Showing posts with label Filin Tunatarwa Da Fadakarwa. Show all posts
Showing posts with label Filin Tunatarwa Da Fadakarwa. Show all posts

Sunday, 24 August 2025

Gaskiya Magana Kan Kalmar Zafin Nema Ba Ya Kawo Samu

Gaskiya Magana Kan Kalmar Zafin Nema Ba Ya Kawo Samu

Idan ana so a kwantarwa mutum hankali, sai ana masa wannan karin magana: “Zafin nema ba ya kawo samu.” Amma idan ka tsaya ka yi tunani, za ka tambayi kanka, “to, me yasa Allah ya ce tashi in taimake ka?”


Gaskiyar magana kan kalmar zafin nema ba ya kawo samu
Hoto: Ridofranz/Getty images

Marubuci:- Dahiru Aliyu Musa


Gaskiya ne akwai lokaci, akwai rabo, kuma Allah yana ba wa wanda ya ga dama a lokacin da ya ga dama. Amma hakan ba yana nufin ka haƙura da ƙoƙari ba, ko ka zauna jiran abin ya faɗo maka daga sama. Sau da yawa, hanyar da Allah ke amfani da ita wajen kawo maka abin da aka rubuta maka ita ce ƙoƙarinka.


Samu yana zuwa ne ga mai neman sa, kamar yadda nasara take zuwa ga mai jurewa wahala da dagewa.


Ka duba manoma. Suna shuka iri da kyau, suna yin aikin noma daga safe har yamma. Su ba sa cewa “idan rabonmu ne za mu girba.” Sun san aikin su shi ne shuka, Allah kuma shi ne mai sa amfanin ya fito.


Ka duba ɗalibai. Ba su zauna a gida suna addu’a kawai su ce “idan rabona ne zan ci jarabawa.” Suna karatu, suna nema, sannan su dogara da Allah don ya sa musu albarka.


Ko ’yan kasuwa. Ba su zauna suna jiran kasuwa ta kawo musu kuɗi ba. Suna tashi da safe suna neman dama, suna jurewa, sannan suna sa ran Allah ya saka musu nasara a neman su.


Don haka, wannan karin magana tana da ma’ana, amma ba cikakkiya ba ce. Abin da ya dace shi ne ka dage, ka nema, sannan ka bar sakamakon a hannun Allah.

Saturday, 15 March 2025

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba

1. Kada ka raina iyayenka. Ba za su dawwama ba, ka kula da su matuƙa.


2. Idan ka gyara kanka, kamar ka  gyara iyalinka. Idan ka gyara iyalinka, kamar ka gyara al’umma ne, idan ka gyara iyalinsa kai ma ka gyara ni ma na gyara sai al'umma ta gyaru.


Gaskiya 25 Da Ba Za Ku Same Su A Ko'ina Ba
Hoto: Getty Images

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


3. Namijin da ya iya fin ƙarfin  sha’awarsa yana da cikakken iko kan rayuwarsa.


4. Kunya ta ɗan lokaci ce, amma nadama tana dawwama. Ka fi son fuskantar kunya da wuri a kan ka yi nadama daga baya. Ka yi aiki tuƙuru kada ka ji junyar wulaƙancin jama'a kan sana'arka.


5. Namiji mara manufa yana rayuwa ne kawai don shagaltuwa da abubuwan banza. Kamar zuwa fati, shaye-shaye da neman mata.


6. Ka guji mutanen da ke ƙin jinsin da suka saɓa da nasu; suna da matsala a zukatansu.


7. Ka saurari tsofaffin da suke farin ciki, sun san abin da suka gani a rayuwa.


8. Ɗa’a (hazaƙa) ta fi ƙwazo (motsi zuciya). Ka dinga yin abin da ya dace, koda ba ka jin daɗin aikata shi a ranka.


9. Idan kana jin buƙatar burge kowa, to kai bawa ne gare su.


Duk lokacin da kake son burge mutane za ka zama kamar bawansu . Duk abin da suke so shi za ka aikata ko ba daidai ba ne. Hakan ya sa malamai suka zama karnukan 'yan siyasa.


10. Mafi yawancin baƙin ciki a cikin maza na faruwa ne sakamakon rashin manufa a rayuwa.


Kaso 90 na maza suna faɗawa wahala ne da ƙunci da talauci saboda rashin manufa da gina kasuwanci ko aiki tun suna ƙananu.


11. Idan namiji yana rashin kunya ga uwarsa, kada ki amince da sh, ba zai girmama ki ba.


12. Namijin da ya saba da jin daɗi mara amfani yana lalacewa. Dole ka saba da wahala don ka bunƙasa.


13. Halayen mace suna ƙarfafa namiji, haka nan kuma halayen namiji suna ƙarfafa mace.


Idan namiji ya samu mace mara manufa sai ta rage tasa manufar da kaso 70 haka idan ya samu mai manufa sai ta cike shi ya zama mai  ɗari bisa ɗari.


14. Rayuwa ba za ta sauƙaƙa ba, kai ne kawai za ka ƙara ƙarfi don fuskantar ta.


15. Babu wanda ya taɓa zama babban mutum ta hanyar zama kan kujera yana kallon fina-finai da tsalle tsakanin facebook da tiktok tsawon wuni/yini.


16. Namiji yana samun mafi yawan farin ciki ne lokacin da yake gina abin da zai bari bayan ya tafi.


17. Kada ka saurari marasa fata da ke cewa rayuwa tana muni idan shekaru suka kai 40. Idan ka dage, kana inganta ta fiye da matashin ɗan shekara 20.


18. Kasance namijin da ke da nutsuwa lokacin da kowa ke firgice aka rasa mene ne mafita. Yi ƙoƙari ka nemo mafita.


19. Gwamma ka yi kuskure a kokarinka fiye da ka zauna ba ka yi komai ba.


20. Yin dariya da mai kiba a dakin motsa jiki kamar yin dariya da marasa gida ne don yana neman aiki. Wannan rashin tunani ne.


21. Zama cikin yanayin wajen da yake shiru da shan iska yana rage damuwa fiye da shan magungunan maye da giya.


22. Koyi yadda za ka karɓi suka ba tare da ka fusata ko ka mayar da martani da zafi ba.


23. Daina kallon batsa, za ka ji daɗin rayuwa kuma ka fi zama namiji nagari.


24. Ka nemi abin da kake so ta hanyar aiki da ƙoƙari, kada ka yarda da son cin banza da neman alfarma.


25. Ka tuna cewa wasu maza suna da kirki ba don suna da hali mai kyau ba, sai don sun kasa tsayawa tsayin daka wajen kyautatawa mata har matan ke juya su kuma suke ganin mazajen nasu masu kirki ne.

Sunday, 26 January 2025

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Idan kana fama da damuwa ko rashin walwala a zuciyar ka, ka yi abubuwan nan guda 3.


Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya
Hoto: Dilok Klaisataporn

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


1. Idan kana da 'yan uwa ko aboki na ƙwarai a wani gari daban, ka kai masa ziyara.


Ma'ana dai ka yi tafiya yadda za ka canja muhalli na wani lokaci.


2. Idan akwai wani abu da ka sa a gaba, kuma ya gagara samuwa, ka watsar da wannan buƙatar, ka haƙura da ita.


Ka kuma yadda ba kowacce buƙata ce take samuwa ba.


Idan kana da hali na wasu 'yan kuɗaɗe, ko kuma wani abu mai amfani, ka farantawa wani rai, da wata kyauta mai ban mamaki.


Insha Allah waɗannan matakai idan ka bi ɗaya daga cikinsu, ko duka ukun, za ka samu sauƙi da maslaha a zuciyar ka.


Allah ya magance mana dukkan damuwar mu, ya kawo mana sauƙi da rangwame Amin.

Saturday, 18 January 2025

Nasarar Dare Daya

Nasarar Dare Daya

Akwai wani kuskure da muke yi, Matashi yana fara samun kuɗi, ko wata dama, maimakon ya yi amfani da wannan damar wajan ƙara gina sana'a ko kasuwancin da yake yi, a'a, sai ya fara tarawa kansa maƙiya na babu gaira babu dalili, shi ne kullum habaici a status; "sun ƙi, Allah ya so.", "Lokacin mu ne, yen yen yen yen....", Kwarai! Lokacin ka ne, amma na faɗuwa, domin da wannan halin babu inda za ka je.


Nasarar Dare Daya
Hoto: Pixel

Marubuci:- Abdulfatah Yakubu


Kada nasarar dare ɗaya ta ruɗeka, rayuwa mataki mataki ce. Idan Allah ya yi niyyar buɗe mana ƙofofin alkhairi dubu, ba lokaci ɗaya yake buɗe mana su duka ba, zai buɗe mana ƙofar farko ne, alla bashshi mu kuma sannu a hankali ta hanyar inganta kai, da alaƙar mu da jama'a sai mu buɗe ragowar ƙofofin.


Kowace dama, dama ce ta samun wata damar. Kowane taku, taku ne zuwa ga wani takun. A kasuwa, dubu ɗarin ka ta farko, dama ce ta samun miliyan ɗin farko.


Iya karanta baƙaƙen kowane yare, dama ce ta fara koyon haɗa baƙi.


Iya zama, dama ce ta fara koyon tsayuwa, tsayuwa kuma dama ce ta fara koyon tafiya, haka dai lissafin yake a kowane ɓangare na rayuwa.


Kai da ka fara yanzu, ina kai ina yi wa waɗanda suka daɗe a ciki habaici?  Yanzu aka fara, kada nasarar dare ɗaya ta ruɗe ka.

Friday, 10 January 2025

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Wuta ita take raba dusar ƙarfe da ƙasa, ta tsarkake shi tare da ƙara masa karfi da daraja. Wuta ita take narka zinare ta raba shi da dukkan datti, har ya zamo mai daraja kuma abun kwalliyya.


Kalaman ƙarfafa gwiwa na sabuwar shekara
Hoto: Rawpixel/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Haka kuma ƙalubalen rayuwa yana inganta ruhin Ɗan Adam, ya saita tunanin sa, ta yadda mutum zai ƙara fahimtar hikimar rayuwa da ma'anarta.


Ma'aiki sallallahu alayhi wasallam cikin Hadithi yake cewa;


"Idan Allah (S.W.T) ya so bawa, sai ya jarrabce shi, idan ya jure kuma ya jajurce, sai ya sami mafita da rabo. Abun da ya biyo baya na ƙaiƙayin zuciya kuma, idan aka yi haƙuri, kankarar zunubi ce ga mumini."


Manufa anan shi ne kada mu karaya a kowanne hali, mu kasance masu fata nagari, tare da kyautata zaton samun sauƙi daga kowanne tsanani, domin bayan dukkan tsanani sauƙi ne yake biyo baya.


Marigayi BASHIR OTHMAN TOFA, cikin talifin sa "TUNANIN KA KAMANNIN KA,, Ya ce "Wahala ita ke matso ƙwazo, shagwaɓa kuma kashe shi take yi."


Jarumi DENZEL WASHINGTON, yana cewa; sauƙi ya fi zama barazana ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than hardship".


Ba ma fatan tsanani ga kawunan mu, ko ga 'yan uwan mu, sai dai gaskiyar magana shi ne, ba za mu iya kaucewa ƙalubale ba matuƙar muna raye, sai dai mu yi tanadi, kuma mu yi komai cikin hankali da nazari.


Sannan mu yi haƙuri da rayuwa a kowanne hali da lokaci.


Mu sani tsanani ba ya dawwama, kamar yadda sauƙi da jin daɗi su ma ba su da tabbas.


Mu yi ƙoƙarin samarwa kanmu da kanmu farin ciki yayin yalwa ko rashi, mu ƙaunaci juna, mu yi afuwa da uzuri ga juna.


Tabbas ƙauna da soyayya wani sinadari ne da yake maganin cututtukan zuciya da yawa, ya ba ta salama, ya kuma amintar da makusantan mai ita.


Fatana gare mu duka shi ne mun shiga sabuwar shekara da sabon tunani, da sha'awar koyo da saurare tare da fahimta kafin yanke hukunci akan komai da kuma kowa.


Mu sani kowa da yadda yake kallon rayuwa, kuma tunanin kowa zai iya kasancewa mai amfani a wani lokaci.


Mafi muhimmanci shi ne mu gane lokacin da ake buƙatar komai da sa'adda ake buƙatar kishiyarsa.


Mu mutunta juna da ra'ayin juna.


Mu sani Allah (S.W.T) yana ganin mu a cikin kowanne al'amari, kuma shi ne Mai hukunci, daidai da dacewa a wajensa take.


Allah ya kawo mana ɗauki ya tsayar da zuciyar mu akan imani, ya sa mu kasance masu amfani ga kawunan mu da al'ummar mu.


Kada mu cutar kada a cuce mu.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara cikin ƙaunar juna da taimakon juna da afuwa ga juna, tare da kare harshen mu daga miyagun kalamai na sukar juna Amin.

Sunday, 5 January 2025

Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba

Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba

1. Ka yi ƙoƙari ka inganta aljihunka, rayuwa ba kuɗi akwai takaici da wahala.


2. Ka cire tsoro ka jarraba wani sabon abun ko za ka dace.


3. Ka rage dogaro da abokai da 'yan uwa, ba koyaushe za su iya taimakon ka ba.


Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba
Hoto: 123RF

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


4. Koda wani ya ɓata maka, ka yi ƙoƙari ka hana kanka yin gaba ko ƙiyayya da shi.


Gaba da ƙiyayya suna hana mutum yin tunani yadda ya kamata, har ya cimma manufarsa.


5. Ka koyi yin afuwa, koda ba za ka sake yarda da mutum ba.


6. Duk mu'amalar da za ka yi, ka yi cikin gaskiya. Allah yana taimakon kasuwanci ko duka aikin da aka yi tsakani da Allah.


7. Kyautata zato yana da muhimmanci, amma kada ka bari ka zama sakarai. 


Ka dinga kulawa da manufar mutanen da kake mu'amala da su.


8. Ka rabu da hassada da ƙyashi, domin ita hassada ɓata lokaci ce, ba ta hana wanda kake yi wa cin nasara.


9. Idan kana son wani abu ka tashi ka nema, fata ba ya kawo sakamako sai aiki.


Idan ba ka gane wani abu ba, ka tambaya domin zato yana shigar da mutum cikin ruɗani.


10. Ka koyi haƙuri ka koyi jira, komai yana da lokacin da Allah ya ajiye masa.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara a sa'a da imani da lafiya da mutunci da kuɗin kashewa Amin.

Wednesday, 1 January 2025

Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara

Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara

1. Mu yi nazarin 2024, nasarorin da muka samu, da kurakuran da muka yi.


2. Mu mayar da hankali sosai wajen fahimtar kurakuren da muka tafka, da nufin gano musabbabin su, da yadda za mu kaucewa maimaita su a 2025.


Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara
Hoto: Good housekeeping 

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


3. Mu yi duba sosai akan abubuwan da suka fi cinye mana lokaci, mu ware waɗanda ba sa amfanar da mu, domin maye gurbin su da ayyukan da suke tallafar rayuwar mu.


4. Mu yi nazarin alaƙar mu da jama'a da nufin ƙara kusantar mutane na ƙwarai musamman waɗanda za mu koyi wani abu daga gare su (Mentors). Mu zare jikin mu daga mutanen da za su iya gurɓata rayuwar mu ko daƙile ci-gaban mu.


5. Ga wanda iyayensa suke raye, mu ƙara kusantar su tare da ƙoƙarin ba su farin ciki, hakan babban dafa'i ne. Kuma zai ƙarawa rayuwar mu albarka.


6. Sakamakon canjin rayuwa da aka samu, dole ne mu binciki yanayin samun kuɗin mu, tare da duba hanyoyin da za mu inganta neman mu, ko ƙara wasu hanyoyin samun kuɗin shiga.


7. Dole ne mu yi watsi da ɗabi'ar nuna isa da ƙasaita mara dalili, mu daina raina kowacce sana'a, matsawar za ta kawo kuɗi na halak.


8. Mu mayar da hankalin mu kan ƙanana da matsakaitan sana'oi waɗanda al'umma ta fi buƙata, akwai sirri da kuɗi mai yawa ga wanda ya fahimci alfanun ƙananan sana'o'i na gama gari.


9. Wajibi ne kowa ya ƙirƙiri asusu na ajiya, ya kuma tabbatar yana ɓoye wani abu komai ƙanƙantar samun sa, saboda ɓacin rana da larurori na bagatatan.


10. Kada mu ji kunyar tattauna matsalolin mu da waɗanda suka dace domin neman shawara ko shiriya (Guidance) don fita ko kaucewa matsalolin da suka dame mu.


11. Mu dinga samun lokacin nishaɗi muna jingine wasu matsalolin ko damuwa domin inganta lafiyar ƙwaƙwalen mu da samawa zuciyoyin mu sauƙi.

Monday, 30 December 2024

Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi

Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi

Abubuwa biyar yana da kyau duk wani matashi ya sani kuma ya kiyaye su. Idan kai matashi ne ya kamata ka san waɗannan abubuwa biyar ɗin.


Ga su kamar haka:


 1. Lokaci


A halin da kake kana cikin wani lokaci ne wanda Allah ya ware maka na musamman a rayuwarka, ƙarfin ka ya kai ƙarfi, tsokar jikinka da gaɓoɓin jikinka duk suna nan lafiya, sannan ƙwaƙwalwarka na saurin yanke shawara.


Ƙaramin yaro ba zai samu wannan damar ba, sannan tsohon mutum ba zai samu ba sai kai.


Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi
Hoto: Adobe Stock

Marubuci:- Khalid A Gombe


Duk abin da za ka nema ka neme shi a wannan lokacin kada ka bari lokacin ya wuce maka. Da zarar ka kai shekaru 20 to kana da sauran shekaru 20 da Allah ya albarkace ka da su.


Ka nemi duniyarka da lahirarka ba tare da  gajiya ba.


2. Abokai


Ka zagaye kanka da abokai nagari waɗanda suke da natsuwa. Zama da mutum na gari zai sanya ka zama nagari.


Duk yadda mutumin banza yake son ka da abota kada ka sake ka yi abota da shi. Ka yi abota da mutanen da suka yi nasarar rayuwa, kai ma za ka yi nasara.


3. Zamani


Ka kula da zamani sosai domin shi ne abin da ya fi ruɗar mutane. Idan ka ga ana yayin wani abu sai ka ji kana son mallakar abin.


Kada ka mallaki abu don kawai ana yayin sa ko don ka burge wani, ka mallaki abu domin kana da buƙatar abin kuma domin amfanin da abin zai maka.


4. Ka maida hankali


Kada ka zama mai sa'ido akan harkokin wani maimakon haka ka maida hankali wajen tafiyar da naka harkokin.


Matuƙar kana so ka ci gaba to dole sai ka daina shiga abin da bai shafe ka ba. Ka yi ƙoƙarin gano laifinka kuma ka gyara laifin ya fi ka dinga bincikar laifin wani.


5. Haƙuri


A duk abin da kake nema to ka sani haƙuri ne kaɗai zai ba ka abin.


Kada ka damu don abokanka sun riga ka samun arziki kai ma naka na zuwa a lokacin da ya dace.


Wani zai iya riga ka aure kuma ka riga shi haihuwa haka wani zai riga ka samun arziki amma ka zo ka fi sa arzikin. Don haka ka kwantar da hankalinka lokacinka zai zo.

Thursday, 19 December 2024

Tafi Sama

Tafi Sama

Duk abun da ya yi sama ka jira zuwan shi ƙasa lokacin da zai faɗo ƙasa babu wanda ya san zai faɗo, to haka ma ɗaukaka take zuwa ta kuma tafi lokacin da ba ka tunani.


Tafi Sama
Hoto: Stock Adobe

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Allah ya sa mu dace Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Saturday, 14 December 2024

Kasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim

Kasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim

Duniya budurwar wawa, mutuwa tana kan kowa, haka dole za ta biyo ka kodayaushe ko ba ka so ba.

Ƙasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim
Hoto: Rollover/iStock photo

Zuciya tana mini rauni, ta hana ni in yi sukuni, watarana za mu rabu dukan mu ba za mu sake gamo ba.

Lamarin yana mini tsauri, a cikin bugawar fari, babu wanda sam ya sani idan ba kaliƙin mu guda ba.

A cikin watan watarana za a yanke duk wata ƙauna, dukkanin abin da ka mallaka ba za a kai ka da shi ba.

Daɗa yanzu ka zama gawa, haka za a kai ka kushewa, daga kai kaɗai sai ayyukan da ka aikata ba wai ba.

Duniyar ga ƙyalƙyal banza, kyan macijiya ba izza, walwali take daga nesa in ka iso ba za ka gani ba.

Yaudarar tana mini zafi, da shigo-shigo ba zurfi, ran da duk ka bi ta ta kai ka inda ba za ka ko dawo ba.

Shi agogo ba ya baya, kuma lokaci bai ƙarya, duk irin da kai ka dasa shi dole akwai yinin yin girba.

Furfura alamar tsufa, yau da gobe tamkar jifa, lokacin ka ba ya jira idan ya wuce ba zai dawo ba.

Ga jikin ka ba shi da ƙwari, yara duniya labari, duk abin da za ka saye shi don ka ci sam ba zai daɗi ba.

Maigidan ka ya mutu shi ma, mutuwar ka ba ta girma, jinjiri ya kan mutu saurayi yai rayuwa gwaggwaɓa.

Ka taho kana yin kuka, ka mace ana maka kuka, da bazar ka ne wasu ke rawa ba su so a ce ka kau ba.

Wasu sun mace sun huta, wasu sun wuce an huta, kar ka zam a gundura har da za ka mace ba ai kewa ba.

Ka yi tarbiyyar 'ya'yan ka in ka tsufa za su ji ƙan ka, haka nan idan ka mace ba za su gushe suna addu'a ba.

Annabin ka ne baƙon ka, girmama shi kar ka guje shi kar ya guje ka, wanda duk ya girmama Ɗan Adam ba zai rashin matsayi ba.

Arzikin ka na a jikin ka, zai biyo ka kan ajalin ka, bi a hankali dukkan rabon ka ba za ya zo ya wuce ba.

Duniya gidan kashe ahu, la'ila ha illallahu, yanzu ƙila likkafanin ka ya isa kasuwa ba ka sani ba.

Sa'eed Ibrahim ne wanda ya gabatar da wannan ƙasida mai cike da saƙonni masu amfanarwa ga kowa, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ƙasidar a rubuce domin ilimantarwa da fadakarwa a gare mu gabaɗaya.

Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan ƙasidu a rubuce masu ma'ana tare da waƙoƙi a rubuce su ma masu ma'ana.

Friday, 6 December 2024

Rasa Komai

Rasa Komai

Za ka iya rasa komai a rayuwa, ka mayar da shi ko mafiyin sa amma ba za ka iya mayar da iyayenka da su riga mu gidan gaskiya ba.


Rasa komai
Hoto: fran kie/Stock Adobe

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Sannan ba za ka iya mayar da duk daƙika ɗaya da ta wuce ba (Duk damar da ta wuce ko kuma duk lokacin da ya wuce ya riga ya tafi kenan) sai dai wani ba shi ba.


Allah ka jiƙan iyayenmu waɗanda suka riga mu gidan gaskiya ka sa Aljanna ce makomar su, idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Thursday, 28 November 2024

Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa

Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa

Shi so ba a yi masa tilas. Duk wanda ya cusawa zuciyarsa abin da ba ta yi na'am da shi ba (Ba ta aminta da shi ba a karan farko) daga ƙarshe ladama/nadama ce za ta biyo baya.


Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa
Hoto: Shutterstock da Salsa 4 life


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Shi so ba a yi masa dole. Idan ba a son ka, kar ka tsananta, duniya da faɗi, je ka nemi daidai da kai domin a lokacin da wani ya tsane ka, a lokacin wani yake masifar son ka.


Allah ya haɗa mu da masu son mu saboda shi, kuma su guje mu saboda shi Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Wednesday, 27 November 2024

Illar Da Zina Za Ta Yi Ga Rayuwar Matashi

Illar Da Zina Za Ta Yi Ga Rayuwar Matashi

Zuwa gare ka matashi: Zina ita ce tushen duk wani bala'i. Idan ka bijire wa dokokin Ubangiji, ba za ka taɓa samun albarkarSa ba a cikin al'amurranka.


Illar Da Zina Za Ta Yi Ga Rayuwar Matashi
Hoto: Gawrav/iStock photo

Idan ka kuskura ka aikata zina, to ka jefa kanka cikin wani tarko da ba ka da ranar fitowa daga cikinsa.


1. Za ta ɗaiɗaita rayuwarka, ta kassara mafarkanka/burinka, ta gusar da kwarjini daga fuskarka sannan ta tarwatsa alaƙar da ke tsakaninka da mutanen kirki.


2. Za ta zubar maka da mutunci hatta a idanunka, kai da kanka za ka bar ganin ƙima da mutuncin kanka, kuma hakan zai sa ka daina yin duk wani abu mai amfani ga rayuwarka. 


3. Za kuma ta haifar maka da shakku da tsoro da nadama a cikin ranka. Kullum kana ɗar-ɗar kamar wanda ya saci kaya yake tsoron a kama sa, saboda ka keta alfarman abin da Allah Ya tsarkake shi.


4. Za ka rasa ƙimar kanka da kaifin basira da azamarka sannan ka zama bawa ga sha'awarka. Tunaninka zai canza daga tunanin masu manufa zuwa tunani irin na dabbobi waɗanda ba su da aiki face ci da sha, da jima'i.


5. Ba a nan illar ta tsaya ba. Idan zina ta bi jikinka to ko ka yi aure ba za ka iya daina wa ba. Matarka ta halal ba za ta taɓa gamsar da kai ba, sannan za ka koma kallon duk wata mace da sha'awa wanda hakan zai sa rayuwarka ta tarwatse cikin gaggawa.


6. Kana tunanin za ka tsoma hannunka ne a cikin wuta ba tare da ta ƙona ka ba? 


Maganar gaskiya ita ce ba za ka taɓa tsira daga illolin wannan mugun aikin ba har abada. Don haka kada ka yi kuskuren afka wa zina, saboda illolin da za ta haifar ga rayuwarka ba su da iyaka. Duk a saboda gajeren sha'awa?


7. Zina ba wai zunubi ba ce kawai, amma kamar wata ƙofa ce da take shigar da mutum cikin wata rayuwa mai ɗauke da nau'o'in masifu da bala'o'i iri-iri.


8. Zina halaka ce kuma guba ce wacce za ta gurɓata zuciyarka da ruhinka, sannan ta wargaza rayuwarka. Za ta rugurguza iyalinka, da karatunka, da kasuwancinka, da sana'arka sannan ta raba ka da komai.


9. Za ta lalata alaƙarka da Mahaliccinka sannan ta bijirar da kai ga haɗurran shaiɗan da kuma haɗurran zuciyarka. 


Za ta cire maka nutsuwa a zuciyarka, kuma ko kana da dukkan abin da kake so ba za ka samu kwanciyar hankali ba.


10. Ka nemi aure, kuma ka fifita kamewa akan sha'awa na ɗan ƙaramin lokaci wacce za ta halakar da kai.


Aure yana da tsarki kuma yana da alfarma. Alƙawari ne wanda Allah da kanSa Ya zama shaida a ciki. Amma idan ka afka wa zina, babu kai babu tsarki, ko kariya da kiyayewar Ubangiji.


Daga nan za ka fuskanci duk rigingimun rayuwa a karan kanka. Babu kai babu jagorancin Ubangiji. Allah Ubangiji Ya mana kariya.


Duk abin da ba wannan ba kuwa tafarki ne da zai kai ka ga halaka da taɓewa!


Tushe/Asali: Hausa Motivation

Tuesday, 26 November 2024

Wanda Ka Raina Shi

Wanda Ka Raina Shi

Wanda ka raina, sai ka ga Allah Ya ɗaukaka shi. Kai dai kawai nema a wajen Allah Maɗaukakin Sarki.


Wanda Ka Raina Shi
Hoto: Namibian

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kar ka tsaya jiran wani ya taimaka maka.


Yi ƙoƙarin ka fahimci abin da kake son cimma a rayuwa.


Kada ka manta ba kowacce dariya ko murmushi da mutane suke yi maka yake zama so ba, amma ka sani a ko'ina ba a rasa na banza, haka ma a ko'ina ne ba a rasa na kirki.


Kai dai kawai miƙa al'amuran ka ga Allah (S.W.T).


Allah ya sa mu dace duniya da lahira Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Monday, 25 November 2024

Duk Ɗan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu

Duk Ɗan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu

WANNAN BABBAN SAƘO NE NA MUSAMMAN GA ƊAN SHEKARA 40 DA WANDA KE DAF DA CIMMA SHEKARU 40.


Assalamu alaikum warahmatullah.


Ina fatan kun tashi lafiya, Allah Ya ƙara lafiya da sutura duniya da lahira.


Bayan haka, haƙiƙa rayuwa cikin musulunci da ƙoshin lafiya ni'imomi ne masu girma da babu abin da mutum zai yi sai dai ya yi ta godiya ga Allah Ta'ala a kansu tare da nuna gazawa da ƙasƙantar da kai a gare Shi.


Duk Dan Shekaru 40 Ya Dakata Anan Yanzu
Hoto: DMP/iStock photo

Marubuci: Shehu Mansur Dala


Shekaru arba'in a duniya wani zango ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa wanda Allah Ta'ala ya nuna darajarsa domin a wannan lokaci ne Yake aiko manzanninsa masu girma. Kuma a wannan zango ne mutum yake zama kamili a kusan kowanne ɓangare na rayuwarsa, yake fara fahimtar haƙiƙanin rayuwa a bisa yadda take musamman idan ya samu kyakkyawar kulawa da ingantacciyar tarbiyya a baya.


Lokaci ne da tunani ya kan canja, abubuwa da yawa na salon rayuwa da jiki su sauya.


A lokacin farin gashi (furfura) yake kankama a kai da gemu, wasu ma tun kafin wannan lokacin ake ganinta.


Wani daga wannan lokaci alamun tsufa suke fara bayyana a gare shi, amma kuma a ilimance ba za a ce da ɗan shekara arba'in tsoho ba, amma yanayin rayuwa da tunani da cimaka na mutum shi ya kan sa ka ga yaro ya tafke, babba kuma ka gan shi kullum kamar yaro.


Waɗansu sukan firgice daga sun shiga shekara ta arba'in su ɗauka su tasu ta ƙare, mutuwa kawai suke jira musamman idan furfura ta yi gaggawar fesowa. Wannan kuskure ne domin idan shekaru 60 ko 70 aka yanka masa zai yi a duniya ai ka ga yana da sauran shekaru 20 ko 30 waɗanda zai iya yin abubuwa masu kyau da yawa a cikinsu.


Tsige furfura ko aske gemu don kada a ga furfurar mutum a ce ya tsufa haramun ne, ai haƙiƙanin tsoho shi ne wanda zuciyarsa da tunaninsa suka tsufa suka daskare, kuma ita furfura ado ce ga mumini kuma alama ce ta nutsuwa wacce take haifarwa da mutum kwarjini a idon mutane musamman idan an tsare mutunci.


Babu laifi a rina furfura da jar kala ko ruwan ɗorawa, amma a guji rina ta da baƙi.


CANZA SALON RAYUWA


Ya kamata ga ɗan shekara arba'in zuwa sama da ma wanda ya kusa kai wa arba'in ya canja salon rayuwarsa kamar haka:


ZUZZURFAR TUNANI


Mutum ya zaunar da kansa ya yi dogon tunani akan rayuwarsa ya gayawa kansa gaskiya ya tambayi kansa tambayoyi uku:


1 Shin me na aikata a shekaru arba'in da suka wuce? Waɗanne ire-iren nasarori na samu kuma waɗanne matsaloli na fuskanta a rayuwata?


2. Shin yanzu a wanne mataki nake na rayuwa, me nake yi?


3. Shin nan gaba me nake son yi? yaya kuma zan yi shi ?


TUNANIN ABUN DA ZA KA BARI


A yayin amsa tambaya ta uku ka yi tunani da aiki na gaske kan me za ka bari bayan mutuwarka wanda za'a riƙa tuna ka da shi ana yi maka addu'a saboda amfanarsa da mutane suke yi?


Wannan abu ne mai yiwuwa saboda mu dubi ɗimbin alkhairi da shugaban halitta ya bar mana mara yankewa wanda ya fara shi ne yana ɗan shekara arba'in. Ashe idan za mu yi koyi da shi ba za mu ce mun makara ba.


TUNANIN WA ZA KA BARI


Lallai a duk matakin da kake kai na rayuwa ka fara tattali da horon waɗanda za ka tafi ka bari domin ɗorawa daga inda ka tsaya a ayyukan alkhairi.


Idan kai Malami ne Malamai nawa za ka mutu ka bari a cikin ɗaliban ka waɗanda za su ci gaba da gwagwarmaya bayan mutuwar ka? 


Idan kai Ɗan Kasuwa ne ko wani mai sana'a ko ma'aikaci, attajirai nawa ko ƙwararru nawa za ka tafi ka bari waɗanda da an gan su za a tuna ka a yi maka addu'a?


Kai har 'ya'yanka ka yi tunani kuma ka tsara ka kuma yi aiki don ganin wanne irin samari da 'yammata da iyaye za ka tafi ka bar wa al'ummarka? Wacce irin gudummawa za su bayar wajen ci gaban zuri'arka da al'umma gaba ɗaya?


CANZA GABA-ƊAYAN SALON RAYUWAR KA


Kusan kowanne ɓangare na salon rayuwar ɗan shekara arba'in zuwa sama da wanda ya kusa kai wa arba'in yana da buƙatar sake nazari da canjin salon gudanar da shi.


Waɗannan ɓangarori sun haɗa da:


1. CAJA BATIRIN IMANI


Ya kamata a ƙara yawaita ibadu masu ƙara imani da tausasa zuciya. Idan kuma ba a yi to a fara.


Misali ƙiyamullaili, farkawa cikin dare domin yin salla da addu'a, aƙalla awa ɗaya ko rabin awa kafin sallar asuba domin a ribaci wannan lokaci mai matukar fa'ida da albarka.


Yin azumin nafila koda sau uku ne a kowanne wata.


Yawaita aikin hajji da Umara ga wanda yake a kusa da garin Makka ban da na nesa. Jaddada tuba da yawaita istigfari.


2. IDAN AN GIRMA A SAN AN GIRMA


Ya kamata wanda ya kai wannan mataki na rayuwa ya san fa yanzu ya zama babba wataƙila an fara tara 'ya'ya, kuma manya sun fara tafiya nauyi ya fara yin yawa, to ya kamata a bar hululu a yi sallama da halaye marasa kyau musamman shaye-shaye, da taɓe-taɓe, da ɗauke-ɗauke da fitintinu da 'yan uwa da maƙota da abokai, a yi sulhu da kowa, a rungumi zumunci, a tallafawa 'yan uwa da sauran mabuƙata.


3. ME KA YI WA ADDININKA?


Ya kamata kowa ya yi wa kansa tambaya wacce irin gudummawa yake bayarwa ga addininsa? Kuma mai zai tafi ya bari na ci gaban addini bayan rasuwarsa?


Wani sai ya zo duniya ya koma bai yi wa addininsa wani abun a zo a gani ba, sai dai kawai ya tara kuɗi ya sayi ƙasa ya yi abubuwa kala-kala ya tafi, shi kenan. Lallai ya kamata a sake tunani, musamman waɗanda Allah Ta'ala Ya ba su dama ta dukiya ko ilimi ko muƙami.


Za ka iya shiga kwamitin wa'azi da musuluntar da waɗanda ba musulmi ba da sauransu.


KULA DA LAFIYA


Ginshiƙan samun lafiyar jiki da ƙarkonsa su ne:


1. Cin lafiyayyen abinci: A yawaita cin ganyayyaki da kayan marmari na asali ba na gwangwani ko kwalba ba. A rage cin jan nama. A guji shan taba sigari da giya da dukkan kayan maye. A tsara lokutan cin abinci. A rinƙa yawan shan tsaftataccen ruwa.


2. Samun wadataccen hutu: A ƙalla a kullum a samu barcin awa shida ba tare da yankewa ba, a wurin da iska take gewayawa. In da hali a haɗa da barcin rana koda na mintina 15 ne.


A gujewa tara barci a ka musamman saboda kawai ana kallo ko amfani da waya.


3. Kaucewa yawan ɓacin rai: Mutum ya guji duk abin da zai jawo masa fushi da ɓacin rai. Idan kuma abin ya faru a yi haƙuri, a kai zuciya nesa. A daina riƙo da hassada da gaba. Waɗannan halaye na saurin tsufar da mutum da haifar da cututtuka musamman na damuwa da karya garkuwar jiki. Yawan murmushi da farin ciki na inganta lafiya da samun tsawon rai a duniya.


4. Motsa jiki: Lallai a kullum mutum ya tabbatar yana motsa jikinsa musamman ta hanyar tafiya a ƙasa, aƙalla tsawon mintuna 40 a kullum.


GEMU BA YA HANA KARATU


A yanzu bayan ka girma za ka iya riskar abun da ba ka samu damar riska ba a baya na karatun addini da na zamani.


Za ka iya shiga harkar koyon karatun Alkur'ani da haddace shi, da kuma majalisai ko makarantun ilimi.


Akwai manyan Malamai da sai da suka girma suka fara neman ilimi kuma suka zama bijimai hamshaƙan malamai irinsu Ibn Hazmi da Izzuddin Ibn Abdussalam da Al-Imamai Alqaffal.


Haka kuma za ka iya komawa makaranta domin kammala karatun boko da yanayi ya dakatar da shi koda kuwa ta salon karatu daga nesa ne ko kuma buɗaɗɗun jami'o'i.


Ka sani cewa ƙwaƙwalwar ka tana da buƙatar abinci lafiyayye wanda shi ne ilimi.


Yi ƙoƙari aƙalla a kullum ka ware awa guda domin karatu, ba lallai sai littattafan larabci ba, akwai littafai na Hausa masu yawa da ɗimbin fa'ida.


ƘARA INGANTA ZAMAN IYALI


Anan ma ya kamata a ƙara nazari akan yanayin zaman da ake yi, a ƙara ƙarfafa hanyoyin zaman lafiya a toshe duk wata kafa ta fitina da tashin hankali.


A ƙara kulawa sosai da tarbiyyar 'ya'ya musamman manyan cikinsu. A riƙa ba su lokaci ana zama da su ana tattaunawa da su.


Idan da buƙatar ƙara aure a yi shi cikin fahimta, a yi adalci kuma a tabbatar za a iya yi ban da rigima.


Sha'awar jinsi ita ce ƙarshen abin da yake ƙarewa ga mutum. Wani ma sai ya tsufa sai sha'awar ta dawo kamar ta matashi (balagar tsufa) ya kamata ma'aurata da iyalansu su fahimci haka kada a zalunci kowa.


Waɗannan su ne muhimman saƙonni da masana suke isarwa ga 'yan shekara arba'in zuwa sama da waɗanda suke dab da shiga arba'in domin tattalin nasarori da aka samu da ƙara haɓaka su da kaucewa matsalolin da aka gamu da su a shekaru masu zuwa da kuma samun damar kyakkyawar cikawa da barin zuri'a managarciya.


Domin samun cikakken bayani duba:


✓جدد حياتك رسالة إلى من جاوز الأربعين للدكتور محمد موسى الشريف

 

✓صحتك بعد الاربعين المعصومة علامة 

جدد حياتك لمحمد الغزالي


✓ريح النسرين فيمن بلغ الاربعين للشيخ محمد بلغوا بن عثمان بن فودي


Ina roƙon Allah Ta'ala Ya inganta rayuwar mu, Ya kyauta ƙarshenmu, Ya albarkaci zuri'armu, Ya tsare imaninmu gabaɗaya Amin.


Ku taimaka ku yaɗa wannan saƙon.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Maasallam.

Sunday, 24 November 2024

Babu Amsa

Babu Amsa

Mu dinga yi wa juna uzuri Dan Allah. Idan  kana ganin mutum a Online kodayaushe, hakan ba ya nufin ba shi da aiki ba ne, don haka kar ka yi masa mummunar fahimta.


Babu amsa
Hoto: Meaww

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Idan kana aikawa da saƙonni ka ga ba a dawo maka da amsa wato Reply, kar ka yi fushi, saboda ba kai kaɗai ba ne kake tura masa da saƙonni. Don haka ka yi masa uzuri.


Idan kana ganin mutum a Online cikin dare 12:00am,1:30am har zuwa 4:00am ko 5:00am, ka tura masa da saƙonni babu Reply wataƙila bacci ne ya ɗauke su.


Da yawa ba sa sanin lokacin da suke barin wayar akan yanar gizo-gizo wato Internet, musamman masu amfani da wayar Android, amma masu amfani da ƙananan wayoyi to su idan suka bar wayar tasu akan yanar gizo-gizo idan aka ɗan jima tana sauke kanta daga kan yanar gizo-gizo har sai dai idan kai ne ka ci-gaba da amfani da ita.


Dan Allah mu rinƙa kyautata kyakykyawar fahimtar junan mu.


ALLAH ya sa mu dace da dacewarsa Amin ya ALLAH.

Monday, 18 November 2024

Kowa Kotu Kawai

Kowa Kotu Kawai

Hmm Nigeria kenan, da an yi magana kotu, kowa idan abu ya yi zafi ba zai iya haƙuri ba sai ya ce "Mu haɗu a kotu.".


Kowa Kotu Kawai
Hoto: Chris Ryan/iStock photo

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kada ka biyewa son zuciya ko kuma abokai masu karancin tunani su kai ka su baro, saboda da yawa daga cikin su suna tare da kai ne domin su cimma manufar su a kanka.


A  ganina duk abin da haƙuri bai bayar da shi ba to tabbas akasin shi ba zai bayar ba.


Idan kai haƙuri komai zai wuce, sannan za ka ga nasara akan haƙurin da ka yi.


Nazari aikin mai hankali.


Allah ya sa mu dace Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Friday, 15 November 2024

Darasi A Rayuwa

Darasi A Rayuwa

Rayuwa gaba-ɗayan ta darasi ce ga mai hankali, haka kuma ilimi ce ga mai tunani da aiki da abin da ya ji ko ya gani, ya san yadda zai tafiyar da shi.


RAYUWA GABA ƊAYAN TA DARASI CE GA MAI HANKALI
Hoto: Be slick

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Duniya kuma makaranta ce, wasu sun yi nasara. Wasu kuma akasin ta.


Allah ya sa muna cikin waɗanda za su yi nasara anan duniya da kuma lahira Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Monday, 11 November 2024

Wasu Lokuta A Rayuwa

Wasu Lokuta A Rayuwa

Wataƙila sadaka ko kyautar ₦10 ba komai ba ce a wajen ka, har ma za ka yi tunanin ko ka bayar babu abin da za ta yi ma wanda ka ba shi, amma ba ka sani ba shi abin da yake nema kenan ya fita daga matsalar da ya samu kansa a ciki. Don haka da zarar ka ji zuciyar ka ta yi tunanin aikata alkhairi to ka zartar a aikace kawai, ba lallai ka sake samun wannan damar ba.


Wasu lokuta a rayuwa
Hoto: Yacobchuk1/Depositphotos 

Marubuci:- Muhammad Yahaya Bamalli


Saboda haka kada ka ƙaskƙantar da duk abinda ka ga wani yana so, kada ka wulaƙanta abin da wani yake buƙata, kuma kada ka raina abin da za ka taimaka wa bayin Allah da shi.


Wani lokaci a cikin rayuwa abinda ba ka buƙata, abinda ba ka ɗauke shi a bakin komai ba, shi ne abinda wani yake buƙata ya rayu cikin kwanciyar hankali, abin da bai da sauran amfani a wajen ka shi ne abin da wani yake nema ya tsira a rayuwa.


Wani idan bai samu wannan abin ba zai iya tagayyara a rayuwa, ko kuma ya faɗa cikin hatsari ko ya mutu, abinda ba ka bukata, abin da ka fi ƙarfin sa a yau, wani kuma idan ya samu, ya samu abin da zai rayu da shi cikin kwanciyar hankali kenan.


Abin da za ka bayar ɗin wataƙil shi ne fata na ƙarshe da wani da ke cikin wata rayuwa me ƙunci yake buƙata ruwa a jallo.


Wani yana ciwon kai, ba don ₦20 da ka taimaka masa da ita ya sayi magani ba da wataƙil ajalin sa kenan.


Rigar da kake ganin ka gama amfani da ita, saura ka jefar a bola, wani kuma da zai same ta zai je Masallacin Idi ko wajen ɗaurin auren sa da ita cikin alfahari da jin daɗi a zuciyarsa.


Kada ka jefar, ka yi kyauta, ka yi sadaka ɗan uwa, wani yana buƙata.


Kada ka raina abin da za ka bayar ma wani, ba ka san tasirin abun a wajen wanda za ka ba shi ba, ba ka san ƙarfin abin da ka bayar a can sama wajen Ubangiji ba.

Friday, 8 November 2024

Kyawawan Shawarwari 27 Ga Sabon Matashi

Kyawawan Shawarwari 27 Ga Sabon Matashi

Babu amfanin saka damuwa, idan abu ya faru, face fuskantar gaba. Babu amfanin haɗa kanka da wasu, saboda kowanne da irin ƙaddarar sa.


Kyawawan Shawarwari Ga Sabon Matashi
Hoto: IStock photo

Marubuci:- Muhammad Yahaya Bamalli


Shawarwari na musamman ga duk matashin da ya tunkari shekaru 30 zuwa sama.


Ga su kamar haka:


1. Ka yi iya yinka wajen gujewa bashi, sai idan ya zama dole, kuma da zarar ka samu sukunin biya to ka yi hakan da wurwuri. "Bashi ba ƙaramar barazana ba ce ga ci-gaba".


2. Shin ka san wane ne fallasasshe wanda za a yi ma wasoso ranar ƙiyama? Shi ne mutumin da ya je lahira da Sallah, Azumi, Zakka, Sadaƙa masu kyau amma ya zagi wancan, ya cuci wancan, ya ci kuɗin wancan, sai a kwashe ladarsa a biya su shi kuma a turashi wuta. Allah ya kiyaye mu.


3. Idan Allah ya hore maka aiki ko sana'a, ka dinga aje wani kaso komai ƙarancinsa, a asusun ajiyarka. "Ajiya maganin wata rana".


4. Bala'o'i 7 ne a gaban mu, kuma kowane 1 bai kai na gabansa masifa ba: (1). Mutuwa. (2). Kwanciyar kabari. (3). Tashin ƙiyama. (4). Tsayuwar ƙiyama. (5). Auna aiki. (6). Bada sakamako. (7). Hawa siraɗi. 'Yan uwa mu yi tanadi, mu yi shiri kafin lokaci ya riske mu. Allah sa mu cika da Imani.


5. Kada ka cutar da kowa, ka nufi kowa da alkhairi, domin rayuwar wani ba ta hana taka, samun wani ba ya hana naka, lafiyar wani ba ta cutar da taka lafiyar, abin da Allah ya rubuta kuma ya ƙaddara baya canjawa. To mene ne na hassada da ƙyashi?


6. Aƙalla ka samu abin yi fiye da ɗaya, "Gida biyu maganin gobara.".


7. Ka guji yi wa Allah shisshigi a kan makomar bayinSa, sai Ya yafe masu abin da kake zarginsu da shi, kai kuma Ya ɓata ayyukanka. Ka guji hukunci akan niyyoyin mutane, domin ba ka kutsa zuciyarsu ka ga abinda suka nufa ba.


8. A kowace safiya kafin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka iya wani sabon abu. Wayar da kake riƙewa makaranta ce babba "Ilimi kogi ne".


9. Idan har abinda mutane za su faɗa a kanka shi ne damuwarka, to haƙiƙa ba ka shiryawa rayuwa a duniya ba, domin wanda ya mutu ma bai huta ba a bakunan mutane. Ya Allah ka tsarkake mana zukatan mu, ka sa mu kasance masu faɗar alkhairi akan kowa Amin ya Allah.


10. Aƙalla kowanne mako ɗaya, ka yi ƙoƙarin karanta wani littafi. Akwai darussa da dama ƙunshe a cikin littattafai. "Ilmi haske ne".


11. Waɗanda suka rasu ba su yi gaggawa ba, mu da muke raye ba mu yi jinkiri ba, kowa lokacinsa yake jira. Kuma idan lokacin ya yi ba makawa sai an tafi. Allah ka ɗauki ranmu a lokacin da ka yarda da mu muna masu Imani.


12. Ka dinga motsa jiki aƙalla sa'a (awa) ɗaya a rana. "Mafi yawan cututtuka nada alaƙa da rashin motsa jiki.".


13. Ya kamata jiya ta ba ka darasi ka shiryawa yau, domin dacewa a gobe.


14. Ahir, kashedinka da zaman majalisa, a madadin haka yi wani abin da zai amfaneka da wannan lokacin, kodai koyon wani abu ko neman ilimi. "Zaman kashe wando illa ce babba, kuma hurumi ne na wanzuwar giba da annamimanci". Ba za ka gane muhimmancin lokaci ba sai girma ya same ka.


15. Ya kai Dan Uwa! Da kullum kana tuna masifa da bala'in da ke gabanka na mutuwa, kwanciyar kabari da tashin ƙiyama da ba za ka ɓata lokacinka kana bin diddigin laifuffukan wasu ka manta da kanka ba. Babu mai tambayarka aikin wani a lahira, aikinka za a tambayeka.


16. Ka yi tunani da kyau, mace idan ba mahaifiyarka ba ce ko matarka, ba abin da take ƙara wa rayuwarka sai ɗawainiya da wahala. Don haka ahir ɗinka da neman mata, kodai aure ko kuma sai dai gaisuwa, ko kuma kowa ya yi harkarsa. Ka ji ni ko?


17. Ka dinga tashi tunda safe domin tunkarar ayyukan ka na wannan rana. "Da sassafe ake kama fara".


18. Arziki da ɗaukaka a hannun Allah suke, wanda kake ganin ba kowa ba ne gobe sai ka ga Allah Ya maida shi wani, wanda kake ganin wani ne gobe kuma sai ka ga Allah Ya maida shi ba komai ba.


19. Mace duk nagartarta sai tana ƙaunarka za ka mori zama da ita, don haka ka nemi mai ƙaunarka kuma mai tarbiyya.


20. Ka daina ƙasƙantar da mutane saboda ka fi su matsayi. Idan Allah Ya ga dama gobe sai ka gan ka a ƙasansu. 


21. Duk inda ni'ima take dole a tarar da 

mahassada.


22. Ba abinda ke da rashin tabbas kamar wannan rayuwar. Komai mai iya canzawa ne a kowanne lokaci.


23. Kowane yini/wuni kafin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka taimaki wani, koda sadaka koda shawara kai koda da bai wa ƙadangaru ruwan sha ne. Kar ka manta, wata karuwa ta samu gafarar Allah sakamakon yin taimako irin wannan.


24. Idan ba za ka iya yaɗa alheri ba kar ka taimaka wurin yaɗa sabon Allah a doran ƙasa.


25. Tallafawa iyayenka da komai ƙanƙantar abin da Allah ya hore maka, koda kuwa suna da sukuni. Akwai albarka sosai a taimakawa iyaye da yi musu biyayya.


26. Duk inda ɗaukaka take dole a tarar da maƙiya, kai dai ka riƙe addu'a.


27. Kada ka riƙa tallata talaucinka a wurin da babu maganin shi.


Haƙuri wata babbar baiwa ce ba kowa ALLAH yake azurta shi da ita ba, sai ɗaiɗaikun mutane.


Kowane Ɗan-Adam mai kuskure ne, sai da yafiya da haƙuri ake zama lafiya da mutane.


Duka waɗannan shawarwarin matakan nasara ne.