Sunday 24 May 2020

KARANTA KAYATATTUN SABABBIN KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUKATAN MASOYA NA BARKA DA KARAMAR SALLAH

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin
MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku labaran Soyayya har ma  da Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zukatan Masoya , A Yau mun kawo muku wasu daga cikin Rubutattun Sakonnin Soyayya na BARKA DA  SALLAH  (KARAMAR SALLAH) masu ratsa zuciyoyin masoya.

Kalaman Soyayya

Kada Ku Manta dayin Subscribe na Channel din  mu a Youtube MURYAR HAUSA24 TV ko kuma ku Biyo mu a shafin mu na Yanar Gizo a www.MuryarHausa24.Com.NG

Menene Kauna?

Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci, domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna ba’a mutuwa akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali, ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba haka take ba, ko anyi nasarar samun abin kaunar ko ba’ayi ba, ana cigaba da masa fatan alheri kamar yadda kake masa a baya.

Kuma ita kauna bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani bai kwaranyar da ita.

Galibi abinda ke kawo kauna ɗabi’une, wato halayyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga kaunar shi.

RANAKUN BIKIN SALLAH.

Wannan lokaci ne na musamman, rana ce ta farin-ciki ga dukkan masoya.

Ranakun bikin sallah, lokuta ne da kasantuwa ta a tare da ke ka iya kai wa ga sanadin ƙaruwar yalwatuwar murmushin fuskata.

Rashin kasancewar mu a tare a cikin wannan rana ya haifar min da damuwa a zuciyata, amma duk da haka ba zan gaza ba wajen furta miki cewa, Ina Son Ki.

Barka Da Sallah

ABUN DA NAKE TINAWA.

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Rwatsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

A dukkan lokacin da na kalli sararin samaniya, na ga tarin taurari sun yi wa samaniya ado, suna ta faman haske, babu abun da nake tinawa face, tattausan murmushin ki da ke haska fuskata a dukkan lokacin da muke tare.

Fatan kina nan lafiya?

Barka Da Sallah.

FARIN-CIKINA.

Ana gane kyawun shuka ne idan har an gama ta da taki.

Tayaya za a gane sama idan har babu ƙasa?

Kamar haka ne, farin cikina zai yi wuyar bayyanuwa matuƙar ba ma tare da juna.

Na kan shiga damuwa a dukkan lokacin da na duba gefena ban gan ki ba.

Yau rana ce ta farin ciki gare ni da kuma ke da sauran danginmu, a dangane da haka ba zan yi sanya ba wajen ƙara tinatar da ke cewa Ina Son Ki.

BaRKa Da SaLLah.

BA ZAN IYA MANTAWA DA KE BA.

Kin zamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na taɓa haɗuwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya mantawa da ke ba har abada.

 Ina fata da burin kasancewar mu tare a daula mafi tsari da kyawun burgewa wato Aljanna.

Cikin nishaɗi da yalwatuwar murmushin fuska nake furta miki cewa Barka Da Salla!

FATANA DA BURINA.

A gare ki nake samun bargo, a dukkan lokacin da sanyi ya rufe ni.

Ina samun tsaro, a dukkan lokacin da hatsari ya tinkaro ni.

Ina samun farin ciki a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni.

Fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna.

 Ina Son Ki Mata ta Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.

Barka da Sallah

MATSAYINKI A GARE NI.

A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata, zan iya yin amfani da kalmomi irin su…….hmm ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni.

Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai ƙara sanar da ke cewa, ina son ki.

Fatan Za A Cigaba Da Gudanar Da Bukukuwan Salla Lafiya.

Barka Da Sallah Masoyiyata.

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

HAKIKA SOYAYYAR KI DAGA ALLAH MADAUKAKIN SARKI TAKE A GARE NI.

Bana Manta lokacin da Lecturer din mu yake yi mana Dictation Kowa yana rubutawa haka ni ma ina rubutawa.

Bansan cewa ba abinda Malam yake faɗa nake rubutawa  ba , sai bayan ya kammala na duba naga saƙonnin soyayya nake rubutuwa Izuwa gare ki sahiba ta , alokacin ne na tabbatar da irin son da nake yi miki.

Haƙiƙa ke ta daban ce a gare Ni hakan yasan ya naji ina sonki.

Wasu suna cewa bamu da ce ba Ni kuma ina cewa ƙarya ne inaji a jiki na Wata Rana zaki zamo tawa Insha Allah.

Barka da Sallah

KO DA A CE MUN TSUFA.

Shi so na gaskiya ba ya taɓa canjawa daga yadda ya kafu a zuciya tun asali, sai dai a samu masoyan sun canja daga yadda suke tun fari.

Ko da a ce mun tsufa, idaniyata ba za ta daina ganinki a matsayin wannan kyakkyawar macen ba, zinariya mai kyawun sura.

Barka Da Sallah

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

KI DAURE KI AMSA KIRA NA.

Sahiba ta Halima Na shiga damuwa a lokacin da kika nesanta da ni, ki taimaka ki dawo gare ni tun kafin zuciyata ta kara afkawa cikin hali na damuwa.

Yau ranar farin ciki ce a gare ni da dukkan sauran musulman duniya gimbiyata a saboda haka nake kara jaddada miki cewa, ina kaunar ki.

BARKA DA SALLAH.

LAMBUN FUREN SOYAYYA.

Zan kasance cikin baki furen soyayya a dukkan lokacin da muka haɗu, matuƙar na samu tukuicin murmushinki a kan haka, to fa tilas na gina mana gida cikin da’irar lambu mai cike da tarin furanni masu kyawun launi da daɗin ƙamshi.

 Ina Fatan Kin Yi Salla Lafiya?

FARIN CIKI DA DAMUWA.

Anya abu ne da zai iya faruwa, bayyanar farin ciki da kuma damuwa a cikin zuciya guda a kuma lokaci ɗaya?

To ni dai a halin yanzu na kasance cikin irin wannan yanayi.

Ina farin ciki domin kasantuwar wannan lokaci na bikin sallah ƙarama.

 Ina kuma cikin damuwa ta dalilin rashin kasantuwar mu tare a dai-dai wannan lokaci na farin ciki.

Ina Son Ki ina kuma Fatan Kun Yi Salla Lafiya?

Barka da Sallah


ARZIKINA NAKI NE.

Shin Masoyi ya ta Halimatut Sadiya ko kin san Ina da burin mallakar tarin dukiya duk domin na yi amfani da ita wajen hidimta miki?


Da ganin na inganta rayuwarki, ya kasance mun rayu tare cikin jin daɗi da walwalar rayuwa.

Barka Da Sallah


MAI SA’AR RAYUWA.

Wannan rana ce ta musamman kamar yadda kike ta musamman a wurina.

A saboda haka nake son bayyana miki cewa, da akwai wani sirri da yake tare da ke, wanda shi ke sa wa na manta da dukkan wata damuwa na ji ni a matsayin mai sa’ar rayuwa, a dukkan lokacin da muke tare.

Tabbas kina da baiwa.

Nagode Allah da samun ki a cikin rayuwata, domin kuwa kin haskaka duniyata.

Barka Da Sallah.

ZAN ZAMO MIKI GARKUWA.

Alkawari ne na ɗauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matukar muna a tare da juna, ina fatan nan da wani ɗan lokaci ki tabbatar da hakan bayan kin zamo mata a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa.

 Halimatut Sadiya ki huta lafiya.

Ki kula min da kanki.

Ina son ki.

BARKA DA SALLAH.

FATAN ZAN SAMU ABUN DA NAKE NEMA?

A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke muradin samu daga gare ki?

Ba komai bane face ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa ba.

Ina son ki.


BARKA DA SALLAH.

TAURARUWATA.

Na kan ga wani haske ya gifta a dukkan lokacin da na rintse idanuna.

Haske ne irin na tauraruwar da haskenta ke haske maraya da karkara.


Wannan tauraruwa ba kowa bace face KE!

(ina nufin Masoyiya ta Halimatut Sadiya).

Ina son ki, ina kuma cike da burin son kasancewa a raye  a tare da ke har abada.


Barka Da Sallah


RANAR GAMO.


So wani abu ne da……..hmm ko don ba sai na bayyana miki hakan ta hanyar amfani da harufan rubutu ba, da sannu za ki fahimci hakan a dukkan lokacin da idanuwan mu suka yi gamo da juna.

Ina Son Ki kuma Ina ƙaunar ki.

Ki sha shagulgulan sallah lafiya.

 Barka Da Sallah

Kalaman Soyayya


NA MATA.......

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

INA SON KA!

M. Kabir Son ka na haskawa a cikin zuciyata tamkar yadda tauraro ke haske a bisa  sararin samaniya.

Ina son ka fiye da yadda kalmomi za su kwatanta hakan a rubuce.

Fatan ka yi salla lafiya?DAMA A CE HAKAN YA KASANCE A ZAHIRI.A kullum na kan yi mafarkin ga mu a tare cikin ɗaki tare da ‘ya’yan mu, shin ko hakan yana nufin za mu mallaki juna kenan?

Tabbas idan hakan ya kasance bani da wani sauran buri a rayuwata face na yi fatan kasancewa a tare da kai a gidan aljanna.

Ina son ka M. Kabir , ka kula min da kanka karda ka bari kowacce kazamar yarinya ta raɓe ka.

Ni ce taka Halimatut Sadiya.KAI NE A CIKIN BACCINA.


Tun bayan haɗuwata da kai na manta da wani abu mai suna damuwa.

Shin wai tayaya ma zan kasance cikin damuwa bayan kai ne a cikin furuci na, kai nake gani a cikin baccina, da kai nake kwana a cikin zuciyata da kai nake tashi.

 Ina son ka masoyina.

Barka Da Sallah

BUGUN ZUCIYATA.

 M. Kabir Muhammad Kai ne sirrin rayuwata, masoyina na gaskiya, kai ne bugun zuciyata, da kai zan ɓata lokaci mafi muhimmanci a rayuwata.

Ina son ka, so na gaskiya.

Barka Da Sallah.


ZAN WADATA KA DA JIN DAƊI.


Ka kusanta da ni, zan wadatar da murmushi a saman fuskarka, zan yi ƙoƙarin wadata ka da jin daɗi daga cikin nau’ikan ababen jin daɗin rayuwar duniya.

Ina sonka.

Barka Da Sallah

TSANTSAR SOYAYYA.


A halin yanzu kawai kana ganin kaso ne mafi ƙanƙanta daga cikin irin son da nake yi maka, amma lokaci na nan zuwa da zan nuna maka tsantsar soyayya mara misaltuwa, bayan mun yi aure.

Ba zan taɓa mantawa da kai ba dai-dai da ƙiftawar ido, saboda INA SON KA!

 Barka Da Sallah

KAI NE MURADINA.


Kamar yadda furanni ke buƙatar ruwa domin su tsira, mutum ke buƙatar abinci domin ya rayu, dare ke buƙatar duhu domin bayyanar da kansa, kamar haka ne nake son kasancewa tare da kai domin na yi rayuwar farin ciki.

Kai Ne Muradina.

Ina Fatan ka yi Salla Lafiya?

Barka Da Sallah

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

NA MAGIDANTA MA'AURATA MAZA DA MATA.

FARKON GANIN KI.

Abar ƙaunata Halimatut Sadiya, A farkon fara ganinki kin ɗauki hankalina ta yadda na kwana ina tinani da mafarke-mafarke a kanki.

Bayan na isa gare ki, sai rayuwata ta canja izuwa ta musamman mai cike da farin ciki.

Bayan na mallake ki, kin zama mata ta na zamo miji a gare ki, sai ya kasance bana son nesanta da ke dai-dai da kowace motsawa ta agogo.

Ina son ki mata ta, burina mu mutu tare, mu tashi mu rayu tare a Aljanna.

Barka Da Sallah

NA YI BACCI A GEFENKI.

Ni abun da na ɗauka so shi ne, yadda nake kwana shimfiɗe a bisa kafaɗunki na yi bacci kwance a gefenki, na rintse idanuwana na kuma ganki cikin baccina.

Hmm! Kar da ki damu da wannan azancin nawa mata ta.

Yau rana ce ta farin-ciki da nake ƙoƙarin ƙara bayyana miki adadin yadda nake son ki.

Barka Da Sallah

NUTSUWATA.

A dukkan lokacin da duhu ya mamaye idanuwana, ya kore ganina, kallonki a kusa da ni, ko jin sautin muryarki, shi ne abun da ke dawo min da dukkan abun da na rasa na daga nutsuwata.

Ina son ki mata ta fiye da yadda baki ko wani sashi na jiki zai iya bayyana hakan.

Ina Mai Yi Miki Barka Da Sallah

IDAN KA NESANTA DA NI.

M. Kabir Muhammad Mijina uban ‘ya’yana.

 Da yawan mutane na sanar da ni cewa na bika sau da ƙafa, suna furta min na yi maka biyayya domin na samu Aljannata, amma me ya sanya ba sa tinatar da ni kan cewa rayuwar farin-ciki da walwala zata yi min wuyar samu matuƙar na rasa ka a rayuwata?

Na gane hakan ne ta yadda idan ka nesanta da ni nake shiga cikin damuwa har sai zuwa lokacin da ka dawo gare ni na gan ka, sai na samu farin ciki.

A yau cikin wannan lokaci na bikin sallah nake ƙara sanar da kai cewa,  Ina Son Ka!! Maigidana uban 'yva'ya Na.

Barka Da Sallah


SO NA GASKIYA.

Abun da nake son samu a rayuwata shi ne SO.

So na gaskiya.

Samun so na gaskiya daga wurin kyakkyawar mace zinariya wato ke.

Ina matuƙar so da ƙaunarki.

Ki Huta Lafiya.

Barka Da  Sallah.

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

MATSAYINKA A WAJENA.

A yau a cikin wannan lokaci na farin ciki da walwala ga Musulman duniya, nake son bayyana maka adadin yadda nake son ka ta hanyar yin amfani da kalmomi na musamman kamar……

Hmm ko don dukkan abun da zan furta maka na san ka riga ka sani.

Kalma ta yi kaɗan ta bayyana cikakken matsayinka a wajena.

Ina son ka mijina tamkar yadda kake so na.

Ina kuma yi maka, Barka Da Sallah


KIRA GA MASOYA A WATAN RAMADANA.

Yi wa masoyiyar ka kyauta da kayan shan-ruwa hakan zai ƙara janyo maka martaba da ƙarin girmamawa daga wajen ta da kuma ‘yan uwanta.

Tabbas, wannan al’ada ce da ta shahara wajen ƙara dan ƙon soyayya a tsakanin saurayi da budurwa a ƙasar Hausa.

Wannan ita ake kira da Toshin barka da shan ruwa.

Ke ma kuma za ki iya bawa saurayin naki kayan shan ruwa, domin samun lada da ƙaruwar soyayya a tsakani ta hanyar faranta ransa.

Kar da ku manta ana fara aikawa da kayan shan ruwan ne tun goma ga azumi.

Ana kuma bada abubuwa ne nau’in su kayan marmari ko abubuwan sa wa a baka.

Misali: Ayaba da gwanda da lemo da abarba da madara da bambita da sauransu.

Allah ya bar soyayya har ya zuwa bayan aure Amin.

Kalaman Soyayya


ME NE NE SO DA KAUNA.?

So da kauna, wani shauki ko hali ne wanda ke kama da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a aikace .


Hmm nasan wasu zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da soyayya.

 Tirƙashi...

To ka sani Madarar da zumar ilimin soyayya tatacce daga addinin musulinci, yake.

Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take tatatta, kuma amintatta.

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

Wacce babu yaudara ko ha'incin juna tsakanin masoya.

DUBA WADANNAN:

Download Sababbin Kalaman Soyayya Na Barka da Sallah Masu Ratsa Zukatan Masoya Na Zamani Audio/Video

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA MAZA DA MATA NA ZAMANI

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

Kalli Shagalin Bikin Yaro dan Shekara 17 da Yarinya 'Yar Shekara 14...Latest Video

KARANTA ME NE NE MA'ANAR KALMAR KAUNA?

Za Ka/Ki iya amfani da waɗannan Kalaman Soyayyar ga Masoyiyar Ka haka Ke ma zaki iya amfani da waɗannan Kalaman Soyayyar ga Masoyin Ki, amma  Dan Allah Kada kayi amfani da shi domin Yaudarar wata Ruhi , Ka tuna da wanda yake kallon ka ako ina kake (ALLAH SWT).

ALLAH YASA MU DA CE AMIN.

Kada Ku Manta dayin Subscribe na Channel din  mu a Youtube MURYAR HAUSA24 TV ko kuma ku Biyo mu a shafin mu na Yanar Gizo a www.MuryarHausa24.Com.NG


Zaku iya samun mu a shafin mu na yanar gizo a www.MuryarHausa24.Com.NG

Domin samun wasu , Mungode.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user