Showing posts with label Hikayoyi. Show all posts
Showing posts with label Hikayoyi. Show all posts

Tuesday, 25 March 2025

Hikayar Wani Mutum Da Kyakkyawan Doki

Hikayar Wani Mutum Da Kyakkyawan Doki

Wani manomi ne da ke zaune a wata alƙarya, yana da wani kyakkyawan doki kuwa, a duk lokacin da mutane su ka ga wannan dokin, sai su ce kai gaskiya wannan dokin naka kyakyawa ne, ka yi sa'ar samun wannan doki.


Hikayar Wani Mutum Da Kyakkyawan Doki
Hoto: The spruce pets

Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


Shi kuma sai ya ba su amsa da cewa "wata ƙila"


A na nan, wata rana doki sai ya ɓata, aka neme shi sama har ƙasa aka rasa.


Sai mutanen ƙauyen nan su ka fara zuwa masa jaje, duk wanda ya zo sai ya ce "kai dokin ka ya ɓace, gaskiya ka yi rashin sa'a."


Shi kuma sai ya ba su amsa da cewa "wata ƙila". Ya ci-gaba da sha'anin sa ba tare da ya damu ba.


Can bayan kwana biyu, sai ga doki ya dawo tare da shi da akwai kyawawan dokuna har guda bakwai, su ka zama su takwas kenan.


Manomi ya kama su ya ɗaure, mutane su ka yi ta zuwa suna taya shi murna, ai ka yi sa'a, kai ai gwara ma da dokin nan na ka ya ɓata.


Nan ma ya ce musu "wata kila".


Ai kuwa washegari, ɗan sa ya hau ɗaya daga cikin dawakan nan, sai kuwa ya goce ya faɗo har ya samu karaya a ƙafa.


Nan ma aka yi ta zuwa masa jaje, duk wanda ya zo sai ya ce abin ba daɗin ji, gaskiya an yi rashin sa'a.


Sai ya ce da su "Wata ƙila".


Bayan kwana biyu kuwa sai ga wani soja daga cikin dakarun sarki, ya zo da saƙo cewa sarki yayi umarni da ya zo ya tafi da duk wani matashi mai lafiya za'a tafi yaƙi, daga nan aka kwashe duk matasan garin, amma ban da yaron manomi saboda ya samu karaya.


Sai sauran mutanen gari su ka zo wurinsa su ka ce da shi kai ka ga sa'a, ɗan ka ba'a tafi da shi ba.


Manomi ya yi murmushi ya ce "Wata ƙila"


Darasi


Duk wani abu da ya faru da kai, na farin ciki ko baƙin ciki, ka mayar da lamuran ka ga Allah, wata ƙila wannan abin farin ciki ya zama sharri gare ka, wata kila kuma wannan abin baƙin cikin ya zama alheri gareka, wanda wata rana za ka ce "Kai, gwara ma da abu kaza ya faru".


Tuesday, 5 November 2024

Karanta Hikayar Tajiri Da Ifiritu (2)

Karanta Hikayar Tajiri Da Ifiritu (2)

Tsoho na biyu ma’abocin karnuka ya matso kusa da ifiritu ya fara bayar da labarinsa, ya ce, ka sani ya kai shugaban sarakunan aljanu, waɗannan karnuka biyu ‘yan uwana ne, ni ne na ukunsu. Mahaifinmu ya mutu ya bar mana gadon dinari dubu uku. Da aka raba waɗannan kuɗaɗe aka ba wa kowa nasa, sai ni na buɗe rumfa a kasuwa ina ciniki a cikinta, ina saye ina sayarwa. 'Yan uwana kuwa suka tafi fatauci.


Ci-gaban Hikayar Tajiri Da Ifiritu
Hoto: Walter Crane


MarubuciBukar Mada


Bayan shekara guda, sai 'yan uwan nan nawa suka komo daga fatauci, babu komai tare da su na daga dukiya, duk sun salwantar da ita. Na ce da su, “Ya ‘yan uwana ashe dama ba sai da na ba ku shawarar kada ku tafi fataucin nan ba?” Su ka ce da ni, “Ya ɗan uwanmu ashe ba ka yarda da ƙaddarar Allah mai girma da ɗaukaka da ya yi nufi a kanmu ba?”


Na karɓe su. Na riƙe su, na tafi da su gidana, na ba su abinci da sutura mai yawa, sannan na tafi da su zuwa ga rumfata ta kasuwa na ce da su na yarda su zauna mu yi kasuwanci tare da su, duk ribar da aka samu a raba ta uku daidai, kowa ya ɗauki kashi ɗaya.


Mu ka zauna akan haka har zuwa wani zamani mai tsawo. Sai wata rana ‘yan uwan nan nawa suka ce suna so za su koma fatauci tunda yanzu sun sami nasu jari, suka kwaɗaitar da ni akan mu tafi tare domin an fi samun riba mai yawa a fatauci. Na ƙi amincewa da in bar rumfata saboda na san ina samun riba sosai a cikinta.


'Yan uwan nan nawa ba su gushe ba suna kwaɗaitar da ni akan zuwa fatauci har tsawon wasu shekaru. Daga ƙarshe dai suka shawo kaina na amince da za mu tafi tare da su. Muka ƙidaya kuɗin da ke gare mu, muka ga muna da dinari dubu shida. Na ba da shawarar mu raba kuɗin nan biyu, mu binne rabi a ƙasa mu tafi da rabi, koda tafiya ba ta yi kyau ba, idan mun dawo muna da jarin da za mu ci gaba da kasuwancinmu. Suka aminta da wannan shawara tawa.


Muka raba kuɗin biyu, muka binne dinari dubu uku a ƙasa, sannan kowannen mu ya riƙe dinari dubu ɗaya. Muka sayi kaya, muka gama ciko, muka biya kuɗin jirgi, muka haura cikin bahar maliya. Sai da muka yi wata ɗaya muna tafiya a cikin jirgi, har Allah ya kai mu wani babban birni.


Bayan mun sauke kayan mu, muka shiga cikin birnin nan, muka fara ciniki, Allah kuwa ya sa wa kayan nan namu albarka, muka sayar da su duka. Muka ci riba har sai da kowane dinari ya koma dinari goma. Bayan mun huta a wannan birni tsawon wani ɗan lokaci kaɗan, sai muka yi niyyar komawa gida. Muka haɗa kuɗinmu, muka nufi bakin bahar maliya domin hawa jirgi.


Muna zuwa bakin gaɓar bahar maliya, sai muka iske wata yarinya wadda aka halicceta kyakkyawar halitta. Tana ganin mu, ta gaishe mu da ladabi, ta dube ni ta ce, “Ya shugabana, ko za ka yi mini wata alfarma guda ɗaya, ni kuma in saka maka da wani abu daban?” Na ce da ita, “Na’am, faɗi buƙatarki, zan yi miki koda kuwa ba za ki saka mini da komai ba.”


Yarinyar nan ta ce, “Ya shugabana, alfarmar da nake nema a wurinka ita ce, ina so ka aureni, ka tafi da ni garinku, ka aikata duk yadda ka so da ni a matsayin matarka. Haƙiƙa idan ka biya mini da wannan buƙata, to ka yi mini alheri mai girma wanda ba zan manta da shi ba, sannan ni kuma zan saka maka da alherin da ya fi wanda ka yi mini.”


Yayin da na ji zancen wannan kyakkyawar yarinya, sai na ji tausayinta a zuciyata, na yarda da buƙatarta. Na yi mata shimfiɗa mai kyau ta alfarma a cikin jirgin da muka shiga. Na yi mata karamci na martaba ta. Yayin nan jirginmu ya miƙa cikin bahar maliya.


Zuciyata fa ta so yarinyar nan, so mai tsanani, na zamana ba ni rabuwa da ita dare da rana. Na shagala da ita ga barin 'yan uwana. Ashe duk kishi ya kama su ban sani ba. Kuma da ma can ashe suna yi mini hassada game da yawan dukiyata da kayana. Kuma wannan tafiyar ma da muka yi ashe duk cikin shiri ne na su hallakani su kwashe dukiyata, Sheɗan ya rigaya ya yi musu huɗuba.


Sai da suka bari dare ya yi, kowa ya yi bacci a cikin jirgin nan, sai 'yan uwan nan nawa suka ɗauke mu, ni da matata, suka jefa cikin bahar maliya. Su na jefa mu sai na farka, matata kuwa sai na ga ta juye ta zama aljana, ta ɗauke ni ta yi sama da ni, ta kai ni kan wani tsibiri ta ajiye ni. Sai ta juya ta nufi inda jirginmu ya ke.


Da gari ya waye sai ga aljanar nan ta dawo wurina ta ce, “Ni ce matarka. Tun lokacin da na gan ka tare da waɗannan 'yan uwa naka, na yi dubi izuwa zuciyarsu na gani cewa su sun zo da kai wannan fatauci ne domin su halaka ka, na kuma yi dubi izuwa zuciyarka na ga kai mutumin kirki ne, kana tare da su ne tsakaninka da Allah. Domin na kuɓutar da kai, shi ya sa na rikiɗa zuwa ga kyakkyawar budurwa na nemi da ka aure ni domin in taimakeka. Amma 'yan uwanka sun cuceka, na yi fushi da su, babu makawa yanzu in kashe su.”


Yayin da na ji haka, sai na yi al’ajabi akan wannan al’amari, sannan na yi ta rarrashin ta ina ba ta haƙuri a kan kada ta kashe mini 'yan uwa. Na gaya mata labarin yadda nake da su duka. Ta ce lalle ba makawa sai ta dulmiyar da su cikin ruwa tamkar yadda suka yi niyyar yi mana. 


Na ce idan ta aikata haka haƙiƙa ta cuce ni domin 'yan uwana ne, sannan na tuna mata akan farkon haɗuwarmu da alƙawarin da ta yi na saka mini da alherin da na yi mata. Da ta ji haka, sai ta ɗauke ni ta yi sama da ni, ba ta ajiye ni ba sai tsakiyar gidana a garinmu. Na je wurin da muka binne kuɗin nan na tone su na ɗauka. Na je kasuwa na karɓi rumfata ga wanda na ba wa haya da niyyar washe gari in koma ga kasuwanci na.


Da dare ina shiga gida sai na tarad da waɗannan karnuka guda biyu a ɗaure cikin sarƙa. Su na gani na sai suka fara kuka suna kewaya ni, ni ban sani ba. Sannan sai ga matar nan tawa ta bayyana. Ta ce, “Waɗannan 'yan uwanka ne.” Na tambaye ta wane ne ya aikata haka gare su? Ta ce da ni ita ce ta aika da su wajen 'yar uwarta ta mayar da su haka, ba za su koma ga siffarsu ta asali ba sai bayan shekara goma. Wannan shi ne hukuncin laifin da suka aikata maka.


Tsoho mai karnuka ya ci gaba da ba wa ifiritu da sauran mutanen nan labarinsa. Ya ce, ya kai ifiritu, shugaban sarakunan aljanun duniya, yau shekara goma ke nan da faruwar wannan abu, yanzu haka ina kan hanyata ta zuwa wajen 'yar uwar matata da waɗannan karnuka domin mayar da su ga siffarsu ta asali, sai na ga wannan mutum zaune da wannan tsoho mai barewa, na tambayi labarin zamansu nan, suka gaya mini. Wannan shi ne labarina da waɗannan karnuka. Idan wannan labari ya zama abin al’ajabi a wurinka, ina so ka ba ni sulusin jinin wannan Tajiri da ya kashe ɗanka.


Ifiritu ya yi mamaki da wannan labari matuƙar mamaki. Ya ce haƙiƙa wannan labari naka abin rubutawa ne a ajiye shi domin mutane su dinga karantawa har zuwa ƙarshen lokaci. Na ba ka sulusin jinin wannan mutum.


Sai tsoho mai alfadara ya matso ya ce, ya kai shugaban aljanu, haƙiƙa labarina duk ya fi na saura ban mamaki da al’ajabi, amma ba zan gaya maka ba sai idan ka yi alƙawarin za ka ba ni sulusin jinin wannan mutum. Ifiritu ya amince. Tsoho mai alfadara ya fara bayar da labarinsa mai cike da ban al’ajabi da kuma mamaki.


Tsoho na uku mai alfadara ya gabata zuwa ga ifiritu ya fara labarta wa Ifiritu hikayarsa, ya ce, ya sarkin aljanu, babbar tutar aljanu, ka sani cewa wannan alfadara da kake gani matata ce. Wata rana na yi tafiya zuwa fatauci, na bar matata a gida har tsawon shekara guda ban dawo ba. Ran nan sai Allah ya yi dawowata gida. Ya yin da na iso garinmu a cikin dare, sai na nufi gidana. Ina shiga ɗakina sai na sami matata kwance da wani baƙin mutum a kan shimfiɗata, suna zance suna raha da dariya tare da sumbatar juna.


Yayin da ta ga na yi tsaye ina kallonsu cike da mamakin wannan abu da na gani, na daga cin amana, sai ta yi sauri ta tashi ta ɗauko wani ruwa a cikin kasko, ta yi wani zance na sihiri a cikin ruwan, sannan ta watsa mini shi a jiki ta ce, juye daga siffarka ta mutum ka koma ga siffar kare. Nan take na zama kare. Suka kore ni waje cikin duhun dare, suka mayar da gida suka rufe.


Bayan matata da mutumin nan sun kore ni daga gidana, sai na kama hanya ina tafiya ban san inda nake nufa ba. Ban gushe ba ina tafiya har na kai cikin kasuwa. Na sami wata rumfa nan na kwanta kafin gari ya waye. Ashe rumfar nan ta sarkin fawa ce.


Da gari ya waye, mutane sun fara fitowa kasuwa, sai ga sarkin fawa ya iso ga rumfarsa. Yayin da ya gan ni ina cin ƙasusuwan da aka watsar, sai tausayina ya kama shi, ya ja ni ya shiga gidansa da ni domin ya ba ni abinci.


Muna shiga gidan sarkin fawa sai ‘yarsa ta yi sauri ta rufe jikinta da mayafi, ta ce da mahaifinta, baba, me ya sa ka shigo mana da namiji cikin gida? Sai mahaifin ya tambayeta, ina namijin?


Ta ce, wannan kare namji ne, matarsa ce ta sihirce shi, ni, ina da ikon kuɓutar da shi. Yayin da ubanta ya ji zancenta, sai ya ce, na roƙe ki domin Allah, ‘yata, ki kuɓutar da shi!


Ta riƙi wani kasko da ruwa a cikinsa, ta yi zance bisa gare shi, ta kwara ruwan bisa gare ni, ta ce, fita daga wannan sura ya zuwa ga surarka ta farko! Nan da nan kuwa na koma mutum, kamar yadda na ke da farko.


Na yi godiya gare ta, na ce da ita, ina son ki sihirce mini matata tamkar yadda ta sihirceni. Sai ta ce, to. Ta ba ni wani ruwa, ta ce, in je in watsa mata shi yayin da take barci, in ambaci duk surar da nake so ta koma, za ta koma nan da nan. Na karba, na yi godiya, na nufi gidana.


Bayan na shiga gidan, sai na iske matata tana barci. Na yayyafa ruwa bisa gareta, na ce, ki fita daga wannan sura ya zuwa ga surar alfadara! Nan da nan ta zama alfadara. Ita ce wannan alfadara da kake gani, ya shugaban ifiritai. Yayin nan tsoho ya waiwaya gare ta ya ce, ko wannan gaskiya ne? Alfadara ta rauda kanta, wato ta ce, na’am.


DUBA WANNANHikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (1)


Yayin da tsoho mai alfadara ya gama zanta labarinsa, aljani ya yi raurawa da farin ciki, ya ba shi sulusin jinin tajiri da ya wanzu, sannan ya ɓace a cikin iska yana mai farin ciki da waɗannan labarai da ya ji, ya bar Tajiri da tsofaffin nan.


Tajiri ya yi wa tsofaffin nan godiya a kan kuɓutar da shi da suka yi daga hannun ifiritu. Sannan kowa ya kama gabansa.

Monday, 21 October 2024

Karanta Hikayar Tajiri Da Ifiritu (1)

Karanta Hikayar Tajiri Da Ifiritu (1)

A zamanin da, a wani babban gari, an yi wani babban attajiri, mai yawan dukiya, mai yawan tausayi da taimakon talakawa.


Hikayar Tajiri Da Ifiritu
Hoto: Gutenberg


MarubuciBukar Mada


Wata rana attajirin nan ya fita bayan gari yawo shi kaɗai domin shan iska, sai ya tsaya domin ya huta a ƙarƙashin wata itaciya mai sanyin inuwa. Ya fito da gurasa da dabino da ruwa daga cikin jakarsa, domin ya ci ya kuma sha ruwan kafin ya wuce gaba.


Bayan ya gama cin gurasa sai ya ɗauko dabino yana ci. Yana cikin cin dabinon nan sai ga wani Ifiritu (aljani), mai girman jiki, tamkar itaciyar kuka, mai tsayin gaske, tamkar itaciyar rimi, da jajayen idanu, tamkar garwashin wuta. Ya fito riƙe da takobi a hannunsa, ya ce da wannan attajiri, tashi na kashe ka tamkar yadda ka kashe ɗana.


Tajiri ya ce, “Ta yaya na kashe ɗanka?”


Ifiritu ya ce, “Yayin da ka ci dabino ka yi jifa da ƙwallon ya sami ɗana a kirji har ya faɗi ya mutu. Babu makawa yanzu in ɗau fansa, in kashe ka tamkar yadda ka kashe shi.”


Tajiri ya ce, “Ka sani ya kai wannan Ifiritu akwai bashi mai yawa a kaina. Ka bar ni in tafi gida, tsawon shekara guda, in bai wa dukkan mai haƙƙi haƙƙinsa, sannan in komo nan ka aikata abin da ka yi nufi a kaina, za ka same ni mai cika alkawari, haka Allah ya kaɗɗara.”


Ifiritu ya yarda da bukata tasa.


Tajiri ya komo gida, ya faɗa wa iyalansa da danginsa da abokansa dukkan abinda ya faru da shi, suka yi ta kuka, kuma ya biya dukkan mai bin sa bashi haƙƙinsa. Bayan shekara guda ya koma inda suka haɗu da Ifiritun nan ya zauna yana jiran fitowarsa.


Yana nan zaune yana jiran abinda zai same shi, sai ga wani tsoho tafe, ya na jaye da barewa, da igiya a wuyanta. Ko da tsohon nan ya iso wurin tajirin nan sai ya ce masa, “Bawan Allah, me ya zaunar da kai wannan wuri? Hala ba ka san cewa wannan wuri matattarar aljanu ba ne?”


Tajiri ya kwashe labarinsa da Ifiritu ya faɗa wa tsoho. Tsoho ya ce, haƙiƙa labarinka akwai ban al’ajibi da tausayi a cikinsa. Lalle ba zan bar nan ba sai na ga abinda zai kasance a gare ka. Ya sami wuri ya zauna.


Suna nan zaune, sai ga wani tsoho tafe ya na jaye da karnuka, baƙaƙe guda biyu. Tsoho mai karnuka ya yi sallama gare su. Bayan sun gaisa, ya tambaye su labarin zamansu wannan wuri wanda ya ke matattarar aljanu. Suka faɗa masa abinda ya ke faruwa. Da ya ji haka sai ya ce, lalle ba zan wuce ba har sai na ga abinda zai faru tsakanin Tajirin nan da Ifiritu. Ya sami wuri ya zauna.


Tsohon nan mai karnuka bai gama zaunawa ba, sai kuma ga wani tsoho tafe akan wata alfadara ramammiya. Da tsoho mai alfadara ya iso ya yi musu sallama, suka gaisa sannan ya tambaye su dalilin zamansu a wannan bigire. Suka labarta masa abinda ke faruwa. Shi ma ya ce ba zai wuce ba sai ya ga ƙarshen wannan al’amari. Ya sami wuri ya zauna.


Tajiri da tsofaffi na nan zaune sai suka riƙa jin wata irin hargowa, mai cike da rugugi da tsawa da iska mai tsanani tana kaɗawa, ƙasa kuwa kamar za ta tsage saboda rugugi da ƙugi. Ƙura ta tashi ta murtuƙe ko’ina, ta rufe hasken rana, ba a ganin komai tamkar a tsakiyar dare.


Yayin da hargowar nan ta lafa, ƙura ta yaye wuri ya koma dai dai, sai mutanen nan suka ga Ifiritu a tsaye da takobi zararre a hannunsa, idanunsa jawur tamkar garwashin wuta. Ya fizgo Tajirin nan daga cikinsu ya ce, tashi in kashe ka tamkar yadda ka kashe ɗana, sanyin zuciyata, farin cikin rayuwata.


Tajiri yana kuka yana kururuwa da hargowa, tsofaffin nan su ma suka fashe da kuka domin tausayin Tajiri. Sai tsohon nan na farko, mai barewa ya matso kusa da Ifiritu, ya durƙusa ya ce, “Ya kai wannan Ifiritu, Sarkin Sarakunan aljanu, da za ka tsaya in ba ka labarina da wannan barewa da nake tare da ita, da ka ji labarin abin al’ajabi wanda ba ka taɓa jin irinsa ba, amma sai idan ka yi alkawarin za ka ba ni wani yanki na jinin wannan Tajiri.”


Ifiritu ya ce, “Na yarda idan ka ba ni wannan labari na ga ya kasance abin al’ajabi da mamaki zan ba ka sulusin jinin wannan mutum.”


Tsoho mai barewa ya yi godiya ya fara ba Ifiritu da sauran mutanen da ke wurin labarinsa, da abin da ya kasance a gare shi tare da wannan barewa, kamar haka:


Tsoho na farko, mai barewa ya ce, ka sani ya kai wannan ifiritu, cewa wannan barewa ta kasance ‘yar baffana ce, na aure ta tun tana ƙarama. Mun zauna tsawon shekara talatin da ita amma Allah bai ba mu haihuwa ba. Sai na sayi kuyanga, na mayar da ita sa-ɗaka, Allah kuwa ya sa na haifi ɗa namiji tare da ita. Yaron nan ya kasance kyakkyawa, mai kyawun sura abin so da ƙauna ga kowa.


Bayan yaron nan ya kai shekara goma sha biyar, sai tafiya ta kama ni zuwa wani birni daga cikin birane. Na ɗebi guzuri na dukiya mai yawa domin ban san iyakar kwanakin da zan yi ba a wannan tafiya. Na tafi, na bar ɗana da uwarsa, da kuma matata, 'yar baffana a gida.


Wannan mata tawa, wadda ita ce wannan barewa da kake gani, ya kai wannan ifiritu, ta kasance masaniya akan bokanci da sihiri kala-kala tun tana ‘yar ƙarama. Don haka bayan tafiyata sai ta sihirce yarona ta mayar da shi bajinin sa, uwarsa kuma ta mayar da ita saniya, ta aika da su wurin mai yi mini kiwon dabbobina a daji, aka saka su a cikin garken shanu.


Bayan wani tsawon lokaci na dawo daga tafiyar da na yi, sai ban ga ɗana da uwarsa ba, na tambayi matata inda su ke. Sai ta ce da ni, ai bayan tafiyarka, kuyangarka ta mutu, ɗanka ya gudu ban san inda ya tafi ba. Wannan labari ya sa ni cikin baƙin ciki da ƙunar zuciya har tsawon shekara guda.


Lokacin da sallar layya ta zo, sai na aika wa makiyayina da ke ƙauye da ya aiko mini da saniya mai ƙiba kuma mai maiƙo domin in yi layya da ita. Wannan mata tawa sai da ta san yadda ta yi dabarar da ta sa makiyayin nan ya aiko mini da sihirtattar saniyar nan, wato kuyangata, uwar ɗana, a matsayin saniyar da zan yanka.


Da aka kawo saniyar, na tashi na cire rigata, na ɗauki wuƙa, bayan an kayar da ita an ɗaure ƙafafunta, na nufe ta da niyyar in yanka ta domin yin layya. Sai ta riƙa kuka da harbe-harbe, kamar za ta yi mini magana, amma babu baki. Sai tausayi ya kama ni, na ba wani yaron gidana wuƙar na ce ya yanka mini ita, ni kuwa na koma cikin ɗaki.


Bayan an yanka saniyar nan, wadda ta kasance kuyangata ce aka sihirce, da aka feɗe ta sai aka tarar ba ta da nama da mai sosai, daga fata sai ƙasusuwa, ni kuwa niyyata in yi layya da dabba mai nama da mai da yawa. Ganin haka sai na sake aika wa makiyayin nan da ya kawo mini wani bajini/bajimi mai nama da mai sosai. Matar nan tawa kuma ta sa aka kawo mini ɗan nan nawa da ta sihirce shi ya zama sa.


Yayin da aka zo da shi, yana gani na, sai ya tsinke igiyar da aka ɗauro shi da ita, ya rugo zuwa gare ni, ya yi kwance a gabana, kuma ya tashi yana kuki yana kuka, yana kewaya ni. Tausayinsa ya kama ni. Na ce, a mayar da shi a zo mini da saniya mai ƙiba da mai. Amma matata kuwa sai ta ce, ka yanka wannan sa domin yana da ƙiba kuma yana da mai sosai. Allah ya sa ban biye shawararta ba, domin tausayin shi ya riga ya kama ni. Aka mayar da shi.


Bayan kwana biyu, ina zaune, sai ga makiyayin nan nawa ya zo wurina, ya ce, ya shugabana, na zo ne in faɗa maka abin farin ciki da albishir. Na ce da shi, na’am, ina saurarenka.


Makiyayi ya ce mini, ya kai maigidana, na kasance ina da wata ‘ya tawa masaniyar sihiri, tun tana ƙarama ta ke a hannun wata tsohuwa, kakarta, wadda ita ce ta koya mata sihiri. Jiya bayan na koma da bajimin san nan da ba ka yanka ba, sai na tarar da ‘yar nan tawa ta zo gida domin bukin Sallah.


Yayin da na shiga da sa gida, ko da ‘yar nan tawa ta gan shi, sai ta rufe jikinta ta ce mini, ya babana, ta yaya za ka shigo mana da namiji, baligi, cikin gida? Bayan kuwa shi ba muharraminmu ba ne? Sai ta fashe da kuka. Na ce da ita, ina namijin da na shigo muku da shi? Sai ta daina kuka, sai kuma na ga tana dariya. Sai na tambayeta, me ya sa ki kuka? Me ya sa kuma yanzu kike dariya?


Ta ce da ni, wannan bajimin da kake tare da shi, ɗan shugabanmu ne, Tajiri, amma an sihirce shi ne, shi da mahaifiyarsa, kuma matar ubansa ce ta sihirce su. Amma abin da ya sa ni kuka shi ne, mahaifinsa ya sa an yanka uwarsa bai sani ba. Amma abin da ya sa ni dariya shi ne, zan iya kuɓutar da shi na mayar da shi ga siffarsa ta mutum, amma sai na yi sharaɗi da mahaifinsa.


Makiyayi ya ci gaba da faɗa mini cewa, na yi al’ajabi gayar al’ajabi, ban yi barci ba har hudowar asuba, domin na zo na sanar da kai wannan labari, ya shugabana.


Yayin da na ji wannan zance na makiyayina, ya kai wannan ifiritu, sai na ce da shi ya tashi maza mu tafi gidansa domin na ji sharaɗin da 'yarsa take so kafin ta mayar mini da ɗana siffarsa ta mutum.


Da muka iso, ‘yar makiyayi ta tare mu da murna, ta gaishe ni cikin ladabi da girmamawa. Da ɗan nan nawa ya gan ni sai ya taso ya zo ya kwanta a gabana. Na ce da ‘yar makiyayi, shin labarin da mahaifinki ya gaya mini ko gaskiya ne. Ta ce, na’am ya shugabana. Wannan bajimi da kake gani ɗanka ne.


Na ce da ita, idan kika kuɓutar da shi zan ba ki dukkan dukiyata da ta ke hannun mahaifinki. Sai ta yi murmushi, ta ce, ka sani ya shugabana, ba ni da kwaɗayi akan dukiyarka, zan kuɓutar da ɗanka amma akan sharuɗɗa guda biyu: Na farko, ka yarda na auri wannan ɗa naka, na biyu ka bar ni in sihirce wadda ta sihirce ɗanka da kuyangarka, ni ma in ɗaureta cikin sihiri tsawon rayuwarta. Idan ka yarda da waɗannan sharuɗɗa, yanzu zan mayar wa ɗanka da siffarsa.


Na ce, na amince da waɗannan sharuɗɗa, kuma na ƙara miki da dukiyar da ke hannun mahaifinki, ‘yar baffana kuwa, watau matata, ki yi duk abin da kika ga dama da ita.


Yayin da ta ji zancena ta ɗauki tasa, ta cika da ruwa, sannan ta yi wasu karance-karance ta tofa a cikin ruwan nan, sannan ta yayyafa wa bajimin sannan, ta ce, idan Allah ya halicce ka, ka kasance bajimi, to ka ci gaba da zama bajimi, idan Allah ya sa sihirce ka aka yi, ka juya ga siffarka ta asali, da yardar Allah Maɗaukakin Sarki. Nan take sai ya juye ya koma mutum, kamarsa ta asali. Na aura masa ‘yar makiyayin nan, ita kuma ce ta sihirce ‘yar baffan nan tawa zuwa wannan barewa da kake gani, ya kai wannan ifiritu.


Idan wannan labari nawa ya kasance mai ban al’ajabi a gareka ina son ka ba ni sulusin jinin wannan Tajiri da ya kashe ɗanka ba tare da ya sani ba.


Ifiritu ya ce, haƙiƙa wannan labari akwai abin al’ajabi a cikinsa, don haka na ba ka sulusin jinin wannan mutum.


DUBA CI-GABAN ANAN: Karanta Hikayar Tajiri Da Ifiritu (2)


Daga nan sai tsoho na biyu mai karnuka ya matso wurin Ifiritu, ya ce ni ma ina da labarin da zan ba ka akan waɗannan karnuka da kake gani, amma sai idan za ka ba ni sulusin jinin wanan mutum.


Ifiritu ya ce, faɗi labarinka mu ji. Tshoho mai karnuka ya fara labarinsa kamar haka:........


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don samun ci-gaban wannan ƙayatacciyar hikayar da sauran zafafan hikayoyi duk a kyauta.

Tuesday, 15 October 2024

Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (7)

Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (7)

Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan domin su gaisa da baƙonsa, ga mamakinsa sai ya ga ƙofar ɗakinsa a buɗe, babu baƙo babu alamunsa, amma kuma ga dabbobinsa nan da kuma hajarsa ta mai.


Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in Kashi Na 7
Hoto: Zu 09/iStock Photo 


Yana nan tsaye yana mamakin inda baƙonsa ya shiga, sai ga kuyangarsa Murjanatu ta fito, ta durƙusa ta gaishe shi.
Ya tambaye ta, ko ta ji motsin baƙonsa? Domin tagar ɗakinta na kallon farfajiyar gidan ne, duk wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu za ta iya ji daga cikin ɗakinta. Ta ce da Ali Baba, "Maigida zo ka duba da idonka, ka ƙara yi wa Allah godiya, da ya kuɓutar da kai." Ta ja shi har zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya buɗe ɗaya da kansa ya ga abin mamaki.
Ali Baba ya buɗe jakar mai ɗaya, sai ya ga mutum a ciki, riƙe da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro, Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su da tafasasshen mai." Ta kwashe labarin abin da ya faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa gidansu lamba, da kuma yadda ta zo ɗibar mai a cikin hajar baƙo, ta gane mutane ne a ciki, da yadda ta ƙona su da mai, da kuma yadda ta ga shugaban ɓarayi ya buɗe gida cikin dare ya arce, da ya gano cewa an kashe masa mutane.


Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata albishir da wata kyauta mai tsoka, amma bai faɗa mata ko mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani bawansa mai suna Abdallah.


Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya faɗa masa abin da ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke cikin gidan su gina ƙaton rami mai faɗi da zurfi, wanda zai iya ɗaukar ɓarayin nan duka, su rufe su ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawansa Abdallah suka gina ƙaton rami, Allah ya taimake su akwai danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha wata wahala ba wurin haƙa ramin.

Suka riƙa cicciɓo gawar ɓarayin nan, ɗaya bayan ɗaya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da ƙasa suka rufe. Ali Baba ya gargaɗi bawan nan, duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje. Jakan ɓarayin nan kuwa, sai Ali Baba ya riƙa ɗibar biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba, har suka ƙare.

Shugaban ɓarayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali Baba, sai ya koma maɓoyarsu a cikin daji. Ba da jimawa ba, kaɗaici da kuma tsoro suka lulluɓe shi, ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kaɗai a cikin daji ba. Saboda haka sai ya ɗebi wani abu daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani baƙon alhaji, ya koma cikin gari.
Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi masa iso gun Sarki, ya ce shi baƙo ne, sunansa Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki. Sarki ya sa dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma yanzu babban ɗansa ne, saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da uku, a ciki.


Koja Husaini ya tare cikin sabon gidansa, lokaci-lokaci kuma ya kan koma maɓoyarsu ya ɗebo wani abu daga cikin dukiyarsu, wadda yanzu ta zama mallakarsa shi kaɗai. Amma ya kan yi taka-tsan-tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja hankalin mutane su fara zarginsa. Kullum zuciyarsa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya kashe Ali Baba.

Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da maƙocinsa, ɗan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su yi ta hira a tsakaninsu.


Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa ɗansa ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na zaune a ƙofar gidansa, ƙarƙashin wata bishiya, yana hutawa. Da ganinsa, nan take Koja Husaini ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan ɗansa, bai ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da ana kallonsa.

Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya yi tafiyarsa. Ba a daɗe ba kuma sai ga ɗansa ya fito, da ya ga Koja Husaini zaune a ƙofar gidansa, sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro, wanda ya zama tamkar abokinsa a halin yanzu, ɗan Ali Baba ne, babban maƙiyinsa a duniya. Don haka sai ya raya a zuciyarsa, bari ya ja shi a jika, wata ƙila ta sanadiyarsa zai cimma burinsa na kashe Ali Baba.

Tun daga wannan rana sai alaƙar Koja Husaini da Ɗan Ali Baba ta ɗauki sabon salo. Koyaushe Koja Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Ɗan Ali Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaƙu da juna suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.

Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida, watau iyalansa da barorinsa kawai. Da Ɗan Ali Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban abokinsa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja Husaini ya yi matuƙar farin ciki a ransa, damar da yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar ƙoƙarin sa ya keɓe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan iyalansa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata sharɓeɓiyar wuƙa ya sulle ta a cikin rigarsa, suka tafi.

Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Ɗan Ali Baba ya gabatar da abokinsa ga mahaifinsa, sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba; Ali Baba da matarsa, Ɗan Ali Baba da abokinsa Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan ciye-ciye da shaye-shaye.

Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganinsa, nan take ƙwaƙwalwarta, mai kama da kwamfuta, ta gane shi. Shugaban ɓarayn nan ne ya sake dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba, ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin hanyar da za ta yi maganin wannan ɓarawo.

Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa bakinsa da abin da aka tanadar. Tuni kuma Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe wannan ɓarawo. Ta raɗa wa bawan nan Abdallah, ya ɗauko dundufarsa ya fara kiɗa ita kuma za ta yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk lokacin da yake buƙatar nishadi. Abdallah ya jawo dundufarsa ta kiɗa, ya fara kaɗawa a hankali, dama kuma gwanin kiɗa ne, ita kuma Murjanatu ta tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.

Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin maza, ta kan riƙe wata 'yar ƙaramar wuƙa a hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo gaban mutum ta ɗaga wuƙar nan kamar za ta daka masa ita a zuciya, sai ta juya wuƙar ta daka masa mariƙin wuƙar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi. Duk ƙasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta Koja Husaini ya san da haka.

Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa, sai ta ɗauko 'yar ƙaramar wuƙa ta riƙe a hannunta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin ranta. Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kiɗa, Abdallah, ta ɗaga wuƙar kamar za ta daɓa masa ita, sai ta daɓa masa ƙotarta, aka yi tafi. Ta wuce wurin Ɗan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban ɓarayi, ta ɗaga wuƙar nan, ta tattara iyakar ƙarfinta a hannunta mai wuƙar ta kirɓa masa ita a ƙahon zuciya. Nan take ɓarawo ya faɗi ƙasa yana shure-shure har ya mutu.

Ko da Ali Baba da ɗansa suka ga wannan ɗanyen aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili ba, sai suka taso mata, hankalinsu a tashe, suka far mata da faɗa, don me za ta kashe baƙon da suka gayyato, laifin me ya yi mata. Murjanatu ta dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane ne wannan baƙo, sannan ta ce musu, "Duk da yake ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida ba, amma na tabbata manufarsa ba ta alheri ce ba."

Da suka duba jikin shugaban ɓarayi, sai suka samu sharɓeɓiyar wuƙa sulle a cikin rigarsa. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu ta kuɓutar da rayuwar Ali Baba daga halaka. Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin da ya ɓoye mata a cikin zuciyarsa, wanda kuma ya taɓa furta mata.

Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na 'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma idan kin yarda ina so ki amince da ɗana ya zama mijinki." Sannan ya juya wurin ɗansa ya ce da shi, "Ya kai ɗana, na san da cewa ba za ka ƙi amincewa da zaɓina ba, ka amince na aura maka Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami galaba a kaina, dama ya yi ƙoƙarin yin abota da kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da buƙatarsa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kuɓutarmu gaba daya."

Murjanatu da Ɗan Ali Baba suka amince da junansu. Bayan 'yan kwanaki aka ɗaura musu aure, aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amma ya 'yanta ta kuma ya aurar da ita ga ɗansa, da ma yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu wanda ya san abin da ya faru.

Ali Baba bai ƙara komawa maɓoyar 'yan fashin nan ba, domin yana gudun ya haɗu da sauran ɓarayin nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da aka shekara ya ga babu wata barazana da ɓarayin nan suka ƙara yi masa, ran nan sai ya shirya ya faki idon mutane ya ɗare saman dokinsa, ya nufi dajin. Ya ɗebo dukiyar ya aza kan dokinsa ya hawo ya dawo.

Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga lokaci zuwa lokaci, yana ɗebo dukiyar da ɓarayin nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk lokacin da ya je ya kan yi sauri ya ɗiba ya dawo don tsoron kada sauran ɓarayin biyu su tarar da shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci gaba da kasuwancinsa a kasuwa, don haka babu wanda ya san sirrunsu. Ya zamana babu mai arziki duk faɗin ƙasar kamar Ali Baba.

Ya yi zamansa shi da iyalinsa cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba su.

ƘARSHE 


Ga waɗanda ba su samu damar karantawa ba tun daga farko ba, to su kwantar da hankalin su, su latsa nan don komawa ga shafin farko na labarin ko kuma nan....



Alhamdulillah! Wannan shi ne ƙarshen hikayar Ali Baba da Ɓarayi Arba'in, wacce muka kwashe tsawon makonni bakwai muna kawo muku.

Idan Allah ya kai mu litanin mai zuwa, za mu zaƙulo muku wata hikayar mai daɗi da kuma ilmantarwa, wacce ma ta fi wannan.

Allah ya kai mu.

Tushe/Asali: Waziri Aku

Sunday, 15 September 2024

Hikaya Mai Daɗi Ta Wani Sarki Da Bafatake

Hikaya Mai Daɗi Ta Wani Sarki Da Bafatake

Wannan hikaya an ciro tane daga littafin khalila wa Dimna, wani daɗaɗɗen kundin labaru masu faɗakarwa wanda Masani Bipdai ya rubuta tun a zamanin mulkin Annabi Zulƙarnaini. 


Hikaya Mai Daɗi Ta Wani Sarki Da Bafatake
Hoto: Steemit

MarubuciSadiq Tukur Gwarzo


Hikayar ta fara da cewa "A wani gari mai suna Baudamana, an yi wani attajiri mai kyauta. Babbar sana'arsa ita ce fatauci, inda yake sayen kayayyaki daga gari zuwa gari.


Sarkin wannan gari na Baudamana inda attajiri yake yana sane da ayyukan karimcin da wannan attajiri ke yi ga jama'a, don haka ma ya janyo shi a jiki tare da naɗa shi matsayin galadima a fadarsa.

 

Wannan attajiri, ya kasance mai yalwar hannu. Kyautarsa ta game sarakuna da talakawa. Idan ya so, yana iya sanyawa a tara masa talakawa ya yi ta raba musu dukiya, idan kuma ya so, yana iya gayyatar manyan attajirai da sarakuna walima tare da gwangwajesu da kyaututtuka.


Rannan bikin 'yarsa ya taso, sai attajiri ya gayyaci sarkin garin da wasu manyan mutane walima a gidansa kamar yadda ya saba. Wuri ya yi wuri, manyan baƙi duk sun zazzauna akan kujerun alfarma da aka tanadar musu. Sai kwatsam attajiri ya hango wani bawan sarki a kan wata kujera wadda aka tanadarwa manyan mutane, ya harɗe yana shan ƙamshi abinsa. Wannan abu sai ya baƙanta masa zuciya. Tun daga nesa ya daka masa tsawa, sannan ya umarci askarawansa su yi waje da shi.



Aka yi taro lafiya aka gama. Ashe bawan nan na Sarki ya yi matuƙar kufula da cin mutumcin da Attajiri ya yi masa, duk da shi ma ya san ya yi kuskure. A ranar da abin ya faru ma, bai iya bacci ba. Yana ta ƙulla Makircin da zai yi don ɗaukar fansa akan attajiri.


Sai bawan ya fara rayawa a ransa "Idan da zan san hanyar da zan bi don Sarki ya wulaƙanta Tajirin nan, da na ɗauki fansa ta. To amma ta yaya ƙasƙantaccen mutum iri na zai iya ɗaukar fansa akan mutum mai daraja irin sa?".


A ƙarshe dai, wata dabara ta faɗo masa a rai.


Bayan wasu 'yan kwanaki, wannan bawan ya shiga ɗakin Sarki shara da sanyin safiya, a lokacin sarki na kan gadonsa yana bacci, amma da alamun baccin da sarki yake yi ba mai nauyi ba ne.


Da bawan nan ya gane haka, sai kuwa ya fara maganganu ƙasa-ƙasa shi kaɗai, yana cewa "Duniya da abin mamaki take, yanzu a ce har Attajirin bafatake ya sami sukunin rungumar matar sarki?..ooo."


Caraf kuwa sai a kunnen sarki. Ya yi firgigit ya farka, da yake mutum ne shi mai kishi. Ya kalli bawan nasa fuskarsa a murtuƙe ya ce " da gaske kake?  Ka taɓa ganin attajiri ya rungumi matata?"


Bawa ya ɗuka gaban sarki, ya ce "ya shugabana, kwana biyu ba na samun yin bacci, yanzu ma gyangyaɗi ke ɗiba ta. Idan ka jini na faɗi wata magana da ba ta gamsar da kai ba, ka yafe ni".


Shikenan, Sarki bai sake cewa bawa uffan ba. Sai dai tunane-tunane da suka yawaita zagaya masa a zuciya.


'Wannan bawan nawa ba shi da shamaki a gidan nan, shi ma wannan attajirin haka, wataƙila akwai abin da bawan ya hango yake tsoron faɗa mini'


Daga nan fa sai sarki ya cika da kishi, ya fara yanke alaƙoƙinsa da attajirin nan. Kana ma, ya ce da dakarunsa kada su ƙara barin attajiri ya shigo masa gida.


Duk abin da ake Attajiri bai sani ba, wata rana ya yi niyyar zuwa kawowa Sarki wata kyauta bayan ya dawo daga fataucinsa, da ya zo shiga sai masu jiran ƙofa suka ce sam ba zai shiga ba, suka sanar masa da cewa sarki ya hana su yin haka gare shi.


Wannan abu ya yi matuƙar girgiza attajiri. Sai ya shiga kokwanton dalilin da yasa sarki ya ɗauki wannan hukunci a gare shi. 


Ashe bawan sarkin nan yana bisa bene, kuma duk yana hangen abinda ke faruwa. Daga can nesa ya ɗaga murya yana cewa "kai dakaru, wannan Bafatake abin so ne ga sarki, mutum ne mai daraja, zai iya sanyawa a ɗaure mutum ko a sake shi kamar yadda ya sanya aka kore ni a ranar da ake walima a gidansa. Ku kula da kanku, abin da ya same ni na iya samunku"..


Dajin haka, sai wannan attajiri ya gano bakin zaren. Ya ɗaga kansa ya kalle shi, sannan ya yi murmushi. Bai ƙara ce musu uffan ba, ya juya abinsa zuwa gida.


Attajiri ya yi tunanin matakin da ya kamata ya ɗauka. Har wata zuciyar ta shawarce shi da ya haifarwa da sarki matsala a mulkinsa kasancewar shi mutum ne da kowa ke so a garin, amma sai ya tuna da cewa shi matafiyi ne, ya zaga duniya, ya san illar rikici, don haka zaman lafiya ya kamata ya nema ba tashin hankali ba.


Bayan wani lokaci sai ya aika aka kira masa wannan bawa na sarki. Ya yi masa karramawa sosai da kyaututtuka, sannan ya nemi gafarar sa akan abinda ya yi masa a baya.


Wannan abu ya farantawa bawan sarki rai. Har ma yake cewa attajiri "Ranka ya daɗe, na gafarta maka, ka girmamani, ka kuma nemi afuwa ta. Don haka zan yi ƙoƙarin juyo da hankalin sarki gare ka ta yadda za ku ci-gaba da mu'amala kamar yadda kuka saba"

 

Abinda aka yi kenan, kashe gari da sassafe bawa ya shiga ɗakin sarki shara kamar wadda aka yi kwanakin baya, sai ya hau surutunsa ƙasa-ƙasa yana cewa "a'aha, muna da wawan sarki a garin nan, kalli yadda ya ci kabewa ya zubar a ɗakinsa. Abar da ake miya amma ita yake ci.."


Nan ma dai sarki ya yi wuf ya juyo gare shi, ya ce "kai wanne irin wawa ne, a ina kaga na ci kabewa na watsar a ɗakin nan?"


Bawa ya faɗi gaban sarki yana neman yafiya, ya bada uzurin rashin bacci ne ke sa shi yin gyangyaɗi idan yana aiki kamar yadda ya bayar a baya.


Tun daga nan, sai sarki ya gane ƙarya bawan yake faɗa a duk maganganunsa, sai kuma ya yi da-na-sanin hukuncin da ya ɗauka akan Attajiri ba tare da ya yi bincike ba. Nan take ya sa a kira masa shi don ya nemi afuwar sa, ya kuma yi masa tanajin kyauta gagaruma.


Ƙarshen hikayar kenan.


Darussa:


Kada ka raina mutum duk kaskancinsa.


kada ka kai kanka matsayin da ba naka ba.


Kada ka rinƙa saurin yarda da magana tare da ɗaukar mataki.


Kada ka yi girman kai wajen neman afuwar laifin da ka aikata.