Friday 6 November 2020

Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata

Tura Wannan Zuwa Ga

ZUWA GA MASOYIYA TA


KIN YI WA SAURA NISA


Son Ki ya mamaye dikan zuciyata. Ina kallon ki ne tamkar tauraruwar nan da ta yi wa saura nisa. Ki huta lafiya.


DOMIN MASOYA

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


BANI DA KAMAR KI


Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-cikin furta su gare ki su ne..... Kodan na san tini kin daɗe da sanin adadin yadda nake son Ki, nake kuma ƙaunar Ki sai dai kawai na ce bani da kamar KI. Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba har abada.


KIN ZAMO FITILAR ZUCIYA


Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane face fitila wadda ke kunnuwa a dukkan lokacin da na sanya idanuwana a cikin naki. Ina son Ki fiye da yadda alamun hakan ke bayyana a saman fuskata. Ki huta lafiya.


KIN ZAMO CIKIN TINANINA


Kina daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce mutuwa ce. Ina Son Ki.


KI KALLI SAMANIYA


Ki kasance mai ɗaga kanki Ki kalli sararin samaniya a cikin kowane dare, karda ki furgita a lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma na samu ganin wata tauraruwa mai haske idaniya da kore damuwar zuciya wato ke. Ina Son Ki.


KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE A CIKIN BACCINA


A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma'abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata. Ki Huta Lafiya.


KO KIN SAN HAKAN NA FARUWA A KANSA SABODA KE?


Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tinaninki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya buƙatar hotonki. Karda ki yi tinanin wani ne na daban face ni. Ina Matuƙar son Ki kamar yadda kika daɗe da sanin hakan.


BURINA KI KUSANTA DA NI


Da akwai wata ƙaya a cikin zuciyata, wadda ta kasance cikin sukana a dukkan lokacin da na tina tazarar da ke tsakaninmu. Da ma a ce zaki mayar da ni wani sashe na zuciyarki na tabbata da na samu sassauci. Abu mafi soyuwar furtawa a gare ni zuwa gare ki shi ne, Ina Son Ki.


KALMOMI SUN YI KAƊAN WAJEN BAYYANA YADDA NAKE SON KI


Masoyiyata, ina son na sanar da ke adadin yadda nake son Ki a cikin zuciyata, sai dai kuma, na rasa samun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana hakan a gare Ki. Ina son ki. Ki kula min da kanki.


KARDA KI ƊAUKI HAKAN A MATSAYIN ALMARA


Da a ce a yau zan samu fukafukan tashi, na tashi izuwa sararin samaniya, na je na gano taurari, na sauko izuwa doron duniya, bana fatan Ki tsunduma cikin matsanancin mamaki a lokacin da na bayyana miki cewa kin yi kama da ɗayarsu wato Zara.

 

ZUWA GA MASOYI NA


ZAN YI RAYUWAR ƘUNCI IDAN BABU KAI


A dukkan lokacin da ka furta baka so na, babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwa a cikinsa face kabari, domin kuwa na san daga ranar duniya za ta zamo  wajen zubar hawayena. Ina Son Ka.


AKWAI WANI SIRRI CIKIN IDANUWANKA


Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon soyayyarka, ka ɗana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli ƙwayar idanuwanka, na kan ji wani shauƙi mara misaltuwa. Ina Son Ka.


KAI NE ABUN SON KALLON IDANIYATA


Ina cikin kewarka, ina cike da ɗaukin son ganin Ka, a cikin kowace rana son ka na lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda fatar bakina za ta iya furta hakan. Ka huta lafiya.


BANA FATAN CANJUWAR RA'AYINKA A KAINA


Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a damuwa shi ne, ka samu wanda kake so shi kuma a lokacin ya faɗa a son wata. Bana fatan hakan ya kasance a tsakanina da kai. Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina Son Ka!!! Masoyina.


FATANA MU KASANCE TARE HAR ABADA


So abu ne mai wahalar da zuciya da kuma sanya ta nishadi. Zan so ka kasance cikin bani kulawa domin gujewa faɗawa wahalar ta so. Ba zan taɓa canja ra'ayina a kan ka ba har abada. Ina Son Ka.


ZUWA GA MATA TA


KIN HASKA DUNIYATA


Samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san zahirin siffa ta SO. Sai bayan da muka yi aure na ƙara fahimtar soyayya ta gaskiya. Ina fatan mu kasance a tare da juna na tsawan rayuwa har zuwa gidan Aljanna. Ina matuƙar Son Ki matata. Amma a lokacin da na dawo gida za ki ƙara tabbatar da hakan. Hmm! Ina nan cike da zumuɗin son zuwa cin girkinki mai daɗi.


ƊAYA TAMKAR DA GOMA


Da akwai wata mace a cikin wannan duniya, wadda ta yi daban da sauran matan dake a gidajensu na aure. Ita ta kasance ta daban ce, halayanta kuma ababen so ne. Ba kowa bace face Ke, a saboda haka nake ƙara son Ki a kullum. Ki kula min da kan ki, har zuwa lokacin da zan dawo gida kulawarki ta dawo hannuna. Ina Son Ki Matata.


ZUWA GA MIJINA


SHIN KO KA LURA DA HAKAN?


Zuciyata ta riga ta saba da kai, ta yadda nake iya jin tamkar na zamo cikin jakarka a dukkan lokacin da ka tashi fita. Da tinaninka nake wuni idan ka fita, sai kuma ka dawo nake samun sukunin yin murmushi. Ina Son Ka Mijina.


HM! HMM!! HMMM!!!


Karda ka so ɗaya, kuma karda ka so biyu, amma dai ka ci-gaba da son ɗaya wadda ta mace a kan son ka. Mijina kai ne abun alfaharina da kuma 'ya'yana. Ina Fatan Dawowarka Gida lafiya.


DUBA WANNAN: HANZARTA SAUKE ZAFAFAN SAKONNIN SOYAYYA AUDIO ANAN


WANNAN SAƘON ZUCIYATA NE ZUWA GA MALLAKINTA


Kalmomi na kasancewa ma'abota sauƙi wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar. Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan ka nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ka kasance mai kare min kanka daga harin da sauran mata zasu ke kawo maka a duk inda kake. A dawo lafiya.


SAKO MAI MUHIMMANCI

Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user