Sunday, 24 August 2025

Gaskiya Magana Kan Kalmar Zafin Nema Ba Ya Kawo Samu

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan ana so a kwantarwa mutum hankali, sai ana masa wannan karin magana: “Zafin nema ba ya kawo samu.” Amma idan ka tsaya ka yi tunani, za ka tambayi kanka, “to, me yasa Allah ya ce tashi in taimake ka?”


Gaskiyar magana kan kalmar zafin nema ba ya kawo samu
Hoto: Ridofranz/Getty images

Marubuci:- Dahiru Aliyu Musa


Gaskiya ne akwai lokaci, akwai rabo, kuma Allah yana ba wa wanda ya ga dama a lokacin da ya ga dama. Amma hakan ba yana nufin ka haƙura da ƙoƙari ba, ko ka zauna jiran abin ya faɗo maka daga sama. Sau da yawa, hanyar da Allah ke amfani da ita wajen kawo maka abin da aka rubuta maka ita ce ƙoƙarinka.


Samu yana zuwa ne ga mai neman sa, kamar yadda nasara take zuwa ga mai jurewa wahala da dagewa.


Ka duba manoma. Suna shuka iri da kyau, suna yin aikin noma daga safe har yamma. Su ba sa cewa “idan rabonmu ne za mu girba.” Sun san aikin su shi ne shuka, Allah kuma shi ne mai sa amfanin ya fito.


Ka duba ɗalibai. Ba su zauna a gida suna addu’a kawai su ce “idan rabona ne zan ci jarabawa.” Suna karatu, suna nema, sannan su dogara da Allah don ya sa musu albarka.


Ko ’yan kasuwa. Ba su zauna suna jiran kasuwa ta kawo musu kuɗi ba. Suna tashi da safe suna neman dama, suna jurewa, sannan suna sa ran Allah ya saka musu nasara a neman su.


Don haka, wannan karin magana tana da ma’ana, amma ba cikakkiya ba ce. Abin da ya dace shi ne ka dage, ka nema, sannan ka bar sakamakon a hannun Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user