Wednesday 24 July 2019

KARANTA LABARIN GOJE MAI DAWA KASHI NA DAYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Goje, mai dawa ɗan Makau, shahararren mafarauci ne da sunansa ya yi tambari a ƙauyen Bugabiri da kewayensa. Idan ya tashi zuwa farauta, yakan yi shirin da yakan ba wa kowa tsoro, domin kuwa yakan fita daga siffar mutane ya koma tamkar wani ifiritu. Yakan sha shuni, ya shige agalemin kura, ya kuma ɗaura warki a ƙugunsa, sannan ya yi ɗamara da karhu inda yakan soke dagage. Yakan cika damuttsansa da guraye, ya kuma ɗaura akayau a ƙafarsa, bayan ya sanya ɓantale-tsiya-na-shirya.


LABARIN GOJE MAI DAWA 


MarubuciBukar Mada

+2348021218337

Daga nan sai ya rataya kutubani a kafaɗarsa ta dama, ya kuma rataya angara da yakan zuba murje a kafaɗarsa ta hagu tare da salka. Sai kuma ya riƙi baka a hannunsa na dama, wani lokaci yakan haɗa da gyanɗamar da yakan ɗura gwadara ko kwaɗagyas. A hannunsa na hagu kuma zai riƙe raba-ni-da-ɓaidu, wani lokaci ma yakan rataya wargaji

Idan ya gama shirinsa tsaf, sai ya fita daga kudandaninsa, ya yi wa gida adabo. Ya ratsa ta cikin gonaki, waɗanda akasarinsu sabra ne da kuma waɗanda aka yi wa gafara-babe, musamman lokacin da aka yi ruwan kwazari. Daga nan sai ya faɗa cikin lababe har zuwa ga burtalai, yana tsallake kwazazzabai da ƙoramu, inda daga ƙarshe zai kutsa kai cikin ƙungurmin daji. Wanda duk ya gan shi a wannan lokaci sai ya saɓi laya wani maridi ne ko askar da zai iya mai da linzami ɗari baya.

Wata rana Goje ya kutsa kai cikin dokar daji, ya yi ta yawo har rana ta faɗi bai kamo ko fara ba, ashe duk namun dajin sun tsorata da shi sun bar wajen. Ya yi niyyar komawa gida sai makuwa ta kama shi, ya rasa gabas balle yamma. Ya yi ta waɗari tsakanin itatuwa. Da ya ga dare ya soma yi kuma bai gane inda yake ba, sai ya yi shawarar ya kwana nan, zuwa da safe idan makuwar ta sake shi ya koma gida.

Har ya share wuri a ƙasa zai kwanta, sai kuma wani tunani ya zo masa, kada ya kwanta ya yi baya ba zani, wani naman daji ya auka masa yana barci, don haka sai ya sami bishiyar marke ya haye can ƙololuwarta, ya sami wani babban reshe da ya yi gwafa ya kwanta yana karanta wasiƙar jaki.

Yana nan kwance ya yi likimo, yana tsumayen zuwan sarkin ɓarayi, sai ya hango wani ɗan haske can da nisa kamar tauraron gamzaki. Nan da nan ya tashi zaune, ya ƙura wa wajen ido ya ce a ransa, "lalle wancan abu da nake hange haske ne. Idan kuwa fitila ce ke haske, ba a rasa mutum a wurin ba." Sai ya yanke shawarar ya sauka ya nufi inda ya hango wutar nan, idan gida ne, sai ya roƙi masu gidan wajen bacci kafin gari ya waye.

Ya nufi inda hasken nan ke fitowa gadan-gadan, ya ɗana kibiyarsa don shirin ko-ta-kwana. Da ya iso inda hasken sai ya tarar da wata 'yar bukka da aka yi da tsabgogi aka tamke da tsawo, aka baibaye da ciyawa, aka yi rufinta da ɗan boto. Daga cikin bukkar ne hasken fitila ke ratsowa ta tsakanin tsabgogin nan.

Goje ya matsa kusa da ƙofar wacce aka rufe da asabari, ya yi sallama. Sai ya ga wani ɗan tsoho tukuf ya leƙo da kansa babu ko hula, gashin nan fari fat kamar auduga. Da ya ga Goje a bakin ƙofa, sai ya buɗe ya fito yana dogara sanda, jikinsa duk ya yankwane, yana sanye da wata tsohuwar riga da aka yi wa face-face a jikinta. Ya dubi Goje da karikitan da ke jikinsa ya ce, "wanene kai? Kuma me ya kawo ka nan?"

Goje ya rusuna cikin ladabi ya ce, "ni mafarauci ne, na zo yawon harbi ne makuwa ta kama ni har dare ya yi mini ina ta yawo cikin wannan daji, na rasa gabas na rasa yamma, har Allah ya kawo ni nan inda kake. Idan ka yarda ina so in kwana wurinka, da safe idan makuwar ta sake ni, in kama gabana."

Tsoho ya harari Goje ya ce, "kai, ni ba na ba mafarauci wurin kwana, kama gabanka ka san inda dare ya yi maka." Sai ya juya zai koma cikin bukkarsa.

Da Goje ya ga haka sai ya yi wuf ya kama haɓar rigar ɗan tsoho ya riƙe, ya durƙusa ƙasa yana ta roƙonsa. Tausayi ya kama ɗan tsohon nan, sai ya riƙi hannun Goje ya shigar da shi cikin bukkarsa. Ya kawo fura cikin gora ya ba shi ya sha, ya bulbulo masa ruwa daga tulu, ya ba shi ya kora, sa'annan ya nuna masa wata tsohuwar karauni, ya ce, "ga wuri nan kwanta idan kana iyawa."

Goje ya yi wa tsohon nan godiya, ya cire kayan farautarsa ya ajiye gefe, ya mimmiƙe bisa tabarma, ba a jima ba barci mai nauyi ya ɗauke shi har da minshari, da ma a gajiye yake liƙis, ga kuma furar da ya sha. Ba shi ya farka ba sai da gari ya waye. Yana buɗe ido sai ya ji bukkar da yake ciki tana girgiza kamar za ta rushe, ya yi zumbur ya miƙe zaune, ya duba ko'ina cikin bukkar bai ga tsohon nan ba. Sai wani irin ruri da hayaniya da hargowa yake ji a bayan bukkar. Ya ridi bakansa ya yi waje, ya ga abin da ke faruwa.

Ko da ya fito bakin ƙofar bukka, sai ya ga wani baƙin bijimin sa ne da wata kyakywar ɓauna ke tankiya tsakaninsu. Kowane sai ya ja da baya, sai ya runtumo da gudu ya haɗu da abokin faɗansa a kaura da ƙahonni. Guje-guje da tirjiyar da dabbobin nan ke yi, ya sa ƙasar wurin ta riƙa girgiza kamar za ta tsage, kukan da suke yi kuwa duk ya cika dajin ko'ina, kowace dabba sai ƙoƙari take ta ga ta soke abokiyar gabarta da ƙaho. Goje ya yi tsaye yana kallon ikon Allah, ya rasa abin yi.

Tsawon lokaci dabbobin biyu na karabkiya, babu wacce ta yi galaba a kan 'yar uwarta, can sai Allah ya ba ɓaunar sa'a, ta kuwa tsire bijimin nan da ƙahonta mai tsini, ta ɗaga shi sama ta yarɓar gefe guda. Nan take ya faɗi yana shure-shure, hanji waje. Ba a jima ba ya shure.

Goje na tsaye dai yana kallon ikon Allah, ba ya da sanannen ciki, sai ya ga ɓaunar nan ta taso masa, kafin ya ce zai ɗana bakan da ke hannunsa har ta runtume shi da ƙahonninta, ta sheƙa da gudu cikin daji da shi. Shi kuwa sai ya watsar da bakan, ya maƙalewa ƙahonnin don kada ya faɗi. Ɓaunar nan ta yi ta gudu da shi babu tsayawa, tana tsallake kwarurruka da tuddai, tana ratsa ciyayi da ƙayoyi, tana tsallake kududdufai da ƙoramu. Goje kuwa tun yana iya salati har ya rufe idonsa, ya ba mutuwa amana. Shi dai jin sa kawai yake yana keta iska, kamar ɗan tsakon da shaho ya sura.

Bayan ɓaunar nan ta yi gudu mai nisa da Goje, sai ta kawo shi gindin wani dogon dutse ta ajiye shi a hankali. Goje ya buɗe idonsa ya miƙe tsaye yana duban inda yake, sai ya ga dutse gingirim gabansa. Ya ga ɓaunar nan ta nufi wani kogo a jikin dutsen, ta ɗaga kai sama ta yi kuka mai ƙarfi, har sai da ƙasa ta girgiza. Ta tunkuyi dutsen da ya rufe ƙofar kogon da  ƙahonninta, sai ga  ƙofa ta buɗe. Wani hayaƙi da tartsatsin wuta ya fito daga cikin kogon nan, har sai da ya sa ɓaunar ta ja da baya.

Za mu ci gaba.

Ana cikin rubuta wannan labari yanzu haka. Ya kuke ganin kamun ludayinsa? An dauki hanyar rubuta labari mai dadi ko akwai abin da ya kamata a gyara?

Shawararku ake nema.

Me ne ne ma'anar waɗannan kalmomi kamar yadda suka zo a cikin labarin?

1. Ifiritu
2. Shuni
3. Agalemi
4. Warki
5. Karhu
6. Dagage
7. Damuttsa
8. Guraye
9. Akayau
10. Ɓantale-tsiya-na-shirya
11. Kutubani
12. Angara
13. Murje
14. Salka
15. Gyanɗama
16. Gwadara
17. Kwaɗagyas
18. Bar-ni-da-ɓaidu
19. Wargaji
20. Kudandani
21. Sabra
22. Gafara-babe
23. Ruwan kwazari
24. Lababe
25. Burtalai
26. Kwazazzabai
27. Ƙoramu
28. Saɓi laya
29. Maridi
30. Askar
31. Mai da linzami baya

Aika shawarar ka a email din mu Muryarhausa24@gmail.com ko a Whatsapp +234 903 166 2096

MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN FADAR BEGE

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BAShafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user