Sunday 16 September 2018

Amfanin Dabino a Jikin Dan Adam: Cikakken Bayani da Yadda ake amfani da Shi

Tura Wannan Zuwa Ga
Dabino dan itaciya ne mai albarka, domin kuwa
Allah Madaukakin Sarki ya ambace shi a gurare
da yawa cikin Alqur’ani mai girma.


Dabino


Marubuci: Assalafy Safe

GURAREN DA ALLAH YA AMBACI DABINO A
AL-QUR’ANI..

1. Suratul Bakara, Aya ta 226
2. An’am, Aya ta 99 da 141
3. Suratul Ra’ad, Aya ta 4
4. Suratul Nahli, Aya ta 11 da 67
5. Suratul Isra’i, Aya ta 91
6. Suratul Kahfi, Aya ta 32
7. Suratul Maryam, Aya ta 23 da 25
8. Suratul Daha, Aya ta 71
9. Suratul muminin, Aya ta 19
10. Suratul Shu’ara, Aya ta 148
11. Suratul Yasin, Aya ta 34
12. Suratul Ka’af, Aya ta 10
13. Suratul Kamar, Aya ta 7
14. Suratul Rahman, Aya ta 11 da 68
15. Suratul Ha’akkah, Aya ta 7
16. Suratul Abasa, Aya ta 29

AMBATON DABINO A SUNNAR MANZON ALLAH
(SAW)

1- Manzon Allah
(SAW) yake cewa, “Idan kun kai azumi,
to ku yi buda baki da dabino, amma idan
bai samu ba to ya yi amfani da ruwa,
domin ruwa na tsarkakewa.”

2-
Haka Kuma MANZON ALLAH
(saww) YACE DABINO AJWA YANA MAGANIN
DUKKAN CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA
KACISHI,BABU WATA CUTA DA ZATA SAMEKA
AWANNAN RANA, KO KUMA SAMMU KO
SIHIRI.”

Wasu MALAMAN MUSULUNCI kuma sunce...

Annabi (SAW ) Yana
nufin kowanne dabino ba wai sai
Ajwa ba (Wallahu A’alam).
Dabino yana dauke da sinadarin da ke
karawa jiki karfi da kwari, yana mayar da
sukari da ke cikin jinin mutum wanda
yake raguwa sakamakon rashin cin abinci
ko abin sha, dabino yana dauke da
sinadarin ‘Iron,’ wanda yake taimakawa
wajen karin jini. Sannan yana karfafa jini
da hantar mutum. Ga wasu daga ciki:-

1. Yana samar da ruwan jiki
2. Yana taimakawa mata masu ciki
3. Yana karawa mai shayarwa ruwan
nono
4. Yana gyara fatan jiki
5. Yana maganin ciwon kirji
6. Yana maganin ciwon suga
7. Yana maganin ciwon ido
8. Yana maganin ciwon hakori
9. Yana gyara mafitsara
10. Yana maganin basir
11. Yana kara lafiyar jarirai
12. Yana rage kiba, wadda ba ta lafiya
ba ce ma’ana kumburin jiki na ciwo
13. Yana maganin, majina
14. Yana sa kashin jiki ya yi karfi
15. Yana maganin gyambon ciki (Ulcer)
16. Yana kara karfi da nauyi
17. Yana maganin ciwo ko yanka
18. Yana karawa koda lafiya
19. Yana maganin tari
20. Yana maganin tsutsar ciki
21. Yana maganin kullewa ko cushewar
ciki
22. Yana rage kitse
23. Yana maganin cutar daji (Cancer)
24. Yana maganin cutar Asma (Asthma)
25. Yana kara karfin kwakwalwa
26. Yana maganin ciwon baya, ciwon
gabbai, ciwon sanyi wanda yake kama
gadon baya.
27. Yana kara sha’awa da kuzari
28. Yana magance cututtuka dake
damun kirji
29. Yana karya sihiri.
30. Yana saurin narkarda abinci
31. Yana taimakawa wajen kara jini
32. Yana taimakawa Ma’aurata maza/mata
33. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a
bayi.
34. Yana Maganin Gudawa
35. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun
basira..
36. Yana kariya daga Sihiri
37. Yana taimakawa Mata masu ciki dan
samun
sauqi wajen haihuwa.
38. Yana kariya daga Sihiri.

YADDA ZA’AYI AMFANI DA DABINO.

CIWON NONO GA WACCEN DA TA HAIHU;

Anacin dabino guda 7 asha man
tafarnuwa karamin cokali sau 1
arana kwana uku.

DOMIN SAMUN NI’IMA GA MA’AURATA;

Ana daka dabino a zuba cikin
madara (freesh milk) sannan a
saka Zuma a ciki a sha awa daya
kafin a kwanta.

GA MATA MASU JUNA BIYU;

Ana cin dabino kwara bakwai
kullum da safe idan anyi kusan
haihuwa Wannan yana hanawa
macce yawan zubar jini lokacin
haihuwa da iznin Allah.

GUDAWA;

Ana daka garin dabino a saka a
ruwan zafi a sha In shaa Allahu
yana tsayar da gudawa.


Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1
da safe da yamma.

SAMUN LAFIYAYYAR FATA;

Ana hada garin dabino da zuma
da man zaitun a shafa a fuska awa
daya sai a wanke fuskar da ruwan
zafi wannan yana saurin gyara fuska.

Bincike
ya
nuna Yawaita cin
dabino na hana kamuwa da ciwon
CANCER ko wacce iri.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user