Monday 23 September 2024

Wakar Asiya A Rubuce Ta Umar M Sharif

Tura Wannan Zuwa Ga

'Yar budurwata!! 'Yar budurwata Asiya son ki yai nisa a zuciya.


Ko cikin birni aka bincika za a sha nema.


Ka'idojin so duka kin cika tunda kin girma.


Ko a tarihi aka waiwaya sunan ki na nan ma.


Ta daban ce ke Asiya zan kula ki kamar marainiya.


Waƙar Asiya A Rubuce
Hoto: Kinga team 2007

Da kin fito an gama.


Ganin ki ya sa ni kiɗima.


Soyayya an ce ruwan zuma.


Ki ba ni in sha a ƙorama.


Gani ki ban dama.


Don na yo girma.


Gani ki ban dama Asiya don na yo girma a zuciya.


A cikin birnin garin mu ke ce kike haske.


Kwalliya tsafta da natsuwa babu tamkar ke.


Da kin fito gayu ta ko'ina ke suke leƙe.


Ke ake rububi a zo a ga tun da kin zamto zinariya.


In ka ga na yi ado na caɓa kwalliya.


Na yi shi ne dan Asiya.


In ka ga walwala a fuskata da dariya, waye sila? Asiya.


Soyayya ce muke bil haƙƙi da gaskiya.


Tunda ga ƙoƙon zuciya.


Rana ta aure Allah ya kai mu in zama ni ne angon Asiya.


Ni wai yaushe mafarkina za ya zam gaske ne?


Wai ni yaushe tunanina za ya zam gaske ne?


Ba ni son wata 'ya mace sai ke.


Ban ganin kyawun mace sai ke.


Ba na ɓoyewa a ko'ina na shiga ni ne na Asiya.


'Yar budurwata!! 'Yar budurwata Asiya son ki yai nisa a zuciya.


Umar M Shareef ne ya rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku.


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user