Monday 17 June 2019

KARANTA ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA GUDA 32 MASU RATSA ZUKATAN MASOYA MAZA DA MATA NA ZAMANI

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng muka shahara wajen kawo muku labaran Soyayya har ma  da Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zukatan Masoya , A Yau mun kawo muku wasu daga cikin Rubutattun Sakonnin Soyayya  guda Talatin da Biyu (32) masu ratsa zukatan masoya.

Soyayya Ruwan Zuma

Kada Ku Manta dayin Subscribe na Channel din  mu a Youtube MURYAR HAUSA24 TV ko kuma ku Biyo mu a shafin mu na Yanar Gizo a www.MuryarHausa24.Com.NG

Idan ba zaku manta ba a kwankin baya mun kawo muku Sakonnin Soyayya Guda 32 cikin Audio  Insha Allah a yau kuma ga rubutattun  sakonnin soyayya 32 domin kara dankon soyayya.

NA ‘DAYA.

Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya,

haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.

NA BIYU.

A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin ɗaya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki,

Domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a kowanne lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada.

 Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.

NA UKU.

Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyar tawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su.

 Ina son ki saboda zuciya ɗaya.

NA HU’DU.

Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shuɗewa soyayyar ki na ƙaruwa a cikin zuciyata,

 A lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta,

Kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina ƙaunar ki.

NA BIYAR.

SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matukar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu?

Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya.

Karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.

NA SHIDA.

SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai ƙona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.

NA BAKWAI.

Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.

Na san burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba.

Ina son ki fiye da gwal ko kuɗi.

NA TAKWAS.

Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA”

Hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada.

 Ina son ki.

NA TARA.

Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada daɗewa ba domin ki tabbatar da abun da na ke faɗa gaskiya ne, dama an ce zuwa da kai ya fi saƙo.

 Ki huta lafiya farin cikin zuciyata.

 Ina son ki.

.....
Duk wani hoto wanda kaga ni a jikin wannan Video Idan Ka/Ki san me hotan, ba muyi amfani da hotan Ka/Ki domin wata manufa ba , sai dai kawai domin isar da saƙon cikin Nishaɗi.

Dafatan Kai/Ke zaku yi mana Kyakykyawar Fahimta.

Mungode!
.....
KIN ZARCE SAURAN MATA.

10. Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata.

 Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.

SINADARIN RAYUWA TA.

11. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki.

 Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

ZAN SO KI JI.

12. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta.

Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!

KE CE MURMUSHI NA.

13 Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya.

 Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba.

Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.

14. Ni M. Kabir Muhammad Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..

Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fika-fikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne?

 Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shauƙi a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke….

Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

HMM!! KI YARDA DA NI.

15. A dukkan lokacin da dare ya yi, ki ɗaga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki.

Karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm!

 Ki Huta Lafiya.

INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA.

16. A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya.

 A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare.

 Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.

 Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.

A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.

17. Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.

Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwan ki.

Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.

HARSHEN ZUCIYA.

18. Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye.

 Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.

BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.

19. A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba.

 Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba.

Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari.

 Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.

20. Masoyiya ta Halimatut Sadiya, Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne?

Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske?

 Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wacce ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni ɗaya cikin kaɗ’aici a dare ko safiya.

Ke ce abar so na.

21. A duk lokacin da na zauna ina yin nazari a dangane da soyayyar mu, sai nai hasashen  cewa dama a ce fika-fikai za su bayyana a jikina da na nausa da ke izuwa kayatacciyar fadar dake can babban birnin masoya na sabuwar duniyar mu domin sada ki da kujerar alfarma ta mukamin sarauniyar ‘yan matan duniya da na dade da baki.

Shin Halima kin kuwa lura da cewa ina neman na zama zautacce a cikin soyayyar ki?

Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan iya fita ba.

Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki.

 Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta.

Fatana dai mafarkina ya zamo gaskiya a dangane da ke.

DOWNLOAD SABABBIN KALAMAN SOYAYYA AUDIO/VIDEO HERE


NA.MATA...

22. Tsuntsaye na buƙatar fuka-fukai domin tashi, kifi na buƙatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina buƙatarka domin na yi rayuwar farin ciki.

 Ina son ka ya masoyi na!

23. Ina son jinka a kusa da ni M. Kabir , ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare.

Mu kasance a tare har abada.

Ina Son Ka masoyi na!

24. A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka.

Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka.

Saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya wata rana.

 Ina Son Ka!

25. Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa faɗuwarta a cikin kowace rana har abada.

 Ka Huta Lafiya.

26. Ina fatan ka fahimci manufa ta? Ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ƙarshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na.Ina Son Ka!

27. Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowacce rana.

 Ina son ki matata.

Babu wani abinci da yake yi min daɗi a baki na matukar ba ke kika girka shi ba.

Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai daɗi.

Ki kula min da kanki.

28. Mata ta uwar ‘ya’ya na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni.

 Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na.

Son Ki.Ina

29. Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna.

Amma ina son ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matuƙar so da ƙauna ba.

 Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki.

 Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.

DOWNLOAD SABABBIN KALAMAN SOYAYYA AUDIO/VIDEO HERENa Mata.


30. M. Kabiru Muhammad Hasken idaniya ta, annurin rai na.

Miji na, uban ‘ya’ya na.

Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata.

Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a  a duniya.

Ina fatan dawowarka gida lafiya, miji na abun alfahari na.

31. Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta.

 Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka kula min da kanka.

.....

32. Ina musanta cewa ina matsantawa a soyayyar ki amma zuciyata ta tabbatar da hakan, lokaci na wucewa soyayyar ki na karuwa a cikin zuciyata.

Kina da tattausan murmushi, kin kasance ma’abociyar kyakkyawar fuska, ina mai tabbatar miki da cewa babu wata da zata iya maye gurbin ki a cikin zuciyata.

Ki huta lafiya.

DOWNLOAD SABABBIN KALAMAN SOYAYYA AUDIO/VIDEO HEREFARIN CIKI BA YA SAMUWA SAI DA SADAUKAR WA A SOYAYYA.

Duk wata mu’amala tsakanin mutane biyu, matukar za a yi ta yau da kullum, to lallai ne a gamu da ciwonta sannan kuma a gamu da waraka wata rana, kwatankwacin soyayya da ita ma ake gamuwa da hakan a cikin ta.

 Tabbas farin ciki ba ya samuwa sai da sadaukarwa.

Zubar da hawaye game da soyayya lallai ne, domin ranar da za ka ga masoyin ka cikin wani yanayi marar dadi kuma ba ka iya magance shi, lallai dole ka yi hawaye.

 Babu yadda za a yi ka yi soyayya ba tare da ka zubar da hawaye ba, matuƙar dai soyayyar ta gaskiya ce, domin kuwa rayuwa tana tattare da abubuwa biyu ne, bakin ciki da farin ciki.

Idan watarana an sha zuma to wata rana madaci ake sha.


Kada Ku Manta dayin Subscribe na Channel din  mu a Youtube MURYAR HAUSA24 TV ko kuma ku Biyo mu a shafixan mu na Yanar Gizo a www.MuryarHausa24.Com.NG


Domin sauke Kalaman Soyayya cikin Audio/Video sai ku hanzarta shiga link din dake kasa.


DOWNLOAD SABABBIN KALAMAN SOYAYYA AUDIO/VIDEO HERE


KADA KU MANTA KU TURAWA 'YAN UWA DA ABOKANAN ARZIKI MUSAMMAN SAMARI DA 'YAM MATA DAGA
NAN WWW.MURYARHAUSA24.COM.NG MUNGODE.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user