Tuesday 24 September 2024

Karanta Sirrin Genotype Da Amfanin Shi Ga Al'umma

Tura Wannan Zuwa Ga

Sakamakon wani rubutu da na yi satin da ya wuce nake bada shawarar ya kamata kowa ya san genotype ɗinsa kafin soyayya ta yi nisa, don rabuwa bayan shaƙuwa babu daɗi, sai wasu da yawa suka dinga neman sanin mene ne genotype? Rubutun ya ƙayatar amma akwai jigon rubutun da ba a sani ba, wanna yasa na ce zan yi gajeren bayani akan mene ne genotype?


Sirrin Genotype Da Amfanin Shi Ga Al'umma
Hoto: Stock Adobe 

Marubuci:- Aminu Murtala Shuaibu


Mutane sun kasu kaso uku ta fuskar halittar jini da Allah ya yi musu:



1. Awai mutum mai nau'in jini AA


2. Akwai mutum mai nau'n jini AS


3. Akwai mutum mai nau'in jini SS


Shi na farko (AA) lafiyayye ne, kuma zai iya aurar mace mai kowanne irin nau'in jini ba tare da sun haifi ɗa mai matsalar amosanin jini (sikila) ba. Kai an ma fi son shi mai irin wannan nau'in jinin ya auri mara lafiya (SS) domin daƙile yawan masu wannan cuta a doron ƙasa.


Idan ya auri mai nau'in jini na uku (SS), 'ya'yan da za su haifa duka za su kasance masu lafiya a karan kansu, amma masu rabin lafiya ne a halittar su. Kenan barazanar su ɗaya ce, dangane da wanda za su aura da kuma 'ya'yan da za su haifa.


Na biyu kuma (AS) yana da rabin lafiya ne (normal but carrier). Shi a karan kansa lafiyayye ne, amma a halittar jininsa rabin lafiya gare shi. Illar tana ga abinda za su haifa ta silar macen da ya aura ko namijin da ta aura. Idan ya auri mai nau'in farko (AA), to duka 'ya'yan da za su haifa lafiyayyu ne a karen kansu, amma akwai yiwuwar su haifi masu irin nau'in jini na biyu (AS) lafiyayye a karan kansa. Amma idan ya auri mai nau'in jini na biyu (AS), to da yiwuwar (probability) ɗin su dinga haifar lafiyayyu (AA), ko masu rabin lafiya (AS) ko marasa lafiya (SS) ko kuma a dinga cakuɗa musu duka. Idan kuma ya auri mai nau'in jini na uku (SS) to wannan kam da matsala babba, domin da yiwuwar su yi ta haifar marasa lafiya (SS) ko masu rabin lafiya (AS), amma yiwuwar samun marasa lafiya ɗin shi ya fi yawa. Don haka ake bada shawarar me rukuni na biyu ya nemi ko ta nemi mai nau'in jinin rukuni na farko.


Na uku (SS), mara lafiya ne, yana fama da cutar sickled cell anaemia (sikila), don haka shi bai da buƙatar kowa wajen aure sai mai nau'in jini na farko( AA), domin ta haka ne kaɗai ba za su samu 'ya'ya masu ɗauke da cutar ba.


Duka 'ya'yan da za su haifa za su kasance masu rabin lafiya (AS), kenan a karan kansu su lafiyayyu ne, illar tana ga abin da za su haifa ta hanyar wanda suka aura.


Jan hankali;


Ya kamata kowa ya san a wanne nau'in yake (AA, AS ko SS) ta hanyar gwaji domin fuskantar abokin rayuwar da ba za su haifi ɗan da zai zamo cikin wahala da ƙuncin rayuwa ba, haka nan ku ma ba za ku kasance cikin ƙaƙanaƙayin rayuwa ba.


Masu sikila suna shan matukar wahala a rayuwa, haka nan iyayensu, sannan tsawon rayuwar su gajere ne, shi yasa da wuya ka ga mai sikila ɗan shekaru sama da 35 (ana samu amma bai fi 1 cikin 100 ba).M


Masu sikila sun kasance ababen shiga rai, ana saurin sabo da shaƙuwa da su, shi yasa duk abin da mutum ya tara to zai iya rabuwa da shi akan lafiyar wani nasa mai sikila.


Maganin bari kar a soma.


A kula:


Duk maganar da muke yi muna yi ne a kan iya namiji, amma kuma hukuncin ya shafi duka ne (maza da mata) domin taƙaita rubutun.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user