Wannan saƙon na shirya shi ne musamman saboda 'yan'uwana matasa, duk da cewa kowa zai iya ɗaukar darasi a cikinsa.
Akwai waɗanda ba su san inda rayuwa za ta da su ba, kawai dai suna kwana ne suna tashi haka nan.
Yawanci za ka same su da waɗannan siffofin:
1. Rashin manufa a rayuwa.
Ba ka da wata manufa da ka sa a gaba a rayuwarka, sannan ba ka da tunani ko tsari na dogon zango.
Idan za'a tambaye ka mene ne burin da kake so ka cika a rayuwa kafin ka bar duniya? Ba ka sani ba.
Idan za'a tambaye ka abinda ka tsara kake so ka zama nan da shekaru biyar ko goma, to ba ka da wani abun faɗa.
Kai dai kawai ga ka nan rayuwa kake yi.
2. Ba ka neman ƙarin ilimi ko sani.
A kullum samun sabon ilimi shi ne ya ke gina tunaninka kuma ya haɓɓaka ƙwaƙwalwarka da basirarka.
Dole ne a kodayaushe ka kasance kana neman ilimi, ko dai:
• Na Addini ko
• Na zamani ko
• Na wayar da kai ko
• Na sana'arka ko ƙwarewarka, da sauran su.
Idan ka wayi gari ba ka neman ilimi kowanne iri ne, to rayuwarka ta hau tafarkin lalacewa.
3. Kana fifita shagali da sharholiya.
Kullum aka neme ka za'a same ka a wurin shagulgula da wasanni.
Idan ba ka je kallon ƙwallo ba, to kana Event center ko ka fita ganin budurwarka.
Idan ba haka ba kana gurin fati ko walima ko gurin bidiri, ko ka je a tura maka fim a waya.
Kana tunanin more rayuwarka kake, ba ka san lalata ta kake yi ba.
4. Ba ka da ra'ayin kanka (Ba ka san me kake so ba).
Ka zamo tamkar busasshen ganyen bishiya a lokacin da goguwa/guguwa ta ɗauke shi, sai yadda ta yi da shi.
Yau a kaɗa ka nan, gobe a kaɗa ka can.
Ba za ka iya zama ka nutsu ka faɗawa kanka abin da ya dace da rayuwarka ba.
Kullum cikin sauraren ra'ayin wasu kake yi saboda ba ka da tsayayyar manufa.
5. Ba ka san kimar lokaci ba.
Masu hikima su kan ce, "Lokaci shi ne rayuwa."
Idan kana so ka samu babbar alama na cewa mutum bai san ciwon kansa ba, to babu kamar tozarta lokaci.
Abin mamaki a ce matasa su ke:
• Bacci har awa 12 a yini/wuni.
• Kallon fim mai episode 200 a wata.
• Ɓata lokuta marasa adadi.
Idan ka samu kanka da wasu daga cikin waɗannan halayen da aka ambata, to lokaci ya yi da za ka ma kanka faɗa.
Ka samu wuri ka keɓe ka yi dogon nazari akan abubuwan da kake yi waɗanda ba su da wani amfani.
Sannan ka musanya su da halaye na ƙwarai.
Ka gina kanka ta hanyar neman ilimi mai amfani wanda zai haifar maka da kwanciyar hankali da gamsuwa.
Ka kusanci mutane masu himma da manufa a rayuwarsu don hakan zai sa ka yi huɓɓasa/hoɓɓasa da ƙoƙarin koyi da su.
Ka zage damtse wurin aiki domin inganta rayuwarka da na waɗanda ke kewaye da kai dare da rana.
Samartaka ta fi kowane zango na rayuwa muhimmanci. Wanda bai ci moriyarta ta hanyar yin abinda ya dace ba, tabbas zai yi nadama a nan gaba.
Idan kun karanta wannan saƙon to ku karanta saƙon mu na gaba mai taken Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi a kyauta kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.
Allah Ubangiji ya tsare mu da aikin da-na-sani Amin
Tushe/Asali: Hausa Motivation