Tuesday 23 July 2019

KARANTA SHAWARA ZUWA GA MA'AURATA DA MASU NIYYAR YIN AURE

Tura Wannan Zuwa
Bayanin da zai biyo bayan taken wannan rubutun yana da nauyi, don haka ayi hakuri da kalmomin da za'a ji, muhimmancin dake tattara da bayyana bayanin a fili yafi boye bayanin saboda amfanar al'umma gaba daya.

Shawara ga Masu Aure da kuma Masu Niyyar Yin Aure

MarubuciDatti Assalafy

Sannan yana daga cikin manufar shafin Datti Assalafiy shine wayar da kan al'umma game da abinda zai amfane su a rayuwa da zamantakewa, da fallasa asirin abubuwan da zasu cutar da al'umma gwargwadon abinda zamu iya.

Na karanta wata doguwar takadda wanda wani kwararren Likitan mata ya wallafa yake bada shawara domin ma'aurata su kiyaye akan abinda yake matukar cutar da lafiyar su a rayuwar aure ba tare da sun sani ba.

Likitan ya bayyana cewa duk ma'auratan da suke yin amfani da yawun bakin su (saliva) a gurin jima'i to su yi gaggawar denawa, saboda yawu yana kunshe da wasu sinadarai masu karfi da suke taimakawa wajen narka abincin da ake ci, wanda idan suka shiga cikin farjin mace suna iya haddasa mata mummunan infection mai matukar wahalar magani, likitan yayi bayanin cewa, wasu infection na iya yin shekara 5 a farjin mace kafin ya bayyana illarsa.

Wato yana daga cikin dabi'ar mafi yawa daga cikin ma'aurata, su kan yi amfani da yawu wajen karawa jima'i ko saduwa armashi, saboda akwai matan da haka Allah Ya halicce su suna da karancin ni'ima, ni'ima da ake bayani anan shine; wani ruwa ne fari mai santsi da yake fitowa daga gaban mace a lokacin da sha'awa ta motsa, ko kuma a lokacin da ake jima'i .

To akwai matan da basu da irin wannan ni'ima, akwai matan da kuma ana cikin jima'i sai ni'imar ta dinga daukewa, daga nan sai su fara jin zafi, anan ne ma'auratan suke saka yawu domin al'aurar tasu tayi santsi a samu abinda ake so, to irin wannan yawu da ake sakawa illa ne sosai ga farjin 'ya mace .

Mutanen da sukayi sabon aure sunfi fuskantar daukewar ni'ima a yayin jima'i, akwai mata sabbin amare da basu taba sanin 'da na miji ba, to saboda tsoron zafin buda hanya a kwanakin amarci ni'imar su tana saurin daukewa, sai suyi amfani da yawu, ko man shafawa ko dai wani abu mai kama da haka, saka yawu kuskure ne balle mayukan shafawa da sauransu da ake sarrafawa da chemicals.

Shiyasa kashi 90 cikin 100 na mata ma'aurata da suke amfani da yawun bakinsu ko wasu mayuka a yayin jima'i suna dauke da infection kala-kala ba tare da sun sani ba yana cutar da lafiyan su tare da rage musu armashin jima'i, wanda kan iya haddasa cin amanar aure ko ma rabuwa.

Ga matan da suke fama da matsalar rashin ni'ima ko daukewar ni'ima yayin jima'i, to ya dace su nemi shawarar kwararrun masana a wannan fanni, amma tabbas suyi gaggawan dena amfani da yawu ko wasu mayukan shafawa a lokacin jima'i .

Don haka ma'aurata da sauran samari da suke sha'awar yin aure a kiyaye, sannan ya dace a yada wannan shawara saboda amfanar al'umma gaba daya.

Allah Ka tabbatar mana da alheri Ka magance mana matsololin gidan aure Amin.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA DALILAI 6 DAKE SA MATA KASHE MAZAJEN SU

KARANTA MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH

KARANTA KAƊAN DAGA CIKIN ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA DA KUMA SANYIN GABA

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user