Showing posts with label Wakoki/Kasidu A Rubuce. Show all posts
Showing posts with label Wakoki/Kasidu A Rubuce. Show all posts

Friday, 20 December 2024

Wakar Allahu Ga Bawan Ka Nan A Rubuce Ta Bash A. Adam

Wakar Allahu Ga Bawan Ka Nan A Rubuce Ta Bash A. Adam

Hmm Allahu ga bawanka nan.


Kewa nake in ba ya nan.


Kare shi Allah ko'ina yake ka sa ya tuna da ni.


Kula da shi namijin gari.


Ya fi min maza miliyan ɗari.


Na ƙuna ba na jin bari a kansa ku mini uziri.


Waƙar Allahu Ga Bawan Ka Nan A Rubuce Ta Bash A. Adam

Hm ƙauna da son ki nake zara.


To kin ga dole na yunƙura.


In babu ke wa zan hara?


Rashin ki zai shiga makara.


Dubun maza ba su kai ni ba.


Don ba su samu kamar ki ba.


Baki ka gan shi yana zuba sai in ƙi na kusa daf da ni.


Ka iya soyayya, ita 'ya mace ka ga tana son rarrashi.


Da nuna kulawar nan ka ji ƙauna wacce ake yi wa alwashi.


Ka zarce maza iya kallon so mai sanya gaɓa ta jiki laushi.


In ka bar ni cikin su maza ban san kuma wa zan ɗauko ba?


Bari!! Wannan batu bai min daɗi ba a kunnena.


In na bar ki na bar baya da ƙura, ya za nai da magautana?


Ke na gasgata ke zan kai gidanmu, ki gai da iyayena, tamkar jariri haka za ki yo ɗawainiya gun rainona.


Na ƙi!! Ni ba za a kai ni ba.


Ina ne wai ba za a je a kai ki ba?


Gidan wanin ka ba zan je shi ba.


Ni ma ba zan bari a raba mu ba.


Ka waiwayo kallon ka bai ishe ni ba.


Har abada ba za na daina son ki ba.


Da kai na so zama ba zan bar ka ba.


Kowa ya kula ki ban yafe shi ba.


Mawaƙi Bash A. Adam tare da mawaƙiya Fati Khalil Zabia ne su rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi ku. Musamman masoya da ma'aurata.


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.

Saturday, 14 December 2024

Kasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim

Kasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim

Duniya budurwar wawa, mutuwa tana kan kowa, haka dole za ta biyo ka kodayaushe ko ba ka so ba.

Ƙasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim
Hoto: Rollover/iStock photo

Zuciya tana mini rauni, ta hana ni in yi sukuni, watarana za mu rabu dukan mu ba za mu sake gamo ba.

Lamarin yana mini tsauri, a cikin bugawar fari, babu wanda sam ya sani idan ba kaliƙin mu guda ba.

A cikin watan watarana za a yanke duk wata ƙauna, dukkanin abin da ka mallaka ba za a kai ka da shi ba.

Daɗa yanzu ka zama gawa, haka za a kai ka kushewa, daga kai kaɗai sai ayyukan da ka aikata ba wai ba.

Duniyar ga ƙyalƙyal banza, kyan macijiya ba izza, walwali take daga nesa in ka iso ba za ka gani ba.

Yaudarar tana mini zafi, da shigo-shigo ba zurfi, ran da duk ka bi ta ta kai ka inda ba za ka ko dawo ba.

Shi agogo ba ya baya, kuma lokaci bai ƙarya, duk irin da kai ka dasa shi dole akwai yinin yin girba.

Furfura alamar tsufa, yau da gobe tamkar jifa, lokacin ka ba ya jira idan ya wuce ba zai dawo ba.

Ga jikin ka ba shi da ƙwari, yara duniya labari, duk abin da za ka saye shi don ka ci sam ba zai daɗi ba.

Maigidan ka ya mutu shi ma, mutuwar ka ba ta girma, jinjiri ya kan mutu saurayi yai rayuwa gwaggwaɓa.

Ka taho kana yin kuka, ka mace ana maka kuka, da bazar ka ne wasu ke rawa ba su so a ce ka kau ba.

Wasu sun mace sun huta, wasu sun wuce an huta, kar ka zam a gundura har da za ka mace ba ai kewa ba.

Ka yi tarbiyyar 'ya'yan ka in ka tsufa za su ji ƙan ka, haka nan idan ka mace ba za su gushe suna addu'a ba.

Annabin ka ne baƙon ka, girmama shi kar ka guje shi kar ya guje ka, wanda duk ya girmama Ɗan Adam ba zai rashin matsayi ba.

Arzikin ka na a jikin ka, zai biyo ka kan ajalin ka, bi a hankali dukkan rabon ka ba za ya zo ya wuce ba.

Duniya gidan kashe ahu, la'ila ha illallahu, yanzu ƙila likkafanin ka ya isa kasuwa ba ka sani ba.

Sa'eed Ibrahim ne wanda ya gabatar da wannan ƙasida mai cike da saƙonni masu amfanarwa ga kowa, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ƙasidar a rubuce domin ilimantarwa da fadakarwa a gare mu gabaɗaya.

Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan ƙasidu a rubuce masu ma'ana tare da waƙoƙi a rubuce su ma masu ma'ana.

Friday, 15 November 2024

Wakar Abar Mini Kayana A Rubuce Ta M. Rayyan

Wakar Abar Mini Kayana A Rubuce Ta M. Rayyan

A bar mini kayana.


Kawai daga ni sai ke, a tare mu yo aure ka rungume 'ya'yana.


A bar mini kayana.


Kawai daga ni sai kai, a tare mu yo aure ki rungume 'ya'yana.


Waƙar ku bar mini kayana a rubuce
Hoto: Freepik

Ƙwalelen 'yammata.


Ku bar ni da kayana.


Ƙwalelen 'yan gayu.


Ku bar ni da kayana.


Ƙwalelen 'yammata.


Ku bar mini kayana.


Ƙwalelen 'yan gayu!


A! Ko ya yake ya yi min.


Ku bar ni da kayana.


Salo nasa ya kai min.


Ku bar ni da kayana.


Ni so nasa ya cim min.


Ku bar ni da kayana.


Komai na biɗa ya min.


Ku bar ni da kayana.


Ku bar ni da shi kun ji, ku bar ni da kayana, mai so ya ga kukana uba gun 'ya'yana.


Ƙwalelen 'yammata!!


Ku bar ni da kayana!!


Ƙwalelen 'yan gayu !!


Ku bar ni da kayana!!


A! Muna ra'ayin juna.


Ku bar mini kayana.


Muna mararin juna.


Ku bar ni da kayana.


Sunan ta a bakina.


Ku bar mini kayana.


Da son ta a ƙirjina.


Ku bar ni da kayana.


Da safe zuwa rana.


Na gan ta a damana.


Ta zo a mafarkina ta saita muradaina.


Ƙwalelen 'yammata!!


Ƙwalelen 'yan gayu!!


Ku bar mini kayana!!


A! irin ki idan an samu a ji daɗi.


Fura taka ta sha damu ta ji garɗi.


Kira nai don an kai ki ki yi faɗi.


'Ya'yanmu idan mun samu su ji daɗi.


A bar mini kayana, kawai daga ni sai kai, a tare mu yo aure ki rungume 'ya'yana.


A! abar mini kayana.


Kawai daga ni sai ke, a tare mu yo aure ka rungume 'ya'yana.


Ƙwalelen 'yammata!


Ku bar mini kayana.


Ƙwalelen 'yan gayu.


Ku bar mini kayana.


Ƙwalelen 'yammata.


Kawai daga ni sai ke.


Ƙwalelen 'yan gayu!


Ku bar ni da kayana.


M. Rayyan da Shamsiyya Sadi ne su rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku. Musamman masoya.


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.

Saturday, 9 November 2024

Wakar Ruhin Mijina A Rubuce Ta Aminu S. Bono Ft Zala FKD

Wakar Ruhin Mijina A Rubuce Ta Aminu S. Bono Ft Zala FKD

A! ruhin mijina!!!


Ruhin mijina ban yarda ya mace ba.


Na ji mutane suna ta faɗin ka yo macewa.


Ni ko na san ba haka ne ba tashi nawa.


Domin mutuwa in ta zo sam ba ta wucewa.


Waƙar ruhin mijina a rubuce
Hoto: MSN


Domin yauƙi na gane sai miyar kuɓewa.


Ita ko mutuwa in ta zo ba ta sanarwa.


Ban yarda a ɗauke ka ba can zuwa kushewa.


Haba mijina tashi.


Saboda ƙauna amshi.


Ruwan zuma za na ba ka ka sha ka wanke dukkan ƙalbi.


Kuka nake yi a kanka a yau ina ta yin jan carbi.


Yaushe mu kai auren har a ce da za a ɗauke mini kai.


Wayyo mijina tashi!


Haba mijina.


Dan Allah bar zolayana.


Wayyo mijina! Ruhin mijina!!


Ruhi!!


Ruhin mijina.


Ki haƙuri kin ji tawa.


Nabila yau nai macewa.


Iko na Allah mutuwa yau ba ta ƙyale kowa.


Da ni da ke ba rabewa.


Kina cikin ruhina, abadan ba gushewa.


Hakan Ilahu ya tsara, daga aure sai rabewa.


In mutuwa gaskiya ce, addu'a za ki riƙewa.


Allahu shi za ki riƙe, ki bar su su kai ni can makwanci.


Mafi daɗin soyayyata, ku kai ni ramin ƙabarina.


Nabila kuka ki daina, Dan Allah share hawaye, na tafi sai watarana.


Ruhin mijina!!


A farke ba a barci ba, kake min gizo.


Ba ka rage ni komai ba, kallon ka shi na so.


Zaman mu za ya yo riba, da mun riga da mun saba.


Fuskarka ce abin duba, ban da kamar ka na saba.


Ruhin mijina, ku ƙyalen mijina.


Ina son mijina.


Wayyo mijina!!


Ku ƙyalen mijina.


Ruhin mijina!!


Marigayi Aminu S. Bono da Zala FKD ne su samar da wannan waƙar, su kuma rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi  ku. Musamman ga masoyan da su rasa rabin ransu a yanayin da ba su yi tsammani ba.


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi masu ratsa sassan jiki a rubuce da ƙasidu ma a rubuce.

Friday, 1 November 2024

Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (5)

Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (5)

Tamkar mai hauka haka Laila ta koma bayan da ta yi duk abin da za ta iya don ganin masoyin nata a farke, idanuwan Laila tuni sun ƙanƙance saboda tsabar kukan da ta ke yi.


Labarin Soyayyar Majnun Da Laila
Hoto: Kekisruhan

Marubuci:- Auwal Ilyas Adam


Cikin wata murya wadda kunne ba zai iya tantancewa ba ta fara rera wasu baitoci kamar haka:


Wanzuwata da numfashi na na gan ka a damana.


In ka bar ni anan duniyar ga wane ne gatana?


Yaka taso zo, ni ganin ka shi ne fatana.


Tana kaiwa ƙarshen baitocin sai ta ƙwala masa kira da ƙarfin gaske "Majnun!"


Can kuma a mahaɗar nan wadda daga nan ne za ka yi shirin shiga Habasha, wato inda iyayen Laila suka yada zango kenan, bayan iyayenta sun gama shiryawa tsaf sai mahaifiyarta ta duba ba ta gan taba, nan da nan ta sanarwa da mahaifinta halin da ake ciki, neman duniyar nan sun yi a wannan mahaɗar wadda take tamkar wani ɗan ƙaramin gari ne amma ba Laila ba alamarta, hankalin iyayenta ya tashi, anan wasu suka ba wa iyayen shawara akan su ƙarasa cikin Habashan ko wataƙila ta bi ayarin wasu gungun fataken ne.


Hakan kuwa akai wato iyayen Lailar suka amince da hakan, isar su Habashan keda wuya ba su zame ko ina ba sai fadar sarkin, a matsayinsu na su ma masu ƙaramar sarauta a masarautarsu, yayinda iyayen Laila suka labartawa sarkin Habasha labarin ɓatan 'yarsu da ma cikakken labarin Laila da Majnun ɗin, sai sarki da muƙarrabansa suka cika da mamaki yayin da wasu da yawansu suka ringa kuka saboda tausayin waɗannan masoyan, sarki ya haɗa wata tawaga ta mahaya ɗari ya ce su nufi can nahiyar da aka baro Majnun ɗin ko wata ƙila za'a gan ta a can wajensa, kuma ya ce musu idan sun gan su to su taho dasu gabaɗayansu zuwa fadarsa.


Gwauron numfashin da ya ja ne ya sa Laila ta karkato da hankalinta zuwa gare shi, tabbas Majnun ɗinta ne yake numfasawa, sannu a hankali ya buɗe idanunsa waɗanda ba sa iya buɗewa gabaɗaya saboda tsabar wahalar da Majnun ɗin ya sha, Laila ta dube shi cikin shashsheƙar kuka haɗe da dariya ta ce, "Majnun ni ce Lailarka, gani a tare da kai na dawo Majnun... Ba zan iya rayuwa ba ba tare da Majnun ɗina ba..." 


Duk da halin da yake ciki hakan bai hana bayyanar wani tattausan murmushi ba akan kumatunsa, cikin sanyin jiki ya lalubo hannun Laila ya matse shi gam a hannunsa tamkar yana tsoron kada wani abin ya zo ya kuma raba shi da Lailarsa.


DUBA WANNAN: KARANTA CIKAKKEN LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN 


Wata rana Majnun ya zo ya wuce ta gaban mai sallah yana begen Laila bayan mai sallah ya gama sai ya yi sauri ya sha gaban Majnun don ya ji dalilin da ya sa ya tsallaka mashi sallah?

 

Majnun ya dubi mai sallah ya ce


"Yaushe ka gan ni"


Mai sallah ya ce "Lokacin da nake sallah".


Majnunin Laila ya ce "Wallahi ina cikin begen Laila har na wuce ban gan ka ba, kuma Wallahi da soyayyar ka ga Allah ta kai kwatankwacin yadda nake son Laila to na tabbatar kai ma ba za ka gan ni ba.".


Ina jin anan zan tsaya da ba ku wannan ƙayataccen labarin.


Ku ci-gaba da kasancewa da ni domin jin wasu daɗaɗan labaran.