Monday 30 July 2018

Takaitaccen Tarihin Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria : Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Marigayi Sheikh Albani Zaria

Tura Wannan Zuwa Ga

Ash-Sheikh Albani Zaria yayi karatu a hannun Malamai da dama anan gida

 Nigeria da kuma Saudiya.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

An haifi Ash-Sheikh Albani Zaria ne a watan Rabiu Thani 1379 dai dai da 27 Sept 1960, a cikin garin Muciya Zaria, Sabon Garin Kaduna, Najeriya.

Ya karanta kwas din Information Technology a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Yola, Jihar Adamawa. Ya yi sakandaren Barewa College da ke Zariya.

Kafin rasuwarsa dalibi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda yake digiri-na-biyu a kwas din Fannin Sarrafa Wutar Lantarki.

Albani shi ne shugaban makarantar Science Academy da ke Gaskiya a Zariya. Shi ne kuma shugaban cibiyar Daruth Hadith s-Salafiyyah Center a Tudun Wada, Zariya.

Ya yi fice wajen kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram, wadanda suke tayar da kayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

TAKAITACCEN TARIHIN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA DANGANE DA ABUN DA YA SHAFI NEMAN ILIMINSHI DA KUMA MALAMAN SHI.

Malam ya taso tun yana yaro da son ilimi kamar yadda wani malamin shi ya siffanta shi da cewa: “Albaniy tun yana 'Karami da angan shi ina kaje; karatu, ina zaka; karatu, me kake yi; karatu, me ka gama; karatu.

Mahaifiyar shi mai Suna Saudatu ita ta fara bashi 'karfin guiwar karatun addini na musamman, domin itace wadda ta fara siyar da akuyar ta, ta bashi kudin ya siyo littafin Saheehu Muslim inshi na farko. Har ila yau mahaifiyarshi ta taba 'daukan shi tun yana 'karami ta kaishi gurin wasu malamai a cikin garin Kano domin su karantar dashi Karatun addini da zummar cewa 'danta ya zama Malami.

A 'bangaren karatun Al-Qur'ani; Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara karatun Allo ne a cikin anguwar mucciya dake Zaria. A inda ya sauke Qur'ani saukar Farko ruwayar warsh 'kira'ar Nafi'u a hannun Mallam Mato da Alarama Mallam Abubakar.

A 'bangaren Larabci kuwa Ash-Sheikh Albani Zaria ya halarci wani karatu na wata goma sha takwas (18 months) a 'karkashin wani tsarin karatu da marigayi Gaddafi ya kawo Nigeria, a 'karkashin Jagorancin jami'ar Libiya a shekara alif dubu 'daya da 'dari tara da tasa'in. Babban Malami, marigayi Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, shi ya danka musu takardar shedar kammala karatun, kuma sai da yaba Albani Zaria wata takarda na jinjinawa ta musamman.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

Dangane da sauran karatuttukan addinin musulunci kuma.

Ash-Sheikh Albani Zaria yayi karatu a hannun Malamai da dama anan gida Nigeria da kuma Saudiya.

Kadan daga cikin malaman da yayi karatu a hannun su anan gida Nigeria sun kasance kamar haka; Dr Aminuddeen Abubakar Kano (Mai makarantar Kwali), Ash-Sheikh Sani Yakubu Zaria, Shehu Umar (Malami ne a Jami'a), Alkali Mallam Haruna Ishaq Zaria.

 Daga bisani Ash-Sheikh Albani Zaria (Rahimahullah) ya tare a hannun wani mutumin india mai suna Dr AbdulRahim Muhammad Muslim Khan wanda malami ne dake koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Mallam Muhammad Muslim Khan ya karantar da Albani Zaria littattafai masu yawa. A bangaren ilimin hadisi wannan malami Muhammad Muslim Khan ya karantar da Ash-Sheikh Albani Zaria littafin tadriburra'wi da musdala'ul hadith.

A bangaren sauran littattafai kuma wannan malami ya karantar da Albani littafin Sifatu-Salatin Nabiy da kuma littafin Sharhus- Sunnah na Alhafiz Al-Bagawiy.

Daga baya a lokacin da Ash-Sheikh Albani Zaria ya fara kasuwanci yana samun kudi, malam ya kasance yakan sayi tiket na jirgi musamman dan yaje 'Kasar Saudiyya yayi karatu a matsayin shi na 'dalibi mai niman ilimi bawai a matsayinshi na 'dalibin jamiatul Islamiyya ba.

Mallam yayi karatu a gaban Dr Muhammad Amin dake jamiatul Islamiyya dake madina, a inda ya koyi 'kira'ar Qur'ani 'kira'a bakwai ruwaya goma sha hudu.

Mallam Ya yi karatu a gaban Sheikh Uthaimin karatu sosai musamman ta fannin ilimin tafseerin Al-Qur'ani mai girma.

Mallam yayi karatun Aqeeda karatu sosai a hannun Addoktur Assuhaimi da professor Ali Nasir Faqihi wadanda dukkaninsu malamai ne a jamiatul islamiyya dake madina Kulliyatud-Da'awa wa usuluddeen.

Mallam yayi karatu a wurin mallam Tuwaijiri wanda ke karantarwa a Daruul-Hadeethisil Khairiyya dake Saudiyya.

Mallam yayi karatu a wajen Sheikh Zarban Al-gamidy, wanda shi ne tsohon Bursar (shugaban 'bangaren kudi) a jami’ar Madina.

Mallam yayi karatu a hannun Sheikh Abdullahi Bn AbdulRahman Alu Bassam (mai littafin taysirul Allam).

Mallam yayi Karatu a gaban Professor Samir wanda 'dalibi ne na Sheikh Nasiruddeen Albani.

Mallam yayi karatu a hannun Muhammad ibn Ali ibn Adam Al Ethiopy wanda shi kuma mutumin 'kasar Ethiopia ne.

Akwai malaman jami’ar Madina da yawa wadanda malam yayi karatu a gaban su, amma ba’a matsayin shi na 'dalibi a jami’a ba, A’a, a matsayin shi na 'dalibi wanda ya kai kanshi koyon ilimi a wurin su.


Mu muka kashe Sheikh Albani Zaria - Shugaban Ƙungiyar Boko Haram Shekau

Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin cewar ita ce ta hallaka sanannen Malamin addinnin musulunci na Zaria, Sheikh Mohammed Auwal Adam Albani.

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta fitar a 19 Fabrairu 2014, inda Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya yi jawabi.

An dai kashe Sheikh Albani ne tare da uwargidansa da kuma ɗansa a wani hari da aka kai musu a Zaria.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

BAYANIN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA ASA'ILIN DA AKA KIRASHI YA RUFE TARON WA'AZIN KASA NA JIBWIS DA AKA GABATAR A YOLA.

''Marigayi Sheikh Albani Zaria ya fara bayani da hudubatul haaja sannan daga bisani ya tabbatar ma al'umma da cewa bai zo wannan wa'azin dasa ran cewa zai yi wa'azi ba, sai dai ya'zo ne da niyyar ya saurari wa'azi sannan kuma yayi ma iyayenshi mutanen Yola godiya ta musamman domin Annabi (SAW) yana cewa la'yashkurullah ­malla'yashkurun nas (ma'ana duk wanda bai godema jama'a to baya godema Allah).

Marigayi Sheikh Albani Zaria ya' kara da cewayayi farin cikin asa'ilin da yaji Ash-sheikh Bala Lau a wata kafa na yadalabarai yana cewa mimbarin izala na duk ahlussunna ne kuma duk abun da ya inganta na sunna azo a fada. Har ila yau, yayi farin ciki da bayanin Ash-sheikh Sani Yahaya jingir dan gane da kiran da yayi na cewa a cire gaba, ayima juna uzuri azo ayi ma addini aiki.

Marigayi Sheikh Albani ya kara da cewa a shekarun baya wasu sun yi ta amfani da sunan kungiyar izala suna fada dasu. Yace idan shi da makamantar shi suka ki yin da'a ga wayanda suke fada da sunnahsai a koma ace su Albani suna fada da izala. Ya tabbatar da cewa sun yarda da malaman fiqhu amma manzon Allah (SAW) shine a gaba, kuma kamar yadda sheikh Abdulrazak Yahaya Haifan ya fadaa wa'azin shi cewa idan za'a soki sunna a waazin kasa to basu babu wannan taron, to shima yana kan wannan matsayar.

Marigayi Sheikh Albani Zaria ya kara da cewa; basa fada da izala domin su yan izala ne kuma duk mai fada da izala to dasu Albani ya keyi. Ya kuma roki malamai da sauran al'umma da cewa suyimishi uzuri domin ranakun asabar da lahadi ranaku ne masu muhimmanci na karatu a makarantun su na boko da arabiyya dake karkashin Darul Hadeethis-Salaf iyyah zaria. Saboda hakaduk ya kasance nan da shekara goma ba a gansu a wurin wa'azi na kasa ba to ayi musu uzuri a'sani cew suna tare da izala dari bisa dari kuma suna yiima izala fata na alkhairi.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

 A wata hirar da ya yi da jaridar Daily Trust ya bukaci matasa su nemi ilimin boko don su tafi da zamani musamman ma yanzu da kullum ake kara samun abubuwan fasaha da kimiyya. Ya ce wannan dalili ne ya sanya ya koma jami’a don ya yi digiri na biyu.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kisan ko a gano dalilin yin kisan, kodayake Albani ya shahara wajen kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram, domin a lokuta da dama ya rika ba tsohon shugaban kungiyar marigayi Muhammad Yusuf shawarari da hujjoji don ya janye da’awar boko haramun ne.

Albani yana da tarihin dangantaka mai tsami tsakaninsa da jami’an tsaro, idan baza ku manta ba an taɓa tsare shi sakamakon zargin sa da aka yi da dangantaka da kungiyar Boko Haram, hakan ya sanya ya je kotu ya kare kansa, kuma kotu ta wanke shi.

Biography of Sheikh  Albani Zaria

Tsakanin 1993 da 1994 wadansu mahara sun kai masa hari a wani shagon dinki a Muciya ta Sabon Gari da ke Zariya. Ya kubuta ne bayan jama’a sun kawo masa ɗauki.

Baya ga haka an kai masa hari a gidansa sau biyu wanda kuma ba a samu nasara a kansa ba.

HasaShen Da Marigayi Sheikh Auwal Adam Albany Yayi Kafin Rasuwarsa Ya Tabbata


Malam Yake Cewa:

Kai tsaye jam'iyyar BUHARI zamu zaba, alqibilar mu kenan jama'a, amma fa ku sani BUHARI bashi da kudi duk wanda zaiyi aiki a madadin BUHARI karya sa rai za'a bashi ko kwabo, kada kuma yasa rai idan an fara mulki za'a zo ayi masa fenti a gida.

Bari na fada muku BUHARI koya samu mulkin kasar nan bazai iya gyara ta a cikin shekaru 4 ba, abinda muke bukata farko idan ya hau barna ta tsaya, saboda yanzu ba maganar gyara ake ba.

Malam yaci gaba da cewa, irin yunwar nan da aka yi BUHARIYYA aka dinga cin su garin KWAKI, to ko wanne talaka ya shirya sai anyi irin ta saboda gyara za'a yi, ya kamata mutane su gane don kar mutane suzo su ce, ku kuka ce mu zabi mutanen nan amma gashi anzo ana yunwa.

Abinda nake so na fadawa talakawan mu shine, jama'a ko kun zabi BUHARI sai kun bi da addu'a, matakin farko wallahi kasar nan Allah ya azurta mu, amma anyi wawurar da idan BUHARI ya hau hatta shi kan shi abinda yake tunani da za'a shake wasu marasa gaskiya su amayo yana da wahala.

Amma mu abinda muke fata a tsaida zalunci idan aka tabbatar an tsaida zalunci sai a koma shawarar ya za'a yi a cigaba, saboda sunyi kaca - kaca da kasar, domin duk mutunin da zaiyi shugabanci na kwana 7 sai ya azurta kanshi da zaiyi shekaru dubu 70 bazai yi talauci ba.

Tabbas wannan hasashe na Malam ya zama gaskiya, sai dai muce Allah ya jikansa, shi kuma Buhari Allah ya taimaka masa wajen cika burinsa na taimakon talakawa.

Dangane da kashe Albani za a iya cewa duk malamin da yake kalubalantar karantarwar kungiyar Boko Haram rayuwarsa tana cikin hadari ga garari.

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya gamu da ajalinsa a masallaci a Kano a lokacin da yake sallar Asuba, kuma shi ma ya yi fice wajen kalubalantar karantawar kungiyar Boko Haram, haka batun yake ga kisan da aka yi wa Sheikh Umar dan Mai Shiyya a Sakkwato.

Abin tayar da hankali shi ne har zuwa yanzu an kasa gano wadanda suka aikata kashe-kashen ko suke da hannu wajen kashe wadannan malaman.

Wannan shine takaitaccen tarihin malam abin da ya shafi Rayuwar shi.

Al’amarin abin daure kai ne a ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kasa gano wadanda suke da hannu a cikin kashe-kashen wadannan malaman, hakan zai matukar karya alkadarin tarihin kyakkyawan aikin jami’an tsaro a kasar nan.

Muna fata kisan da aka yi wa Albani zai sanya jami’an tsaro su farka daga barcin da suke yi hade da tsage damtse wajen ganin ire-iren hakan ba su faru a gaba ba.

Ya zama dole jami’an tsaro su gano makasan da duk wani mai hannu a ciki don a yi musu hukunci mai tsanani da zai zama darasi ga duk wanda yake yunkurin aikata laifi irin wannan.

Allah (SWT) muke roko da ya jikan Mallam ya kuma sa Aljannat Firdausi ce makomarsa.

Karanta Yanzu Kaji: Shin me kasani dangane da Takaitaccen Tarihin Addinin Kirista???

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user