Monday 23 September 2024

Zafafan Gajerun Kalaman Yabon Kwalliya Da Ado Na Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Kina burgeni idan har na ga kin yi kwalliya da jan kayanki, ba na jin shakkar nuna wannan kyakkyawar fuskar taki.


Kalaman Yabon Kwalliya Da Ado Na Masoyiya
Hoto: Deposit photos

MarubuciImran Musa Jahun


Murmushin da ki kai ne ya haddasa fitowar fararan haƙoranki, a sannan ne na yi tozali da tsagaggiyar wushiryarki, bayan kin lumshe daradaran idanunuwan nan naki a lokaci ɗaya kika ƙara tafiya da zuciyar da na mallaka miki.


Kina ƙara yin kyau idan har ki kai wa daradaran idanuwan nan jagira.


Kina ƙara shiga zuciyata idan na ga kin shafa siririn hancin nan naki, musamman ma a ce kin yi mini farin da kike da idanuwanki.


Dukkan rayuwata na ba ki, na san ba za ki wasa ba, za ki riƙe ta da hannunki, roƙona ga Allah shi ne yasa na zamo mijin ki.


Ba na tunanin komai, hatta mafarki ba ya zuwar min sai da sunanki, koda abinci zan ci sai na haɗa da kallon hotanki, koda hira za ai da ni dole sai an sako min maganar ki.


Kin ce kin amince da ni har na zamo Uba ga 'ya'yanki, na kan yi farin ciki idan na tuno ba kya wasa da addininki.


Kin kasance rayuwata, ni kuma na zama taki, ki ba ni kulawa, ni kuma na ɗauki alƙawarin ninka taki.


Kullum burin rayuwa na tarairayeki, duk mai san farin cikina to ya faranta miki.


Bayan kallon kyawawan haƙoranki na shiga shauƙi har na manta kaina saboda kyawunki, kin iya kwalliya musamman ma na ga kin shafa jambaki a ɗan ƙaramin bakin ki.


Ina jin farin ciki saboda na same ki da tarbiyyarki, ba na jin kiran da ba shi da alaƙa da sunan ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user