Tuesday 31 July 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai acikin Film din Mu Zuba Mu Gani tare da Sharhin Fim ɗin

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Mu Zuba Mu Gani

Tsara Labari: Ibrahim Birniwa

Kamfani: Mia Enterprises

Shiryawa: Muhammad Mia da Abubakar Bashir Mai Shadda

Bada Umarni: Kamal S. Alkali

Jarumai: Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Jamila Nagudu, Fati Washa, Hauwa Waraka, Teema Yola, Asma’u Nas da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar


A farkon fim din an nuna Maimuna (Hauwa Waraka) ta shiga gidan kawar ta Sakina (Jamila Nagudu) inda ta nuna wa Sakina rashin jin dadin ta a kan mijinta da zai kara aure ba tare da Sakina ta fada mu su ba.

Nan fa Sakina ta nuna ba ta son maganar cewa mijin ta zai kara aure ba, kuma ta’ki yarda da hakan har sai da Maimuna ta nuna mata katin shaida sannan ta amince.

Sanin hakan ne ya sa Sakina ta tunzura ta soma mamakin cin amanar da mijinta zai ma ta domin ta dau kudi ta bashi don su yi kasuwanci amma ya dauka ya je ya ‘kara aure da kudin. Nan ta fita zuwa wajen mijin nata Ahmad (Ali Nuhu) wanda ta tarar ya gama shirin fita don zuwa shagalin biki, amma har a sannan bai nuna mata cewar aure zai yi ba, jin furucin bakin sa ne yasa ta ‘kara tabbatar da abinda take zargi, hakan yasa ta debo manja ta watsa masa a kan sabuwar shaddar dake jikin sa kuma ta nuna masa ta riga ta gama gane shirin sa, nan suka fara musayar yawu har suka nufi cikin daki inda Ahmad ya shiga wanka don sauya kayan jikin sa, hakan ne ya bawa Sakina damar kulle shi a cikin daki sannan ta dau wayar sa ta nufi wajen ‘kawar ta Maimuna wadda ta kawo mata labari suka fita daga gidan da nufin zuwa gidan mahaifiyar Ahmad su kai mata ‘karar sa.

Amma bayan zuwan su Sakina gidan mahaifiyar Ahmad sai ta goyi bayan danta ta nuna ai ya dace ya ‘kara aure tunda ita Sakina ba ta haihuwa, jin hakan ne ya tunzura Sakina da ‘kawar ta bayan fitowar su daga gidan suka yanke shawarar zuwa wajen shagalin bikin matar Ahmad, a nan ne Maimuna ta bada shawarar su fara gayyato ‘kawayen su tunda dai sarkin yawa yafi sarkin ‘karfi. Su Sakina suka cika mota daya ita da gayyar ‘kawayen ta suka nufi wajen da ake shagalin bikin amarya.

A wannan lokacin kuma amarya Nabila (Fati Washa) tana zaune a kujera tana jiran ango amma har tsahon wani lokaci bai zo ba, hakan ne yasa ‘kawayen ta su Safiya (Asma’u Nas) suka fara tunanin cewa lallai akwai wani abu da yake faruwa, hakan yasa suka nufi wajen abokan ango wato Mukhtar (Baballe Hayatu) suka nemi sanin jin halin da ake ciki, amma sai Mukhtar ya kwantar wa da ‘kawayen amarya hankali ya nuna musu Ahmad na kan hanyar zuwa, duk da dai shima Mukhtar hankalin sa a tashe yake domin sun kasa samun wayar Ahmad duk da suna tsoron kada ace matar shi Sakina da ake boyewa lamarin ce ta gane, amma basu gasgata hakan ba har zuwa lokacin da Sakina da gayyar ‘kawayen ta suka shiga cikin dakin taron shagalin bikin, nan fa su Mukhtar suka firgita don sun fahimci cewa lamari ya lalace.

A wannan lokacin ne Sakina ta karbi abin magana ta soma jawabi akan cewa mijin ta Ahmad ne ya wakilta ta zuwa wajen taron bikin amaryar sa saboda bazai samu damar halartar taron bikin ba, nan fa ‘kawayen amarya suka tasowa Sakina aka soma musayar yawu cikin bacin rai, kafin wani lokaci rigima ta kaure a tsakanin su aka fara bawa hammata iska ana doke-doke, a haka taron bikin ya watse cikin rashin jin dadi. Bayan wani lokaci Ahmad ya je gidan amarya ya basu hakuri kuma ya fada musu abinda ke faruwa, da farko amarya Nabila (Fati Washa) taci alwashin ba zata tare a gidan sa ba, amma daga bisani Ahmad da abokin sa Mukhtar suka rarrashe ta har ta amince aka kai ta gidan da Ahmad ya kama haya aka saka ta. Kwatsam sai Sakina ta bayyana a gidan da Ahmad ya kamawa Nabila haya ta nuna lallai sai ya biya ta kudin da ta bashi don suyi kasuwancin amma ya dauki kudin yayi mata kishiya. Jin abinda ya faru ne yasa Nabila ta goyi da bayan Sakina kuma ta dau mayafi ta bita akan cewar ba zata taba zama mallakin Ahmad ba har sai ya biya Sakina kudin ta.

 Nabila ta koma gidan Ahmad da zama yayin da suka hade kan su suna yin komai tare, hakan ne ya damu Ahmad don Sakina ta hana shi zama da amaryar sa ta nuna lallai sai ya biya ta kudin ta zata dawo masa da matar sa. Wannan dalilin ne yasa Ahmad ya fara tunanin a inda zai nemo wa Sakina kudin ta ya biya ta, a wannan lokacin ne abokin sa Mukhtar ya bashi shawara akan ya saki Sakina ta koma gidan su ko hakan zai kawo ‘karshen matsalar sa, amma sai Ahmad ya nuna bazai iya yi mata wannan rashin adalcin ba. Daga nan ne Ahmad ya yanke shawarar sayar da gidan sa wanda Sakina ke ciki don ya samu kudin da zai biya ta miliyan biyu din da ta ara masa suyi kasuwanci. Bayan an kira dillalai sun yiwa gidan kudi sai Sakina ta nuna ita zata sayi gidan sai tayi masa cikon kudi akan wanda zai biya ta, nan fa Ahmad ya amince aka kira shaidu aka gama komai Sakina ta sayi gidan ta cikawa Ahmad kudin sa, a wannan lokacin ne Sakina suka yi baram-baram da amarya Nabila don tana ganin cewa Sakina bata da tausayi, haka Nabila ta kwashe kayan ta suka bar gidan ita da Ahmad suka koma gidan da ya kama musu haya. Zaman su a gidan babu dadewa sai Sakina tazo gidan ta nuna cewa ita ma anan gidan zata zauna saboda nan ne gidan mijin ta ba wancan gidan da ta siya ba, kuma mijin ta ne ke da alhakin daukar nauyin ta tunda ba zaman kanta take yi ba, nan dai Sakina ta dauki daki daya a cikin gidan, yayin da Nabila ta hana Sakina zama akan kujerunta saboda ba na Ahmad bane, jin hakan ne yasa Sakina ta sayi sababbin kujeru da sauran kayan amfanin gida aka dauko aka zuba itama nata kujerun da su talabijin a cikin falon, faruwar hakan ne yasa Nabila ta ‘kara jin tsanar Sakina a ranta, suka cigaba da zama cikin rashin zaman lafiya rigimar yau daban ta gobe daban, a kullum Sakina bata da burin da yafi ganin ta raba amincin dake tsakanin Nabila da mijin su Ahmad, don har sharri take yiwa Ahmad a wajen Nabila na cewar bai dauke ta a bakin komai ba, amma ko Nabila tayi fushi daga baya sai ta fahimci cewa sharri ne kawai Sakina ta hada mata.

Wata rana Ahmad sun fita don yin siyayya shi da amaryar sa Nabila, sai wata budurwa ‘kawar Nabila ta gan su kuma ta tuna da cewa Ahmad tsohon saurayin ta ne wanda ya fasa auren ta ya auri ‘kawar ta, hakan yasa ta jawo Nabila gefe ta kitsa mata cewar Ahmad manemin mata ne akwai wata budurwa ‘yar jami’a wadda ya ajiye a wani gida suna zaman dadiro da ita. Jin hakan ne ya tashi hankalin Nabila tayi fushi ta bar wajen siyayyar ba tare da sun jera tare da Ahmad na, duk da ya tsayar da ita yana tambayar ta abubuwan da suke faruwa amma ta’ki gaya masa kuma ta tafi gida ta bar shi a wajen siyayyar shi kadai, yayin da waccan budurwar taji dadin hakan saboda dama tayi masa sharri ne ne don ta rama wulakancin da yayi mata.

Bayan Nabila ta koma gida tana kuka sai ta fadawa Sakina abinda ke faruwa na irin cin amanar da Ahmad yayi musu, jin hakan ne yasa Sakina taci alwashin sai sun ganar dashi kuren sa, bayan Ahmad ya dawo sai Sakina da Nabila suka hade masa kai suka daina kula sa. Har ya zamana cewa ko hira sun daina zama suna yi tare dashi, saboda suna zargin sa da bin matan banza, Ahmad yayi ‘kokarin fahimtar dasu cewar abinda suke zato ba gaskiya bane, amma sun kasa fahimtar sa har zuwa lokacin da aka kira Ahmad aka sanar dashi kwangilar da suke jira ta fito kuma shi da abokin sa Mukhtar suka samu makudan kudi har kimanin miliyan arba’in-arba’in. Tun daga lokacin da Ahmad ya samu makudan kudi sai ya bawa iyalan sa labari, jin hakan ne yasa suka sauko daga kan dokin fushin da suke yi dashi, suka soma neman gafarar sa, musamman Sakina wadda tafi yi masa abubuwa marasa dadi, nan suka nuna masa komai ya wuce.

A wannan lokacin ne Ahmad ya sayi sabon gida sannan suka koma can da zama, kuma ya sanar da su Sakina cewa shi fa aure zai ‘kara, sun dauka cewa Ahmad da wasa yake har sai da ya tabbatar musu da haka.

A sannan ne kuma Ahmad ya nemi shawarar mahaifiyar sa akan zai ‘kara aure, nan fa ta amince amma da sharadin cewa daga baya zai saki uwar gidan sa Sakina, Ahmad ya amince da hakan kuma suka cigaba da sukayya da sabuwar budurwar sa Jamila (Teema Yola) Lokacin da mahaifiyar Ahmad ta samu labarin irin macen da zai aura sai ta’ki amincewa saboda jin cewa Jamila bazawara ce kuma bata jima a gidan tsohon mijinta ba ta fito bayan fitowar ta kuma ta zubar da cikin jikin ta. Jin hakan ne yasa Ahmad ya nuna hakan ba gaskiya bane kuma bazai iya janye maganar auren sa da Jamila ba, hakan ne yasa mahaifiyar sa ta bu’kaci ya kawo mata Jamila tana son ganin ta, Ahmad ya dauko Jamila ya kawo ta wajen mahaifiyar sa, nan fa mahaifiyar sa ta gargadi jamila akan lallai ta rabu da danta Ahmad, amma jamila ta nuna babu wanda ya isa ya hana ta auren Ahmad. Lokacin da jamila ta koma gida ta sanar da mahaifiyar ta abinda ya faru tsakanin ta da mahaifiyar Ahmad, sai mahaifiyar jamila taji dadi saboda jamila bata ragawa mahaifiyar Ahmad ba, kuma suka fara shiri don yin galaba akan duk wanda zai kawo matsala a cikin auren jamila da Ahmad.

Bayan an daura auren jamila da Ahmad sai ya fara ajiye ta a gidan sa tare da su Sakina, amma tun a daren farko aka soma tashin hankali, Sakina da Nabila suka hade kai suka fara shukawa jamila rashin mutunci. Dalilin hakan ne yasa Ahmad ya dauke jamila ya sakata a wani gidan nata ita kadai, sai dai kuma tun daga sannan sai su Sakina suka daina ganin Ahmad, ya daina zuwa inda suke kuma ya daina zuwa wajen mahaifiyar sa, hakan ne ya tashi hankalin su Sakina suka kai ‘karar sa wajen mahaifiyar sa, ai kuwa sai taje har gidan amarya jamila tana neman Ahmad, amma bata samu ganin sa ba, sai ma zallar rashin kunya da jamila ta yiwa mahaifiyar Ahmad.

Tun daga sannan mahaifiyar Ahmad tayi fushi dashi ta soma neman mafita domin jamila ta tare ko ina kuma ta sa Ahmad ya canja layin wayar sa. Wata rana Sakina da Nabila suka zauna suka yi karatun ta nutsu tare da kokarin sake halin su don su zauna lafiya da mijin su, bayan sun roki gafarar Ahmad ne suka nuna sun daina rigima, sai hakan yasa ya nuna zai dawo da jamila cikin gidan su cigaba da zama gaba daya.

Abubuwan birgewa:

1- Labarin ya nishadantar kuma ya rike me kallo ba tare da gajiyawa ba.

2- Jaruman sun yi ‘kokari matuka wajen isar da sakon labarin.

3- An yi ‘kokarin samar da wurare masu kyau wadanda suka dace da labarin.

4- Sauti ya fita radau, abin daukar hoto wato camera itama ba laifi.

Kurakurai:

1- Lokacin da Sakina ta watsawa mijin ta Ahmad manja a rigar sa har ta biyo shi cikin daki tana yi masa masifa, Me kallo yaji ta kira sa da suna Mahmud, shin Sakina ta mance sunan mijin ta Ahmad ne da har ta kira sa da Mahmud?

2- Shin Nabila bata da iyaye ko kuma dangi ne? Duk da irin matsalolin da suka faru musamman a lokacin auren ta amma ba’a nuna iyaye ko kuma wasu dangin ta ba.

3- Mai kallo yaga Nabila ta dawo gidan Sakina da zama a sanda take matsayin amarya, da nufin ba zata koma hannun Ahmad ba har sai ya biya Sakina kudin ta, ba’a nuna lokacin da Nabila ta kwaso kayan ta daga gidan da Ahmad ya kama mata haya ba, shin kayan Sakina take sakawa?

4- Har fim din ya ‘kare ba’a nuna wa mai kallo irin sana’ar da Ahmad yake ba, shin Ahmad ba shi da aikin yi ne? Kuma wacce irin kwangila ce Ahmad yayi wadda har ya samu miliyan arba’in? Tunda ba’a nuna Ahmad yana wata sana’a ba ya kamata ayi bayanin irin kwangilar da yayi ya samu kudi masu yawa haka, idan kuma shi ma’aikaci ne wanda aka kore sa daga wajen aiki, to ya dace a yiwa mai kallo bayani ko da baki ne.

5- Lokacin da Ahmad yaje wajen mahaifiyar sa da maganar cewa zai ‘kara aure saboda matan sa biyu sun hade masa kai, a matsayin mahaifiyar sa wadda aka nuna a uwa ta gari, bai kamata ta bashi shawarar cewa idan ya ‘kara aure ya saki matar sa Sakina ba. Domin duk da sakin aure ba haramci bane, to amma abu ne wanda ko ubangiji ba ya son shi.

6- Akwai wurare da yawa wadanda muryoyin jaruman basu hau da bakin su ba, kamar lokacin da a ‘karshen fim din su Sakina suka yi nadamar abinda suke yiwa mijin su, da kuma lokacin da mahaifiyar Ahmad taje gidan amaryar sa Jamila da safe a karo na biyu, duk muryoyin su basu hau da bakin su ba.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar, amma daga ‘karshe sabon zaren labarin da aka tufka yaso tsinkewa, saboda an kawo karshen fim din tun labarin bai gama direwa ba. Allahu A’alamu.!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Leadership A Yau


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user