Tuesday 8 October 2019

KARANTA DALILIN DA YASA MATAR BAHAUSHE TAFI MAFI YAWAN MATAN KASASHEN DUNIYA GATA A DUNIYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Matar Bahaushe Ta Fi Kowace Mace Gata A Duniya Amma Mafi yawan Mugayen Mata a duniya matar Bahaushe Ce Ta Fi Gasa Wa Namiji Aya A Hannu.

Yadda Rayuwar Mata take Kasancewa a wasu Kasashen

Marubuci: Abdurrashid Adamu Ahmad (Dan Baiwa)

08060606050

A iya binciken da na yi matar Malam Bahaushe tana da gata sosai sama da sauran matan kabilunmu, domin Malam Bahaushe bai yarda ya ga matarsa ta fita tana aikin karfi ko wahala ba.

Shi duk talaucin sa ya fi so matar sa ta zauna a gida shi ya fita ya yi aikin karfin ko wahalar domin ya nemo musu abin da za su ci shi da ita da yaransu.

Da wuya ka ga matar Malam Bahaushe tana zuwa daukan ruwan da zasu sha ko nemo abin da zasu ci, ko daukar nauyin karatunta ko daukar nauyin gidanta da na yaranta ko da kuwa mai hali ce.

Malam Bahaushe idan mai hali ne ma hatta girki da wanki ko wanke-wanke ya haramtawa matarsa sai dai ya dauko masu yi mata hidima... Ita sai dai ta kwanta ta ci ta sha tayi ibada sai kuma kula da tarbiyyar yaransu kawai... Ko Unguwa za ta akwai direba idan ba mota a ba ta kudin a dai daita sahu.

Amma wallahi abin takaici da haushi sai kaji Malam Bahaushe kullum yana kuka da matarsa... Sam ba ta bashi had'in kai kullum cikin tashin hankali da daga masa hankali take... Da yawa daga cikin ire iren wadannan matsalolin ne kan sa wani namiji ƙarin aure ko Allah zai sa ya dace ko kuma yayi tunanin tsallakawa ya auro wata ƙabilar ta daban wacce yake tunanin zai samu zaman lafiya da ita.

Wai kuwa matanmu na ƙasar hausa suna lura da yadda matan wasu kabilun ke fama da aikin ƙarfi domin daukar nauyin mazansu da yaransu? Ta dalilin aikin karfin da suke yi har jikinsu ya murde ya zama irin na maza?

Kuma duk da haka suna girmama mazajensu duk da irin yadda suke gallaza musu kuwa?

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

KARANTA SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA DA MASU NIYYAR YIN AURE

KARANTA DALILAI 6 DAKE SA MATA KASHE MAZAJEN SU

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

Wasu matan kabilun fa su fita kiwon dabbobi ko yin itacen girki, wasu suyi aikin kafinta ko daukar bulo ko gini, wasu da ciki ko goyo suke wannan aikin kuma su samo kudin su dawo gida su girka abinci su ci su da mazajensu da yaransu... Ke kuma matar Malam Bahaushe me ki ka sani game da irin wadannan aiyukan wahalar?

Ni dai wallahi na kasa fahimtar me yake damun wasu daga cikin matan Malam Bahaushe ne, ko dai dadi ne yayi musu yawa?


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode









TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user