LAILA TO GASHI NAN....
Labarin Soyayyar Laila Majnun...
Tabbata baku taɓa cin karo da irin wannan ba....
Waye majnun lailah?
Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya
abisa zancemafi inganci. Sunansa shine "Qais Bn
Mulawwah" daga "kabilar Banu Amir",
Qais balaraben ƙauyene, ya taso tare da ‘yar gidan
kawunsa mai suna "LAILA BNT MAHDI IBN SA’D"
Amfi sanin Laila da sunan "Laila Aamiriya", tare suka
taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka
girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin
balagha.
Kalli bidiyon labarin kai-tsaye
A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci
suka gama bayyana ajikin Laila sai "Qais" ya ruɗe
soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya
tashi.
Domin a wannan lokacin ne "Qais" ya Lura da irin
kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa "Laila", a
kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi
take yi a cikin zuciyar "Qais", a cikin wannan yanayi
ne "Qais" ya shiga rera mata waƙoƙin soyayya kala-
kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi
mahaifin "Laila" ya nemi da "Qais" ya fito dan
maganar aure, saboda nuna soyayya da ƙauna sai
da Qais ya bayar da raƙuma hamsin a gidansu
"Laila" a matsayin kudin aure.
Ana haka sai ga wani mutum da ake kira "WIRD BN
MUHAMMAD" wani dan hamshaƙin attajiri ne daga
cikin ‘ya’yayen masarautar "Banu Umaiyya", katsahan
yayi ido hudu da "Laila" a wata rana a cikin wani
Lambu tana kiwon dabobinta.
Daga wannan rana Soyayyar "Laila" ta hana Wird ya
yi bacci a wannan dare!
Cikin yan kwanaki kadan
Iyayen "Wird" suka sauka a gidan su "Laila" dan
neman aurenta ga ɗansu "Wird".
A wannan rana da Iyayan "Wird" suka je ga mahaifin
"Laila" sai da suka ajiye masa Manyan Raƙuma
guda ɗari (100) a matsayin kuɗin aure, wato ribi
biyu akan abinda "Qais" ya bayar!
Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin
kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna
kwadayi da son abin duniya.
Bayan haka ne
Mahaifin "Laila" ya kira‘yarsa "Laila" cikin ɗaki yanai
mata huɗubar cewar ga mai kudi ɗan masu mulki
shi zai aurawa ita!
Babbar Magana! Laila taƙi amincewa da maganar
mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata
barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince
da auren "Wird" ba!
Kwatsam sai aka wayi gari "Qais" ya ji gari ya ɗauka
da kace nace ɗin an yiwa masoyiyarsa "Laila" aure,
da "Wird".
Nasan da yawan ku zaku tambayi wakilin shafin Muryar Hausa24 ko Wanne irin hali "Qais" zai kasance a wannan ranar?
Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga
idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin
ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye
babu dare babu rana, suka kasance tare da "Qais" a
matsayin abokai na din-din-din!
Waƙe-waƙen soyayya sune zancensa, bashi da
abokin hira sai waƙar da yake yiwa "laila" ga kadan
daga irin abinda yake cewa:
zuwa ga Allah nake kai kukan son "laila"
kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa
zuwa a Allah.
Mara yanda da kafasa ta karye gashi kuma dangi
sun gujeshe "Lallai" rasa iyaye abune mai girman
gaske.
Haka "Qais" da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah”
yake bin kwararo kwararo da saman manyan
duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa
Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai
gushe ba harsai da akayi masa laƙabi da “majnunu
laila”.!
Duk da cewa itama Laila tana matukar son
"Qais" (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta
wahalar dashi, a wasu lokutan ma harda yi masa
wulaƙanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi
wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake
shi yasa majnun awani baiti yace:
“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a
makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar
dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina
sonta) shin hakan da take ba laifi bane?”
Sai Malamin ya fadawa "Qais" cewa: “Wallahi da
sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita
hadu da bala’i”.
Daga nan "Qais" yace, sai na kasa mallakar idona
sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiƙa min
aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta
duk da yake a duniya dan kadanne samunta.
"Qais" ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan
hali har sai da ya samu taɓin hankali.
Domin ya
kasance idan yaga yara suna wasan ƙasa yakan
zauna tare dasu ya taro kasa ya rinƙa gina gida irin
wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waƙa:
“abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!
A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka
baiwa mahaifin "Majnun" wato "Qais" shawara da ya
daukeshi ya kaishi ka’aba (Ɗakin Allah) ya umarce
shi da ya roƙi Allah ya cire masa son Laila!
Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je
ɗakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama
tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila...
Sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka
daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da
nake yiwa "Laila" ba.
A taƙaice haka "majnun" ya rayu cikin wannan yanayi
na abin tausayi!
Ita kuwa "Laila" tuni wanda ya aureta ya ɗauke ta daga
kasar Saudiyya ga baki ɗaya zuwa kasar Iraqi.
Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi
abinka da ‘ya mace mai rauni sai da rashin ganin
"Qais" ya haddasa mata ciwon zuciya .
Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda
tsananin soyayyar "Qais Majnun"!
Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta
Allah ya karbi rayuwarta!
A lokacin da "Majnun" yaji labarin rasuwarta sai da
yaje har ƙasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka
binne ta, a maƙabartar da aka binne "laila" a dai-dai
gindin kabarinta ya tare.!
Bashi da aiki sai kuka da waƙoƙin soyayya a
gareta.
Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi
(Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan kabarinta, ko da
aka zo akaduba sai aka tarar Allah ya yi masa
cikawa!
Allahu akbar
Wannan shine Qarshen hikayar "LAILA MAJNUN" kunjifa yadda akeyin soyayya ruwa-ruwan ta.
Rubutawa Tafarkin Tsira Tace rubutu da tsarawa tare da Hotuna wakilin shafin Muryar Hausa24 .
Haka fa Allah yake jarabtar wasu da soyayya..
Ya Allah kada ka jarabcemu da soyayyar da bazamu iyaba.
KU SAURARA KUJI LABARAI 3 MASU BAN MAMAKI
Duk wanda bai taɓa karanta labarin Romeo da Juliet
ba lallai akwai sauransa ga sanin tarihin soyayyar
artabu, kisisina da sanin kololuwar sadaukarwar
masoya.
Wanda kuma ya ji labarin soyayyar Sarki Shah
Jahan da matarsa Mumtaz Mahal, tare da ginin
soyayya mafi tarihi da tsada ‘Taj Mahal’ ya dan san
wani abu kadan fiye da wanda bai san ko kaɗan ba.
Wanda ya san tarihin soyayya, da sauran labarun
soyayya, amma kuma bai taba fadawa tsaka mai
wuya ba saboda soyayya, kamar Sanawiyya ibn
ustaraz Tabbas bai san komai a Soyayya Ba.
Mutane nawa ke Da bukatar Sonjin Waɗannan
LABARAN SOYAYYA 3 NAN MASU BAN MAMAKI...
Idan kana/kina so ku hanzarta aiko mana da saƙo a email ɗin mu kamar haka Muryarhausa24@gmail.com
Tace rubutu da tsarawa wakilin shafin Muryar Hausa24 .
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com
Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng