Friday 5 July 2024

Karanta Kayataccen Labarin Soyayyar Maryam Da Muh'd Labarin Ya Faru A Gaske

Tura Wannan Zuwa Ga

Shekararsa ashirin ya fara soyayyar gaske inda ya ci karo da wata yarinya mai suna Maryam, sanye da tufafin makaranta a jikinta da alama dai daga makaranta take.


Kayataccen Labarin Soyayya
Hoto: We Heart 


Marubuci:- Buhari Isma'il


A wannan lokacin ya yi ƙoƙarin sanar mata da halin da zuciyarsa take ciki na game da son ta amma sai ya kasa don ganin yadda kyawunta yake sannan yana gudun kar ta wulaƙanta shi, ya nemi ya je gidan su domin ya faɗa mata sirrin zuciyarsa amma hakan ma ya gagara.


Haka kullum yake kwana ya tashi da ita cikin zuciyarsa duk da cewa har a wannan lokaci bai ma san mene ne Soyayya ba sai daga nan ya fara sanin halin da Masoya suke ji.


Maryam dai fara ce tas, ga ta da gashi, hancinta dogo ne sosai, idanuwanta manya, bakinta daidai misali. A taƙaice dai Maryam kyakkyawa ce ta ƙin ƙarawa domin gidan su buzaye ne, haka zuciyarsa ta kamu da son ta.


Kwatsam! watarana sai aka tashi bikin ƙanwar wani abokinsa, aka zo wajensa domin neman alfarmar motar zuwa wajen Party da kuma kai Amarya, a wannan taron bikin ne idanuwansa suka sake yin arba da kyakkyawar fuskar Maryam ita ma ta zo wajen bikin.


Sai dai kuma nan ɗin ma bai iya dosarta ba, ya rasa yadda zai yi ya ɓullowa wannan al’amari domin isar da saƙon zuciyarsa.


Ya yi tunani mai tsawo sai ya ga mai zai hana ya samu abokin nasa ya sanar masa? Nan fa ya same shi ya sanar masa da halin da yake ciki na soyayyar Maryam wanda ya faɗa ciki, abokinsa ya ce _“in dai Maryam ce ta kwana gidan sauƙi domin a motarka ma zan sa maka ita, sauran zance kuma ya rage naka.". Ya yi dariya, haka kuwa aka yi ya saka masa Maryam cikin motarsa da ita da ƙawayenta, ya ji daɗin hakan sosai murna duk ta bi ta ishe shi saboda ganinsa da ya yi da Maryam.


Suna tafe yana satar kallonta don daman a gaba ya saka masa ita, ita ma ɗin satar kallon sa take yi duk da dai ita bai san dalilin da ya sa take satar kallon nasa ba, suka ci gaba da tafiya sai daga can ya ce mata _“Ni kuwa kamar na san ki”_ ta yi murmushi sannan ta ce _“An ya kuwa, a ina ka san ni?”_ Ya kalleta yana murmushi ya ce "A nan mana”. Sai gabaɗaya ƙawayenta suka sheƙe da dariya. A haka dai suka ci gaba da tafiya suna hira har kuma ta saki jiki dashi su kai ta zuba hira.


Bai tsaya sanya ba, ya nuna mata cewa yana son ta ba tare da jinkiri ba ita ma ta nuna amincewarta gare shi ta ce tana son sa. A taƙaice dai a wannan rana shi ne ya kai su ya dawo da su ya kuma maida su gida, kuma nan ne Maryam ta ba shi lambar wayar mamanta, daga nan suka fara soyayya, har ya san ma mene ne so.


Suna waya sosai kuma yana zuwa gidan su sosai, ya yi dace da iyayen Maryam ɗin su wayayyu ne, ba su da wata matsala ko damuwa.


Yana son Maryam sosai son da bai san iya ƙarshen sa ba, son da ba zan iya kwatanta muku irinsa ba, haka ita ma Maryam ta na son sa son da ba shi da iyaka, ta kuma nuna masa Ƙauna kamar yadda ya ƙaunace ta, ta kai ta kawo Maryam duk inda za ta fita sai ta faɗa masa saboda tsabar son da take masa da kuma ƙaunar junan su da suke, kai duk wasu 'ƴan uwanta na jini da sauran ƙawayenta sun san shi sun kuma san abin da ke tsakaninsu batun soyayya ne.


Yakan yi wa Maryam hidima iri-iri da duk wasu wahalhalu ba tare da ta tambaye shi ba, babban burinsa a kullum bai wuce ya farantawa Maryam rai ba, hakazalika duk wani abu da ya san zai iya ɓata mata rai zai iya rabuwa da shi ko mene ne, wannan ya sa suka zama haɗaɗɗun Masoya sosai, har ƙawayenta da abokansa ke kiransa da Mr. Maryam ita kuma su kira ta da Mrs. Muhammad.


Sau uku Maryam na zuwa gidan su gaida Mahaifiyarsa, ganin mahaifiyarsa ba ta ce masa komai a kan Maryam bai gamu da ɓacin ran ta ba, ya sa ya daɗa sakankancewa da zai auri Maryam.


Wata rana yaron mahaifinsa yake faɗa masa cewa ya cire soyayyar wannan yarinya domin Buzaye ne kuma Buzaye ba sa bada aurensu da bare wanda ba buzu ɗan uwansu ba, shi ma ba bashi za su yi ba. Shi dai bai bi ta kansa ba don ya san kawai ya faɗa ne musamman yadda ya ga ya karɓu sosai a cikin gidan su har ma da wajen gidan su, kai har ma da dukkanin 'ƴan uwanta, kuma hakan da ya faɗa ya daɗa ba shi damar ƙara sonta.


Sun shafe shekara huɗu (4) shi da Maryam suna ta raya fure, kullum soyayyar su ƙaruwa take, bai taɓa kwana ba tare da ya ji muryar Maryam ba, haka zalika bai taɓa kwana uku ba tare da ya ga Maryam ba, don a kullum sukan kwana suna waya tare kuma koda yaushe suna haɗuwa su ga juna.


Wata rana ƙawayen Maryam Safiya da Fauziya suka same shi suka faɗa masa cewa “An kusa bikin Maryam don yanzu haka ma an kawo mata kuɗin aure". Shi dai ya ji su kawai domin ba yarda ya yi ba, don babu yadda za a yi hakan ta faru bai sani ba, yarinyar da ko fita za ta yi sai ta sanar masa, wannan zancen dai ya ji shi ne amma bai yarda da shi ba.


Bayan wasu kwanaki ya yi bincike a kan abin da ƙawayenta suka faɗa masa ya gano gaskiya.


Washegari da sassafe misalin ƙarfe 6:12am ya kira ni yana sumbatu yana cewa; _“Maryam ta cuce ni, ta yaudare ni, kuma ta ci amana ta duk irin son da muke wa junanmu amma ta kasa faɗan, Maryam ta zalunce ni. Me ya sa Maryam ta yi min haka? Daman can ba sona take ba? Wanne irin laifi na yi mata wanda ta ƙudurce yin hukunci ta wannan hanya? Ko da a ce na mata laifi bai kamata ta hukunta ni ta haka ba kodan irin shafe shekarun da muka yi muna soyayya, bare ma na san babu wani laifi da na yi mata. Toh! A kullum cikin farantawa junan mu muke, amma sai ga shi an kawo kuɗin Maryam har da saka rana ko kaɗan ba ta taɓa furta min ba.".


Wannan labarin gaskiya ne wanda ya faru akan abokina, a yanzu haka dai Maryam tuni ta yi aurenta ta auri wani, amma duk da haka ya ce har yanzu yana sonta duk da abin da ta yi masa, amma dai ta cuce shi a cewarsa.


Wanda labarin ya faru da shi shi ne Muh'd Sulaiman.


SHAWARA


Masoya sai a kula a daina zurfafa soyayya cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da an fara tabbatar da haƙiƙanin son da masoyi yake wa abokin soyayyar ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user