Tuesday 8 October 2019

SHIN KO KASAN ME YA SA ALLAH YA HALICCI SAURO?

Tura Wannan Zuwa
Duk da yake ba dole ne ilimin mafi yawan mutane ya riski abubuwa da yawa ba, amma mu musulmi mun yi imani cewa a cikin tsarin Allah da iliminsa ba wata halitta marar amfani.


Me yasa aka halicci Sauro...


Marubuci: Dr. Kabir Asgar Hafizahullah

Baya ga cewa dukkan halittun Allah suna da gudumowar da suke ba duniya da sauran halittun Allah wajen daidaita dabi’a da wanzuwar rayuwa, kowace halitta a kebantacce, akwai dalilin da ya sa Allah ya halicce ta.

Masana suna cewa daga cikin alfanun halittar sauro akwai zamowar shi jarabawa da Allah yake yi wa muminai don su yi hakuri su sami lada da ɗaukaka a wajen Allah. Sannan kuma, har ila yau, sauro an halicce shi domin kwado ya sami abin kalaci. Baya ga haka, halittar sauro wata hanya ce da Allah yake amfani da ita wajen karya kwarin bayi masu taurin kai da nuna isa da wuce iyaka wajen mugunta.

A karkashin haka ne sauro yai maganin Lamarudu ya zame masa alaƙaƙai.

A wannan zamanin namu  nau’in sauron da a kimiyyance ake ce ma (Aedes Albopictus) ya gajiyar da binciken Turawa.

MUKALOLI MASU ALAKA:

AKWAI ABIN AL-AJABI GA RAYUWAR WANNAN DABBA MAI YAWAN GASKE WATO KADANGARE

Akwai Abin Al'ajabi da ban Mamaki Mai Tarin Yawa game da Rayuwar Wannan Dabba Wato Tururuwa

KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA FARKO (1) NEW WORLD ORDER

Allah  ya yi amfani da wannan halitta da suke kira da (Yellow Fever Mosquito) don ya gwada musu gazawarsu da karancin iliminsu.

Allah shine mafi sani.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user