Saturday 23 May 2020

A Karan Farko Malaman Addini Sun Fara Bijirewa Umarnin Sarkin Musulmai a Nigeria Muhammad Sa’ad Abubakar III

Tura Wannan Zuwa
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya faɗi matsayarsa dangane da yin Sallah ranar Asabar.

Matsayar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

A wannan ɗan taƙaitaccen bidiyo mai matsakaicin zango malamin ya faɗi dalilin da yasa ya gamsu dayin Sallah a ranar asabar saɓanin sauran al'ummar ƙasar Nijeriya mafi yawancin su a gobe Lahadi zasu yi bikin idin ƙaramar Sallah.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye....

Shehin malamin ya bayyana yau a matsayin ranar Sallah, inda ya ƙara da cewa, anga wata a wasu garuruwan ƙasar don haka su sun ajiye azumin, a cewar sa yau ɗaya ne ga watan shawwal.

A ƙasar Niger maƙwabciya ga ƙasar Nijeriya yau take idin ƙaramar sallah, a ƙasar Saudiyya gobe Lahadi ne ranar idin ƙaramar sallah wanda yayi dai-dai dana ƙasar Nijeriya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user