Friday 14 June 2019

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

Tura Wannan Zuwa Ga
Arewacin Najeriya yanki ne da Allah ya albarkaceshi da ni'imomi masu yawan gaske, kama daga kan muhimman mutane, masana'antu, ilmi, kayayyakin more rayuwa da makamantansu.


Arewacin  Kasar NigeriaMarubuci: Abba Ahmad Gwammaja


Yankin dai ya fara ginuwa ne tun a karni na 11 (11th Century), lokacin da yankin Borno ya fara ginuwa a matsayin daular musulunci, kafin daga bisani cikin karni na 15, inda jahohin Hausa suka kasance a matsayin jihar Musulunci.


Wannan ne yasa Shehu Usman Dan Fodio ya fara jihadi, tare da kafa tutar Musulunci a cikin karni na 19.

Hakan ce tasa yankin na Arewa ya fara kafuwa, tare da samun ci gaba a 6angarorin ilmin addini da suttura (tufafi), tare da tsarin shugabanci. Inda har takai ana yin rubutun Hausa da haruffan Larabci (Ajami).


Ana tsaka da wannan yanayi ne a Arewa, su kuma Kudancin kasar suka fara sanin su waye su, inda a wajen tsakiyar karni na 19 zuwa karshensa, masu da'awar addinin kirista suka samu 6ulla a yankin (Christian Missionaries), wanda hakan ce ta saka Shehu Usman Dan Fodio ya daura damarar jihadi, wanda yakai ga yakar yankin Yarabawa, wanda hakan ce ta saka yankin na Yarabawa suka fara sanin kansu ta hanyar kar6ar Musulunci, da kuma kar6ar tsarukan da addinin yazo dashi.


Ana tsaka da wannan yanayi ne kuma, dai-dai lokacin da Arewan taci gaba sosai, sai kuma turawan mulkin mallaka suka fara kafa sansaninsu a wani yanki na jihar Legas, cikin shekarar 1850, kafin daga bisani tsakanin shekarun 1880-1905 su mamaye yankin kudu gaba daya, wanda hakan ce ta basu damar karasowa Arewa a cikin shekarar 1903, amma sai sukar tarar damu a tsaftace, da ilminmu, da suturarmu, ga kuma masana'antu da kamfanoninmu na gargajiya, sannan suka tarar da yankin cikin tsari da kamala, sannan muna noma, kiwo da kuma sana'o'inmu na gargajiya, sa6anin yadda suka samu Kudu ko sutura basu da ita, sai dai ganye suke daurawa.
Kuma duk ilmin bokon da suka taho mana dashi, sai suka ga ashe cewa tuni ma mun ficeshi, dan kuwa duk yana cikin littattafanmu na Musulunci.


Wannan arziki namu dashi ne akayi amfani wajen gina kasar, lokacin da yankin Arewa da kudu suka cure a matsayin kasa guda (Amalgamation) a shekarar 1914, wanda hakan ne yasa turawan suka kafa sansaninsu da kuma fadar gwamnatin tarayya a jihar Legas.


Inda daga nan Arewa muka dage da noma, wadda takai har ana safarar Auduga da Gyada, Ridi da makamantansu zuwa kasashen duniya da dama ta hanyar sufurin jirgin kasa, kafin daga bisani ayi nasarar gano man fetur a wani gari mai suna Oloibiri dake jihar Bayelsa a ranar 10 ga watan Yuni (June), na shekarar 1956, inda akayi amfani da arzikin Arewa wajen gina matatun man fetur da kuma kayyakin hakoshi.


Daga bisani ne kuma aka shirya za6en wakilai daga kowanne 6angare na kasar, wadanda zasu kasance a matsayin 'yan majalisa ko kuma ministoci (Parliament), wadanda zasu taimakawa Gwamnan da kasar Ingila ta turo, inda aka gudanar da za6en cikin shekarar 1959 wanda jahar Arewa ta lashe kujeru mafiya rinjaye.
Kafin daga bisa 'yan Arewan su jagoranci kar6o 'yancin kai (Independence) a karshen shekarar ta 1959 zuwa farkon shekarar 1960, inda a karshe sukayi nasarar kar6owa, wanda ya bawa Sir. Abubakar Tafawa Balewa damar jan ragamar kasar.
Kasar taci gaba da zama karkashin kulawar manyan jiga-jigan Arewa, har izuwa shekarar 1967 inda 'yan kabilar Inyamurai kiristoci suka tsokani Hausa/Fulani Musulmai, wanda hakan ce tasa saboda karfi irin na 'yan Arewar a waccan rana sukayi nasarar karar Inyamuran zuwa yankinsu, inda ya harzuka Gwamnan jihar gabas (Easteen Region) Janar Emeka Ojukwu, wato yankin Inyamuran, bayyana yankin nasu a matsayin kasa mai cin gashin kanta, inda suka kirata da suna kasar "Biafara".


Wannan fa shine kadan daga cikin girma, karfi, ilmi, wayewa, daraja da kuma daukaka da yankin Arewan yake dashi a baya, wanda hakan ce tasa al'ummar Kudun suke ganin kamar akan me zamu fisu daukaka da daraja, inda mu kuma rashin sanin wannan daraja da muke da ita, shine a yanzu ya jawo mana zagin shugabanninmu, su kuma shugabannin namu suke zaluntarmu, kuma basu damu da damuwarmu ba, yayin da a gefe guda kuma 'yan yankin kudun suke wulakantamu, tare da yi mana cin kashi, da kuma kashemu kamar suna kashe klKiyashi, tunda dai bamu san darajar kanmu ba, kuma bamu da hadin kai irin na wadancan da suka gabacemu, wadanda suka gina kasar.


Saboda haka, idan har muka ci gaba da wannan yanayi to kuwa zamu ci gaba da wulakantuwane fiye da wadda muke ciki a halin yanzu.


Zamu ci gaba insha Allahu....Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user