Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa.
Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan Amina (SAW).
A wani shudadden zamani, a wani gari na cikin kasar Farisa, an yi wadan su mazaje guda biyu yan uwan juna. Babban sunansa Kasim karamin kuwa sunansa Ali Baba.
Bayan rasuwar mahaifinsu, aka raba musu gadon yar dukiyar da ya bari, kowa ya kwashi rabonsa.
Kasim ya auri yar wani babban attajiri na garin, shi kuwa Ali Baba ya auri wata yarinya wacce iyayenta sun kasance talakawa ne. Ba a dade ba, sai surukin Kasim ya mutu, yarsa ta gaji dukkan dukiyarsa, domin ita kadai ce yar da ke gare shi. Ita kuma ta damka dukiyar nan a hannun mijinta Kasim. Nan take Kasim ya zama babban attajirin da babu kamar sa a duk fadin garin.
Shi kuwa Ali Baba sai ya kasance dan abin da ya gada na dukiya daga mahaifinsu ya kare. Ya zama talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku. Sai ya rika zuwa daji da jakansa yana saran itace yana lafto wa jakan nan yana kawowa cikin gari. Idan ya sayar, ya siyo abincin da za su ci, shi da matarsa.
Ana nan haka kullum, wata rana Ali Baba ya shiga daji domin yin sana'arsa kamar yadda ya saba. Bayan ya gama dora wa jakansa itace, yana haramar ya kora su ya tafi, sai ya hango 'kura ta toshe sararin samaniya daga nesa, ta tinkaro inda ya ke. Ya ga cewa idan ya ci gaba da tafiya mahayan nan za su cim masa, sai ya kora jakansa cikin rami, shi kuwa ya sami wata babbar itaciya mai duhuwa, wacce zai iya ganin abin da ya ke kasa ba tare da wanda ke kasa ya gan shi ba, ya haye.
Bai jima da hawa saman itaciyar nan ba, sai ya hango mutane akan dawaki a sukwane sun nufo inda ya ke. Suna zuwa wurin, sai duk suka ja suka tsaya. Kowane daga cikinsu ya sauka daga kan dokinsa, ya daure shi. Ali Baba ya dube su da kyau, ya ga cewa dukkansu samari ne majiya karfi, kowane yana rataye da takobi, yana dauke da kaya a kan dokinsa. Ya kirga su, ya ga cewa su arba'in ne cif.
Ashe mutanen nan barayi ne, masu tare fatake suna yi musu fashi, yanzu ma sun zo ne wurin da suke boye kayan da suke satowa. Ali Baba ya ga daya daga cikinsu, wanda yana zaton shi ne babbansu, ya tafi gindin wani dutse da ciyawa ta lullube shi, wanda idan ba yanzu ba Ali Baba bai taba lura da akwai dutse wurin ba. Ya tsaya gaban dutsen ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya tsaga gida biyu, sai ga kofa ta bayyana. Barayin nan suka yi ta duruwa ciki da kayan da suka sato, bayan kowa ya shige, sai babban ya bi daga baya. Yana shigewa, sai dutsen ya koma ya rufe, tamkar babu dutse a wurin.
Ali Baba yana kan bishiya, yana kallon dukkan abin da ke faruwa. Bayan barayin nan sun shige cikin dutse, sai yayi kamar ya sauko ya kama doki daya ya hau, ya kora jakansa ya tsere, sai kuma ya tuna idan ya sauko kuma aka yi rashin sa'a da barayin nan suna fitowa daga dutsen nan, lalle za su kama shi. Saboda haka sai ya canza shawara, ya ci gaba da zama a kan bishiyar.
Can zuwa wani lokaci sai ya ga kofar dutsen nan ta bude, shugaban barayin ya fara fitowa ya tsaya a gaban kofar yana kidaya barayin nan a lokacin da suke fitowa, har ya kidaya talatin da tara, gami da shi arba'in ke nan. Da suka gama fitowa, sai Ali Baba ya ji ya ce, "Garam, rufe dutsen Simsim." dutse ya koma ya rufe. Suka hau dawakinsu suka juya ta hanyar da suka fito.
Da Ali Baba ya ga kurarsu ta bace, ya sauko daga kan itaciya, ya nufi inda ya boye jakansa da sauri domin ya kora su zuwa gida, sai wata zuciya ta ce masa, "Ka gwada fadin kalmomin nan ka ga ko dutsen nan zai bude." Ya tafi gaban dutsen ya tsaya dai dai inda ya ga shugaban barayin nan ya tsaya, ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Yana fadar haka kuwa sai kofa ta bude.
Ali Baba ya kutsa kai cikin dutsen nan. Yana shiga sai dutse ya koma ya rufe. Da farko yayi zaton zai ga duhu dindim a ciki, amma sai ya ga haske kamar an kunna fitilu. Ya duba haka, sai ya ga dukiya tsibi-tsibi.
Tsibin zinariya daban, tsibin azurfa daban, na tagulla daban, gefe kuma ga kudi nan tsaba cunkus. Ali Baba yayi mamakin yadda wadan nan barayi suka tara dukiya mai yawa haka. Ya ce a ransa, lalle sun gaji dutsen nan ne tun daga kaka da kakanni, domin yawan su ba su isa su tara wannan dukiya ba koda kuwa sun yi shekara dari suna tara ta.
Ya tattaro wasu buhuhuwan zinariya, wadan da ya san jakansa za su iya dauka. Ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Dutse ya bude ya fito da buhuhuwan waje, sannan ya ce, "Garam, rufe dutsen Simsim." Dutse ya koma ya rufe. Ya jawo jakansa ya dora musu dukiyar nan sannan ya dora musu itace daga sama ya rufe yadda mutane ba za su gane ba. Ya kora su da sauri ya nufi gida yana murna.
Da ya isa gida, ya kora jakunan ciki ya kira matarasa suka sauke kayan. Koda ya zazzage, sai wurin ya haske, matar ta ga zinariya tana daukar ido. Ya shaida mata dukkan abin da ya faru. Ta yi godiya ga Allah, ta ce, "Dare daya Allah kan yi bature, hakika duk fadin garin nan yanzu babu wanda ya kai mu arziki. Bari na kidaya na gani"
Ali Baba ya yi dariya ya ce, "Mene ne na batan lokacinki wajen kidaya wannan zinariya? Sai ki yi kwanki ba ki gama gidaya ta ba. Abin da na ke so da ke shi ne, bakinki kanen kafarki, kada ki kuskura wani ya ji wannan labari. Zan je na haka rami mu binne wannan dukiya da Allah ya ba mu."
Matar ta ce, "Duk da haka dai ina so na san adadin wannan zinariya. Kafin ka gama haka rami bari na je nan makwabtanmu, gidan yayanka Kasim na aro karamin mudunsu na awon hatsi domin na ga ko mudu nawa wannan zinariya za ta yi."
Ya ce ba laifi amma ta tabbatar ba ta fadawa kowa abin da za ta auna da mudun ba. Ta fito ta shiga gidan Kasim, ta taras da matarsa. Bayan sun gaisa ta ce ta zo ne aron mudunsu na awon hatsi. Matar Kasim ta tambaye ta babba ko karami? Ta ce karamin ma zai yi. Ta shiga cikin daki domin ta dauko ma ta, ta ce a ranta, me wadan nan matsiyatan za su yi da mudu? Ina kuma suka sami hatsi mai yawa haka da har sai sun auna shi da mudu? Kuma wane irin hatsi ne wannan? Sai ta sami karo kadan ta manna shi a cikin kusurwar mudun wanda ta tabbata karon zai like kwaya daya ta hatsin da za a auna, ta haka za ta iya gano kalar hatsin da suka auna idan an maido mata da mudun. Ta kawo wa matar Ali Baba.
Bayan ta dawo gida, sai ta fara auna zinariyar nan mudu-mudu har ta gama kaf. Ta je ta sahida wa mijinta da yake hakar rami ko mudu nawa ta auna. Ta ce za ta je ta mayar musu da mudunsu. Ashe ba ta lura ba, kwayar zinariya daya ta manne da karon nan a can kasan mudun. Da matar Kasim ta karbi mudu, bayan matar Ali Baba ta tafi, sai ta duba cikin mudun. Wani irin mamaki ya rufe ta lokacin da ta ga kwayar zinariya a cikin mudun.
Nan take hassada ta daki kirjinta ta ce, ashe Ali Baba har yana da zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai awo da mudu. Ina ya sami wannan dukiya? Ko ya fara sata ne? Bari mijina ya dawo in fada masa halin da kanensa yake ciki.
Za mu ci gaba....Ranar Alhamis Insha Allah
Ku ci gaba da Kasancewa da Mu domin samun ci gaban wannan Kayataccen Labarin...
HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN (40) KASHI NA 2 - HIKAYAR TA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com
Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng