Tuesday 31 July 2018

KAƊAN DAGA CIKIN ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA DA KUMA SANYIN GABA - KARANTA YANZU KAJI

Tura Wannan Zuwa
Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i (STDs/STIs) .ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. 


Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mutum - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kaɗai a lokacinda suka ga wasu alamomi da basu saba gani ba (baƙi) ga al'aurarsu, misali , kamar: feshin ƙananan ƙuraje ko ƙaikayi, ko fitar farin ruwa, jin raɗaɗin zafi daga maraina da sauransu. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin maza zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan akwaita.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba'a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu bainar mutane (game gari) :

1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.
2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).
3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko ɗorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
4. Jin zafi wajen yin fitsari.
5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.
6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.
Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba:
1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
2. Zafi da kumburin maraina
3. Zafi da kumburi daga kwararo da fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
4. Zazzaɓi

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza:

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci "Chlamydia" (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin ƙarfin mazakuta idan ciwon yayi ƙamari ba'a magance shi ba. Cutar maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin ƙarfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken ƙarfin al’aurar namiji ko raguwar ƙarfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miƙewar al’aura yayinda ake buƙatar fara jima’i. Bugu da ƙari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima'i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al'aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala, inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar "Chlamydia", cutace daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini, murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau'in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin 'dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu saboda itama anfi yaɗata ta jima'i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin 'dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI, duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko

(1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu

(2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haɗari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haɗari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali.

Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani, haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

Domin neman ƙarin bayani ko neman magani/waraka sai a
kira +234808 402 8794 (Domin neman tura Magani )

+2349079201777 (Domin neman appointment da Malam) - Yaran Malam

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user