Tuesday 24 July 2018

KARANTA YANZU KAJI: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA AL'UMMAR AREWACIN KASAR NIGERIA - WASIKAR TA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga
Ashe Dan AREWA Zai Iya Zagin Shugaban Da Ke Kishinsa?


Da yawa daga cikin masu biye dani zasuyi mamakin yau na zaɓi rubutu nane da harshen Hausa. Saboda haɗarin da yankin arewa ke fuskanta musamman a yanayi da muka tsinci kawunan mu ayau.

Marubuci: Dr. Tukur Alhaji Musa (Babban Malami A Jami'ar Jihar Yobe)

Tabbas wautarmu tana kusa da abinda yafaru da Iraƙi ko Libya. Muna amfani dason zuciya da hassada don kawai wata buƙata tamu.

Wai yaushe ne arewacin nan ta farfado daga bala'i da musiba? Ashe, gajen haƙurinmu ba zai janyo mana tawaya da ƙasƙanci ba?

Ashe, yau ɗan arewa ka iya zagin shugaban dake da kishinsu? Ashe zamu zaɓi tumasanci da bambadanci akan aƙida da kishi?

Wasu marasa kishin arewa, maciya amana sun bullo da wata sabuwar jam'iyya dan ciwa shugaba Buhari mutunci, alhali munyi saurin mantawa da cewar ba mutanen kirki bane su? Maciya amanar ƙasane dakuma arewa.

Ankiramu Almajirai, mabarata kai har malamin addini anan ƙasar yakiramu jahilai !!!

Muyi taka tsantsan da mutane irinsu Buba Galadima waɗanda burinsu itace cin amana ba kishin yankinsu ba.

Ana nuna mana ƙiyayya ta hanyar kisa da sunan fulani da makiyaya. Duk ƙasarnan babu inda tarzoma, kisa, shaye-shaye, Barace-barace, tumasanci da bangar siyasa sai Arewa ???

Wallahi in har muka bari wannan-damar ta ƙuɓuce mana, babu wanda zamui kuka da shi sai kawunan mu. Inhar muka bar Wannan damar ta fice daga hannunmu, zamu kasance daga azzalumai wadanda suka cuci kawunansu Dana jikokinsu.

Duk rabe-rabe na jam'iyya daga ƴan Arewa yake fitowa. Daga ƴan jar hula, sai ƴan ƴaɗa kiyayya da parpaganda ,saikuma marasa kishi dason cin amanar ƙasa !!!
Tabbas, mu shafawa gemunan mu ruwa kafin mu yiwa kawunan mu sakiyar da babu ruwa.

Ta hakan ne zamuzan al'umma masu kishi, masu tsari da ɗabi'a.
IN KUNNE YAJI......

Karanta a Natse Kaji: Wasika Mai Zafi zuwa ga Dr rabi'u Kwankwaso-Daga Adnan Mukhtar

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user