jigonsa yake da alaka da wannan zamanin.
Kuma 'yan wasan, wadanda aka ambaci sunayensu a sama da ma wadanda ba a ambata ba, sun yi kokari sosai.
Za a iya kau da kai daga 'yan kura-kuran cikin fim din - irin su ambatar Yugoslavia a matsayin kasa, kura-kuran nahawun Turancin Ingilishi, da sauransu.

2. Rabi'atu

Maryam Yahaya a fim din Rabia'atuHakkin mallakar hotoGOOGLE
Image captionMaryam Yahaya a fim din Rabia'atu

Rabi'atu, wanda Aminu S. Bono ya yi darakta, an shirya shi ne kwata-kwata a gidaje guda uku; kuma yana nuna irin hadarin da 'yar aikin gida ke shiga a gidan da take aiki.
Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin ita ce Rabi'atu, takan yi duk aikace-aikacen babban gidan Alhaji Rabiu Rikadawa, yayin da matarsa, Hadiza Muhammad, kuwa ke zuwa wajen aiki; 'ya'yansa hudu kuma makaranta suke zuwa.
Rabi'atu dai yarinya ce mai yarinta kuma kamammiya, wacce gidansu ba masu karfi ba ne.
Saboda haka kowa a cikin gidan da take aiki sonta yake yi, har ma manyan 'ya'yan gidan guda biyu suke takara da juna wajen samun karbuwar soyayya a wajenta.
Sai dai ba ta amince da su ba, tana mai jaddada musu cewa sun wuce ajinta.
Sai dai duk da haka ba wanda ya hakura a cikinsu.
Ana haka, kwatsam sai wata rana Alhaji ya zo gidan ya same ta ita kadai har ya yi lalata da ita.
Daga bisani, sai matar Alhaji ta gano Rabi'atu fa ta samu juna-biyu sakamakon lalata da Alhaji ya yi da ita.
Aka yi ta gumurzu dai har zuwa karshe.
Fim din bai ci kudi ba, amma ya yi matukar dacewa da yanayin da ake ciki yanzu.
Sannan, labarin ya yi kama da zahiri kuma daraktan da mataimakansa da kuma 'yan wasan, wadanda ba shahararru ba ne, sun yi aiki da basira sosai.
Babu rawa da waka a ciki.
Ba ma wannan ba, karshen fim din ya kayatar.

3. Fuska Biyu

Fim din Fuska BiyuHakkin mallakar hotoADAM ZANGO
Image captionFim din Fuska Biyu

Fuska Biyu yana nusarwa ne game da yadda wasu iyaye ke saurin aurar da 'ya'yayensu mata ba tare da bincike kan mazajen da za su aurar wa ba.
Fim din yana ba da labari ne na wani madugun masu garkuwa da mutane, Adam A. Zango, wanda da rana yake bayyana a matsayin mai sayar da kifi.
Amal, wata kamilalliyar yarinya, wacce 'yan uwanta ba masu karfi ba ne, takan sayar da abinci a gefen teburin da Zango ke ikirarin yana sayar da kifi.
A haka sai suka fara soyayya.
Irin abin duniya da yake ba ta ya sa mahaifiyarta take jin akwai lauje cikin nadi.
Amma mahaifinta kuma ya dage cewa 'yarsa fa ta samu mijin aure.
Sai kuma da lokaci ya kure sannan mahaifin ya fahimci kuskurensa.
Fim din akwai jan hankali cikinsa.
Yana da amfani sosai a kalle shi.

4.Risala

Fim din RisalaHakkin mallakar hotoABUBAKAR S SHEHU
Image captionFim din Risala

Sunan wannan fim, Risala, wata kalma ce ta Larabci, wacce ke nufin "sako".
Risala, wanda Abubakar S. Shehu ya yi darakta, siffofin zamanin baya yake da su.
Gogaggen tauraron nan, Sadiq S. Sadiq (Zakariyya), ya yi wata tafiya da nufin neman mutumin da ya yi wa ba-daidai ba don neman afuwa.
Tafiya ce mai cike da karaskiya, masifu da abubuwan al'ajabi.
Abin bai tsaya a haka ba - sai da ya sake haduwa da wata jarrabawa a wani gari da ake kira Baihan, garin da mutumin yake.
Wannan mutumin ya yarda zai masa afuwa amma sai in ya amince zai auri 'yarsa, wacce, a cewarsa, ta fi kowa muni a garin kuma musaka ce.
Sai Zakariyya ya amince amma ba cikin son ransa ba.
Ashe dai yarinyar nan ba haka take ba; hasali ma, yarinyar matukar kyau ne da ita.
Bayan 'yan kura-kurai da fim din ke da su kamar rashin takaita darussa da yake koyarwa, da kuma ci-da-karfi wajen aiwatar da wasu abubuwa, fim din ya dauko tarihin haihuwar shahararren malamin addinin Islaman nan ne, Abu Hanifa.
Kodayake yawancin fina-finan Kannywood kwaikwayo su ake yi daga wani waje.
Baya ga haka, sautin shirin ya dauku.

5. Hakki

Fim din HakkiHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/HAMISU IYANTAMA
Image captionFim din Hakki

Kamar yadda ake fada, tsohuwar zuma da ita ake magani.
Sanannen kamfanin shirya fina-finai, Iyantama, shi ya yi fim din Hakki yayin da Hafizu Bello, kwararre a harkar, ya yi darakta.
Labari ne kan wani mai suna Jabir, wanda jajirtaccen ma'aikaci ne kuma dan gwagwarmaya a wani kamfanin fata.
Ba a san shi da karba ko ba da cin hanci ba.
Ba tare da nuna fargaba ba, yake yaki da rashin adalci da kuma rashin kyautawar da hukumar kamfanin ke yi wa ma'aikata.
A bangare guda kuma, akwai labarin wani gungun 'yan mata da suke janyo mazaje cikin wani loko domin abokansu na aikata miyagun laifuka su samu damar fasowa don yi musu fashi.
Har yanzu fim din a sinima kawai ake samunsa.
Ya kuma samu damar shiga sahun fina-finai don samun lambar yabo.
Ya samu karbuwa ne saboda irin sakon da yake isarwa, wanda gaba daya ya sha bamban da irin fina-finan Kannywood na soyayya.
Kuma ya dace da zamanin da ake ciki musamman yayin da kungiyar kwadago ke ta fama da gwamnati wajen ganin an samu karin albashi.

6. Mariya

Fim din MariyaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI NUHU
Image captionFim din Mariya

Fim din Mariya, wanda Ali Nuhu ne daraktansa, yana nuni ne kan yadda lamarin auren 'ya mace yake a kasar Hausa.
Labari ne na Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin Mariya kuma ake tuhumarta da kashe mijinta, Baba Karkuzu, da abokinsa, Musa Maisana'a, ta hanyar saka musu guba.
Kafin a yi mata auren dole, tare da Abdullahi (Umar M. Sharif) take soyayya.
Ga shi tana da buri na karantar aikin likita.
Daga bisani sai aka gano ashe ba ita ta yi kisan ba.
Babban kuskure a cikin fim din shi ne rashin fito da takamammun al'amura fili.
Duk da haka, fim din ya dace da zamanin da ake ciki yanzu.
'Yan wasa ma sun yi kokari.
Maryam Yahaya, kamar yadda ta saba, ta yi abin a-zo-a-gani.
Wadanda suka fito hatsabibai ma kamar su Garzali Miko, Baba Kurzuku, da Alhassan Kwalle sun taka rawar gani.
Tacewa da haskakawa da kuma kwalliya a fim din suna da jan hankali.

7. Larai Ko Jummai

Maryam Yahaya da Amal Umar a fim din Larai ko JummaiHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/SADIQ MAFIA
Image captionMaryam Yahaya da Amal Umar a fim din Larai ko Jummai

Rikici tsakanin kishiyoyi ba bakon maudu'i ba ne a Kannywood yayin da nuna fada kan 'ya'yayen kishiyoyin kuwa abu ne bako.
Jummai (Amal Umar) da Larai (Maryam Yahaya) 'yan uba ne.
Yayin da mahaifiyar Jummai (Ladidi Fagge) masifaffiya ce, ta Larai kuwa ba haka take ba: shiru-shiru ce.
Mijinsu (wato Bashir Nayaya) yana ta hakuri da su dai.
Kamar yadda ya saba faruwa a kauyuka, kawai sai 'ya'yan baffanunsu (Abdul M. Sharif da Garzali Miko) suka tsunduma cikin soyayya da wadannan 'ya'yan Bashir Nayayan.
Da yake Garzali attajiri ne saboda a birni yake aiki, Ladidi sai da ta yi kutun-kutun ya auri 'yarta.
Kwatsam sai abubuwa suka sauya: Abdul ya zo ya fi Garzali kudi bayan ya bi shi sun tafi birni tare.
Sadiq N. Mafia ne daraktan fim din kuma shi wannan fim ya kece sauran fina-finai saboda dalilai da dama, duk da bai watsu kamar sauran fina-finai ba saboda ba a kashe masa kudi sosai ba.
Fim ne da ke matukar nuna zahiri, wanda za mu iya cewa shi ne zakara wajen nuna ainihin rayuwar Hausawa a kauye da kuma rashin jituwa kan "abin da bai taka kara ya karya ba" da ke tsakanin kishiyoyi a gidan mijinsu.

8. Taqaddama

Fim din TakaddamaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI GUMZAK
Image captionFim din Takaddama

Fim ne da Ali Gumzak ne daraktansa kuma labari ne na "abin da ya taba faruwa da gaske" na wani sangartaccen dan wani shahararren mai kudi, Hassanu (Aminu Sharif).
Duk lokacin da ya yi laifi aka kulle shi, attajirin mahaifinsa, Alhaji Bilya (Ali Nuhu), wanda yake kut-da-kut da 'yan siyasa, kan ba da kudi domin a sake shi.
Ga shi mahaifin ba ya karbar shawara ko uzurin kowa.
Sai dai Hassanu da mahaifin nasa karshensu bai yi kyau ba bayan ya kashe abokinsa, Salisu, a lokacin da suka yi rigima a wani gidan rawa.
Hassanu ya ja kunne wa dayan abokinsu, Nura (Abba Almustapha), wanda aka yi kisan a gabansa, cewa kar ya fada wa kowa shi ma zai kashe shi.
Sai dai Nura bai iya barin wannan barazana a zuciyarsa ba, wanda hakan shi ya tona asirin wanda ya yi kisar, wato Hassanu.
Fim din ya yi kokari wajen nuno yanayin rayuwar manyan Najeriya.
'Yan wasan sun yi kokari.
Shirin Ya koyar da darasi sosai, duk da cewa "kayatarwa" da "koyar da darasi" a lokaci guda abu ne da Kannywood ke fama da shi.

9. Kawayen Amarya

Fim din Kawayen AmaryaHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/YAKUBU MOHAMMED
Image captionFim din Kawayen Amarya

Fim ne da 2 Effect Empire wanda kuma Yakubu Muhammad ya ba da umarni.
Kuma fim ne da 2 Effect din suka saba yin irinsa, wato mai kyale-kyale da kuma tattaro manyan taurari.
Labari ne na wani mai kudi, Alhaji Abdulsalam, da ke da mata uku.
Bai taba haihuwa ba.
Saboda fargabar haka sai ya dauko wani yaro ya mayar da shi a matsayin dansa.
Daga baya ma sai matan nasa suka samu juna biyu suka haihu.
Uwar gidansa (Saratu Gidado, wato Daso) kullum alfaharinta shi ne "ai mahaifinta ne sanadin kudin Alhaji", saboda haka, ya kamata komai nata da na danta ya zama daban.
'Ya'yan Alhaji (wato Ali Nuhu da Sani Danja da kuma Yakubu Muhammad) a rana guda suka yi aure.
Kamar yadda sunan fim din yake, haka fim din ma yake tattare da cakwakiya da kaceniya a yayi da bayan bikin auren, wanda yawancin kwayayen amaren ke janyowa.
Duk da fim din na ban-dariya ne, amma yana dauke da darrusa.
Babban matsalarsa ita ce "sautin ADR", wanda shi ne sake nadar murya don a saka wa fim kafin watsa shi.
Maganganun ba sa tafiya daidai da motsin lebe a fim din.
Haka dai babu abin da aka yi wa Daso bayan ta kashe mutane har biyu.
Fim ne da zai kayatar sosai.

10. Li'ani

Fim din Li'aniHakkin mallakar hotoINSTAGRAM/ALI GUMZAK
Image captionFim din Li'ani

Ali Gumzak ne daraktan wannan fim din.
Labari ne na wani mai suna Alhaji Sunusi (Rabiu Rikadawa), wanda sam ya ki yarda juna-biyun da matarsa ke da shi nasa ne.
Hakan ya kai ga sun je gaban alkali sun yi rantsuwa (Li'an).
Dan da ta haifa, wanda shi ne Ali Nuhu, a wajenta da mijin da ta aura ya girma.
Sai dai daga baya alhaki ya bi Alhaji Sunusi, wanda yake ganin kamar sakayya ce daga Ubangiji sakamakon abin da ya yi wa wannan matar tasa.
Mata takwas ya aura, yayin da daya daga cikinsu ta taba yunkurin kashe shi, amma hakan bai yiwu ba.
Sai da lokaci ya kure kafin ya gane kuskurensa.
Fim din ya hadu saboda irin maudu'in da ke ciki, wanda ba a saba yin fim a kansa ba.
Masu shirya fim din da 'yan wasan duk sun yi kokari sosai wajen saurin fito da al'amura fili.
Babu waka ko rawa a ciki.
Akwai wasu 'yan al'amura na daban wadanda su ma sun taimaka wajen isar da ainihin sakon fim din.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user