Monday 21 October 2024

Zafafan Kalaman Karfafa Gwiwa Na Musamman

Tura Wannan Zuwa Ga

Dole ne ka tashi ka jajirce domin cikar burinka. Mutane  da dama suna mutuwa cikin mummunan talauci ba wai don ba su da ƙarfi ko wayewa ba, sai don sun rasa jajircewa a kan abun da suka saka a gaba, kowanne mai kuɗi ko mai mulki idan ya ba ka labarin wahalar da ya sha sai ka ji kamar ka yi kuka amma a yau ya zama abun kwatance ga sauran al'ummar duniya. 


Kalaman Ƙarfafa Gwiwa  Na Musamman
Hoto: Ramsey voice

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Shin labarin Albert Einstein bai zo maka ba?

  

Mutumin da aka haifa har ya shekara huɗu ba ya iya magana har ya kai shekara tara 9 Malam Albert maganarsa ba ta fita ya kan yi magana kamar mai shanyayyiyar murya, wasu malamansa ba su taɓa tunanin shi ba nakashashshe ba ne ta ɓangaren harshe.


A shekararsa ta 16 a  duniya wato a 1895 ya kasa cin jarrabawar shiga makarantar Swiss Poly Technic wadda take a Zurich amma hakan bai karyarwa da Malam Albert gwiwa ba, bayan shekara ta zagayo ya ƙara gwadawa ya samu nasara da ƙyar.


Bayan kammala karatunsa na jami'a ya fita da kwalin da ba yabo ba fallasa ya ci gaba da watangaririya a titi na rashin tabbas ɗin inda ya kama.


Da ƙyar ya samu aikin siyar da inshora yana bi ofis-ofis domin tallata hajarsa, bayan shekaru biyu ya ga hakan ba wani ci-gaba ya nemi aikin koyarwa bai samu ba da ƙyar ya samu aikin mataimakin magatakarda a ofishin bada lamuni na swiss wato a turance ana kiransa da (Patent clerk at the Swiss Federal Office for Intellectual Property in Bern.)


Albert Einstein yayin gabatar da wani jawabi kan Kimiyya da Wayewar Kai a 1933
Hoto: Keystone/Getty


Tabbas shi ne wannan mutumin da a yau  duniyar ilimi take tunƙaho da shi musamman ɓangaren ilimin kimiyya ta ɓangaren physics, tasirin photoelectric da Einstein ya gabatar  ta haka ne aka samar da  bom ɗin Atom, haƙiƙa Albert Einstein ɗaya ne daga cikin manyan masana kimiyya na ƙarni na 20, kodayake shi a matsayinsa na masanin kimiyya, ba shi da hannu kaitsaye a ƙirƙirar bam ɗin atom, wasiƙar da ya rubuta zuwa ga shugaban Amurka na lokacin ya fara farawa. Daga baya ya yi magana a bainar jama'a don yin kakkausar suka kan amfani da bama-baman nukiliyar, wanda ya kai ga halaka mutane da dama a japan.


Shin ko ka san malam Albert Einstein har koyarwa ya nema a makarantar sakandire bai samu ba saboda rashin kyawun sakamakonsa na jami'a?


Tabbas jajircewar Sheikh Albert Einstein ce tasa yau shekara 67 da yin mutuwarsa ake matuƙar ji da shi a ɓangaren kimiyya da sauran ilimai na turawan yamma, ya kuma kasance jagoran dukkan masana falsafa ta ɓangaren kimiyya da fasaha kuma mutumin da duniya ba za ta manta da shi ba tabbas.


"I want to go when I want to go. It is tasteless to prolong life artificially. I have done my share; it is time to go".


Fassara


"Ina so na tafi lokacin da nake son tafiya. Ba shi da ma'ana  don tsawaita rayuwa ta hanyar wucin gadi. Na yi rabona; lokacin tafiya ya yi".


Wannan itace maganar ƙarshe ta imamuna Albert Einstein.


Makomar mu tana ga abubuwan da muke aikatawa a yau.


Kada rashin nasara ya sa ƙarfin gwiwarka ya ragu wani lokacin da ma sai rayuwa ta juya maka baya hikimomin nasara suke zuwa ƙwaƙwalwarka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user