Da zarar ka ga macen da kake so ko kuma ka daɗe kana son ta amma ka rasa yadda za ka yi, to kada ka yi ƙasa a gwiwa kawai ka bi waɗannan matakan Insha Allah za kai nasara.
Marubuci:- Ridwan Khan Adam
Kada ka tsaida ita inda taron mutane yake domin ba za ta ba ka damar yin magana da ita ba, ka kasance mai tsabta sannan ka koyi yadda za ka dinga saka tufafi ko sutura tun kafin ka tunkare ta hakan zai sa ka burgeta ta samu ƙwarin gwiwar amsar soyayyarka.
Idan ka samu damar ganin fitowarta za ta je wani wuri sai ka bi ta sannu sannu a baya amma fa ka gyara takunka yadda ko juyowa ta yi ba za ta gane cewa ita kake bi ba.
Idan ka ga an kai gurin da akwai natsuwa a gurin, sannan babu hayaniya, sai ka yi mata sallama na tabbata za ta amsa maka, sannan kuma za ta tsaya ta ji me kake son ka faɗa mata.