Monday 23 July 2018

Hotuna da Cikakken Tarihin Hadiza Gabon: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Jaruma Hadiza Gabon

Tura Wannan Zuwa Ga
An haifi Jarumar kannywood Hadiza Aliyu Gabon a ranar 1 ga watan Yuni na shekara ta alif dari tara da tamanin da tara (1 June 1989) a garin Libreville na kasar Gabon.


Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da suna “Hadiza Gabon” wata Jaruma ce a masana’antar fina finan Hausa ta Kannywood a Najeriya.

Yawa yawan mutane a cikin masana’antar Kannywood da ma wajen ta baki daya kan kalli Hadiza Gabon a matsayin “Sarauniyar Mata” . Ta kasance mace mai kamun kai a masana’antar gami da girmama na gaba da ita. Bugu da kari ba’a taba samun ta da wani ashararanci ba irin wanda akan zargi fitattun Jarumai mata da shi.

Hadiza kan yi shiga irin ta mata a addinance. Sannan kuma bata fitar da tsaraicin ta a waje. Wajen tafiyar ta al’amura kuwa na rayuwa, Hadiza Gabon ba’a bar ta a baya ba, inda shima ta kasance daya tilo.

Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo masu yawa a masana’antar Kannywood. Sannan ta kasance Jakadiya ta kamfanin
MTN a Najeriya.

Bugu da kari ta kasance mace ta farko da ke tafiyar da gidauniya mai zaman kanta a masana’antar Kannywood mai suna Gidauniyar HAG (HAG Foundation) wanda kan bayar da tallafi ga yara kanana da mata marasa galihu a fannin ilimi, ciyarwa, lafiya da dai sauran su.Kuruciya, Rayuwar Gida da ta ‘Yan Uwa
Jaruma Gabon haifaffiyar garin Libreville ce na kasar Jamhuriyar Gabon. Mahaifinta Malam Aliyu ya kasance dattijo dan asalin Gabon. Ta bangaren mahaifiyar ta kuwa ta kasance Bafulatana daga jihar Adamawa a kasar Najeriya. Tayi karatun piramare gami da sakandare a kasar Gabon inda tayi jarrabawar gaba da sakandare da sha’awar zama lawya inda ta fara karatun digirin ta na farko a kan fannin lauyanci.

Hadiza ta fice daga neman ilimin lawyanci a shekarar farko saboda wadansu dalilai da suka hana ta cigaba.Amma daga bisani ta samu kammala karatun difloma a harshen Faransanci wanda kuma hakan ya bata damar koyarwa a wata makaranta cikin harshen na Faransanci.

Hadiza Gabon na da ‘yan uwa wadan da suka hada da Malam Aliyu (mahaifi), Hajiya Halima (mahaifiya), Muhammad Umar (dan uwa), Aisha Umar (dan uwa), Zakari Ali (dan uwa), Issa Ali (dan uwa), Hamidou Ali (dan uwa), Hachimu Ali (dan uwa),
Muhammad Ali (dan uwa), Dahirou Ali (dan uwa) da kuma Adam Ali (dan uwa).Kasancewa Jaruma

Hadiza Gabon ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood a yayin da ta shiga garin Kaduna daga jihar Adamawa bayan samun sha’awa da tayi a citin masana’antar ta Kannywood tare da wata ‘yar uwarta. A wannan lokaci ne ta samu haduwa da Jarumi Ali Nuhu inda ta nemi taimakon sa gami da hadin kai domin zama Jaruma. Hadiza ta samu fita a shirin fim ta farko a rayuwar ta a cikin fim din Artabu a shekara ta 2009.


Lambar Yabo da ta Girma

Hadiza Gabon ta samu lambobin yabo dana girma kala kala a masana’antar Kannywood. Ciki harda Fitacciyar Jaruma a masana’antar Nollywood a shekara ta 2013 a fim din ‘Babban Zaure’ da kuma Jaruma a taron ban girma na biyu a masana’antar Kannywood wanda akayi a shekarar 2014 a fim din ‘Daga Ni Sai Ke’ . Mai Girma Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso shima ya samu baiwa Jaruma Hadiza Gabon lambar yabo a shekara ta 2013.

Jaruma Hadiza Gabon ta dauki lambar girmamawa daga Kannywood AWA 24 Film & Merit Award a shekarar 2015 a fim din ta na ‘Ali Yaga Ali’ .


 Sai kuma taron African Hollywood Awards shima data samu na fitacciyar Jaruma a shekara ta 2016 a fina finan Hausa na nahiyar Africa a cikin yaren Hausa.

Hukumar Gidan Malamai da aka fi sani da Kano State Senior Secondary Schools Management Board ita ma ta samu karrama Hadiza Aliyu Gabon a shekara ta 2016 a bisa gudummawar da ta kam bawa ilimi a Jihar Kano karkashin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sai kungiyar Start Up Kano ina ta karrama Hadiza a shekara ta 2016 a bisa babbar gudummawa akan bayar da jari ga marasa aikin yi.


Aikin Gidauniyya

Hadiza Gabon ta fara aikin kafa gidauniya a shekara ta 2015 wanda kuma a cikin shekara ta 2016 tayi mata ragista.

Gidauniya mai suna HAG Foundation anyi ta ne domin tallafawa mata da kananan yara marasa galihu a fannin ilimi, lafiya da abinci. Hadiza Gabon ta kasance mace ta farko a masana’antar Kannywood da ta fara bayar da irin wannan gudunmawa.

A watan Maris na 2016, Hadiza Gabon ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira a Jihar Kano wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa dasu inda ta raba kayayyaki da suka hada da kayan abinci da sutura dama sauran ababan more rayuwa.

Takaitaccen tarihin Fati Washa da Hotunan ta: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Fati Washa-Karanta Yanzu Kaji

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: Muryar Arewa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user