Tuesday 26 May 2020

Shin Ko Ya Dace Na Zabi Budurwa A Ranar Sallah?

Tura Wannan Zuwa Ga
Yawancin mutane sun yarda da cewa ba dabara bace mutum ya zabi budurwa ranar Sallah, saboda a ranar ne kowa da kowa ya kure a dakarsa wajen cin ado babu yadda za ai ka gane wacce take da kyau da tsafta idan ba da Sallah bane!


Zaben Budurwa A Ranar Sallah

Marubuci: Sahibul Kalam

Ni kuwa sai nawa ra’ayin yasha ban-ban!

A tawa fahimtar ranar Sallah shine ranar da ya kamata mutum ya zabi abokiyar zama!

Dalili na akan hakan kuwa shine ranar Sallah itace ranar da kowa ya kure hikimarsa wajen ganin ya fita fes-fes, yana walkiya da kyalkyali da sheki, hakan ya nuna kenan ita wacce ka zaba din wannan shine irin kyawunta na asali wanda Allah ya halicce ta dashi, ba wanda zaman Nijeriya ya mayar da ita ba.

Saboda haka ashe kenan indai zaka sama mata abubuwan yin kwalliyar to haka zata zamo kullum kamar tauraruwar daren goma sha hudu.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA BABBAN KALUBALEN DAKE GABAN SAMARI

KARANTA DALILIN DA YASA MATAR BAHAUSHE TAFI MAFI YAWAN MATAN KASASHEN DUNIYA GATA A DUNIYA

KARANTA ALAMOMI 10 DAZAKA FAHIMCI MACE TANA SON KA

Idan kuwa ya kasance ba ranar Sallah ne ka zaba ba, to fa ba zaka gane ba ko zata iya fin haka idan tayi kwalliya ko kuma iya kyawunta kenan oho!

WANNAN SHINE RA’AYINA, KU KUMA MABIYA SHAFIN MURYAR HAUSA24  ME NE NE NAKU RA'AYIN AKAI??? AIKA RA'AYIN KA/KI A EMAIL DIN MU A Muryarhausa24@gmail.com


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user